*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA ARBA'IN DA TARA.*
_Kuna ina? Masoyan littafen *ZAMANTAKEWA!* wannan shafin sadaukarwa ne gareku na gode sosai da k'aunar ku Allahu ya barmu tare Ameen. #ILYSVM._
*_ONE WEEK LATER!._*
BAYAN SATI D'AYA!.
Yau ta kama alhamis(Thursday)kuma yau ne aka fara event d'in su Jabeer da Jawaheer.
Shiri suke yi sosai dan k'arfe hud'u na yamma(04:00pm)za su tafi kamu.
Tsaf amarya ta shirya cikin doguwar riga gown ta had'ad'd'en material kalar ja(Red)da duwatsu(Stones)a jikin shi, sai kuma nad'in head d'inta da ya yi masifar yi mata kyau kalar golden da stones red a jikin shi. K'afar amarya da hannunwanta sun sha k'unshi mai zanen folawa bak'i da ja. Shahararriyar mai kwalliya(Make up) mai suna Aunty Hureeya aka d'auko dan yiwa amarya kwalliya. Sosai amarya ta fito d'agwas da ita sai zuba k'amshi take. k'awayenta kuwa sun shirya tsaf cikin material d'in su mint green da red head suma sunyi kyau ainun.
K'arfe hud'u da minti goma na yamma(04:10pm)suka wuce wajen kamun.
Hall d'in yayi tsit kowa yana zaune akan kujera da tebur a gaban sa, ga drinks da ruwa da kuma y'an kayan motsa baki a kan teburin bayan jakunkunan da aka raba tun a bakin gate.
A hankali cike da natsuwa ango da amarya suka tako zuwa cikin hall d'in, abokanin ango da na amarya suka take masu baya. Sosai couple's d'in suka yi kyau kowa sai yaba su yake yi, kai tsaye wajen da aka tanada dan zaman amarya da ango suka nufa suna zama mutanan hall d'in suka tafa masu. Bayan wasu mintina mc ya fara jawabi daga nan kuma aka shiga gudanar da bikin kamar yadda aka tsara.
Wasu mata na hango sai faman shan drink suke yi, can d'aya daga cikin su mai suna Taufeeqa ta numfasa game da maida dubanta ga sauran k'awayenta ta ce
"Wallahi ba k'arya ango da amaryar nan sun yi matuk'ar birgeni"
"Hmmm! Kamar kin san abin da zan fad'a kenan ji nake ina ma ace ni da mai sanyi na ne" Cewar Basmah.
"Ke da mai sanyin ki ko dai ni da Faruk d'ina" Kausar Luv ta fad'a tana lumsar ido sai ka ce Faruk d'in ne a gabanta.
"To Allah ya basu zaman lafiya tare da zuri'a mai albarka" Rabi'at A'A ta ce da su tana murmushi.
"Allahummah Ameen" Suka amsa da shi dukan su.
"Yauwa Taufeeqa wai ina kika baro man Waleedina?" Kausar ta ce da ita.
"Yana gida na bar shi. Ina zan iya zuwa da su duka awurin biki ni da nake son na kwashe shoki, ai ko Ahmad aje man shi za kuyi sai na gama kwasar shoki"
Dariya suka yi dukan su kafin kausar ta furta
"Ni bazan rik'e maki shi ba, meyasa shi baki bar shi a gida ba?"
"Haba Kausar wannan jaririn zan bari a gida?"
"Eh mana"
"A'a nikam ai bazan iya yin hakan ba"
"Ai kuwa za ki kwashe shokin da shi dan bazan k'arbe shi ba tunda kika k'i zo man da waleedina" Kausar ta furta fuskarta cike da annuri.
"Tayi maki kyau" Taufeeqa ta ce da ita tana murmushi.
KAMU SEDANG MEMBACA
ZAMANTAKEWA!.
NonfiksiSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...