BABI NA GOMA SHA BIYAR.

702 62 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*





*Na Xarah~B~B.*


*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com

  *Vote me on Wattpad @Zarah_bb.*


_Sau da yawa mu ke kuskuren fahimtar mutane. Ma'aunin da ba ya kuskure shi ne ka ajiye kanka a matsayin wanda kake yiwa hukunci._


  *BABI NA GOMA SHA BIYAR.*


    Da haka har ta iso ta shiga mota. Juyawa yayi ya nufe gefen mai tuk'i ya zauna.

"Ina wuni Yaya"
    "Lafiya k'alau my queen, amma kinyi kyau ba kad'an ba, anya kuwa zan kaiki wurin bikin nan"

Murmushi tayi wanda har sai da kumatunta suka lotsa(Dimple/Beauty point) ta ce

    "Meyasa?"
"Saboda kada a kalle mani ke" Ya fad'a idon shi k'yam akanta.

"Hmmm! Wazai kalleni?" Ta sake tambayar shi.
   "Au ba ki sa ni ba?" Ya fad'a yana k'ok'arin tayar da motar.

"Eh!" Ta bashi amsa atak'aice.

    Sai da ya murmusa kana ya ce "Mazan da ke wajen bikin"

"Ai walima ce za'ayi kuma bada maza ba"
    "Wai! Har na ji sanyi a raina"

Yadda yayi maganar yayi matuk'ar bata dariya. Haka dai suka cigaba da firar su cike da so da k'aunar junan su har suka isa k'ofar gidan su Sarah da ke gwammaja. Dai-dai nan wayar Jawaheer ta d'au k'ara, tana dubawa taga Sarah ce murmushi tayi sannan ta d'auka.

"Haba JJ tun d'azu fa nake jiran ki amma har yanzu baki zo ba"
    "Sorry y'an mata gani a k'ofar gida" Wani ihun murna Sarah ta sa ki had'e da kashe wayar.

"Ba fa za ki fita ba sai ta zo da kanta"
   "Ayi hak'uri Yayana"

"Ai ba laifi kika yi ba kawai dai akwai sak'on da zan bata ne"
    "To bara na fad'a mata"

Ta d'auko waya kenan da niyyar kiran Sarah sai gata ta fito.
    "Y'ar halak" Abin da Jawaheer ta ce da ita kenan tana dariya.

"Me akayi ne halan?" Sarah ta tambaya.
   "Yaya ne ya ce bazan fita ba sai kinzo, shine zan kira ki sai ga ki kin fito.

Murmusawa tayi game da mai da dubanta ga Jabeer ta ce
  "Sannu Yaya ya gida?"

"Lafiya k'alau Saratu ya hidimar biki"
    "Lafiya k'alau mungode Allah"

"Masha Allah! Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka"
    "Ameen ya rabbi"

"To ga amana nan na ba ki kada wanda ya kallar mani ma ta" Jabeer ya fad'a fuskar sa cike da annuri.

    "Angama Yayanmu"

"Yauwa nagode sai na zo d'aukarta anjima"
    "To nima nagode" Sarah ta ce da shi had'e da d'agawa daga wajen kad'an.

Da k'yar ya bari suka yi sallama cike da kewar junan su.
    Inda Sarah take tsaye ta isa suka shiga cikin gida.

Ganin sun shige yasa ya ja motar shi ya tafi.

****

Suna shiga Jawaheer taje ta gaishe da Maman Sarah tare da bata sak'on da Innah ta ce akawo mata. Sosai Maman Sarah tayi godiya.

   Haka aka cigaba da hidimar biki k'arfi uku na rana aka fara walima. Sosai Malama Khairat B Umar tayi wa'azi mai ratsa jikin mai sauraro. Amarya kuwa tasha kyau har ta gaji.

K'arfe biyar da rabi Jabeer ya zo d'aukar Jawaheer. Har mota Sarah ta rakata sallama suka yi sa'annan suka wuce.

"Bani labarin biki" Cewar Jabeer.
   "Hmmm! Biki yayi kyau sosai"

"Haba dai?"
   "Allah kuwa Yaya"

"Insha Allah namu sai ya fi wannan had'uwa"
    "Ko?"
"Eh!"

"Allah ya kaimu"
   "Ameen, amma meyasa naga kamar jikin ki ya mutu?"

"Bakomai"
    "Noo ki fad'a mani gaskiya mana"

"Kawai ina tunani ne anya kuwa Mumy zata yarda ka aureni?"
   Shiru yayi na sakanni kana ya ce

"Mu cigaba da addu'a insha Allah komai zai dai-daita"
   "To Allah yayi mana Jagora"

"Ameen ya rabbi my queen" da haka har suka isa unguwar su. Nesa kad'an da gida ya ajiye ta gudun kar su ci karo da Mummy. Har zata bud'e k'ofa ta fita sai ya kira sunanta. Dakatawa tayi da fitar ta juyu, murmushi suka sakarwa junan su kafin ya mik'o mata ledar da ke hannunshi, kafad'a ta mak'e alamun bazata karb'a ba. D'aure fuska yayi game da furta
   "Bana son haka, ki k'ar6a ko kin raina ne?"

"A'a! Ban raina ba amma ai hidimar tayi yawa Yaya"
   "Idan banyi maki ba wa kike son na yi wa?"

Shiru tayi bata ce komai ba.
   Sa ke mik'a mata yayi, cike da ladabi ta amsa tare da yi masa godiya.

Murmushi kawai yayi duniya kyawawan d'abi'u da halayen Jawaheer na k'ara tsunduma shi cikin kogin k'aunarta. Dan yanzu kashi cis'in da biyar(95%) na y'an matan yanzu rok'o da kwad'ayi yayi masu yawa. Shiyasa akuda yaushe yake rok'on Allah da ya mallaka ma shi Jawaheer amatsayin matar shi uwar y'ay'an shi.

"Yaya ni zan tafi" Maganar da ta maido shi daga tunanin da ya afka.
  "OK dear na sai munyi waya ki gaishe mani da su Innah"

"Za su ji insha Allah"
   Sallama suka yi ta fice daga motar.







*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt