BABI NA HAMSIN DA D'AYA.

623 37 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*














*Na Xarah~B~B.*













*{NWA}.*












www.zahrabb.blogspot.com









*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*




 
   _Kada ki/ka sa ranki/ka cewa mutane duk za su so ki/ka. Zukatan mutane a kullum cikin canji suke, abin da suke so yau, shi suke k'i gobe. Allah ya sa mu dace Ameen._

  *_Gaisuwar ta ku ce my Wattpad fans i really really appreciate the way you vote and comment, keep it up!.#one luv._*









       *BABI NA HAMSIN DA D'AYA.*






    Zamanta Maryam ta gyara tare da yin ajiyar zuciya kana ta ce

"Wallahi Waliyya ina jin tsoron samarin wannan zamanin ne."

   "Meyasa kike jin tsoron su Maryam?"

"Saboda k'alilan ne masu tsoron Allah"

"Kamar ya? Bangane me kike nufi ba"

   Murmushi Maryam tayi wanda ya fi kuka ciwo game da rik'o hannun Waliyya tare da fad'in

"Za su ce suna sonki sai sun koyar da ke soyayyar su daga baya su yaudare ki. Waliyya mafi yawancin samarin zamanin nan sha'awar mace kawai suke yi, masu yin soyayya domin Allah basa da yawa, wasun su za su zo ne kawai su 6ata maki rayuwa. Duba fa ki gani halin da Aunty Zubaida ta tsince kanta duk a sanadin saurayi." Ta k'arasa maganar cikin rawar murya.

   "Hakane kam amma kuma kar ki manta kowa da ta sa k'addarar kuma ba wanda ya isa ya guje mata. Rashin kula samari ba shi zai sa kada a yaudare ki ba, sannan ita Aunty Zubaida k'addarar ta kenan kuma idan da rabo zata shiryu Insha Allah" Waliyya ta fad'a cikin tattausar murya.

Shiru Maryam tayi bata ce komai ba.

   "Dan Allah ki cire duk wata damuwa da fargaba a ranki. Ki maida dukkan lamarinki a wajen mahaliccin ki, ki yarda da duk abin da ya same ki k'addarar ki ce ta zo da hakan, ki daina korar samarin ki, mace d'an k'aramin lokaci ne da ita."

"Insha Allah Waliyya zan daina amma ki taya ni da addu'a"

    "Karki damu Mero ta addu'a kam ana yi sai dai a dad'a"

"To tawan nagode sosai Allah ya bar k'auna tsakanin mu"

   "Ameen Ameen Ya Rabbi Mero ta"

Duka Maryam ta kaiwa Waliyya tana cewa

   "Allah ki daina kirana da Meron nan"

Dariya Waliyya tayi ta ce

   "Aradu bazan bari ba dan sunan da dad'i"

"Lallai ma! Haka za ki ce?"

    "Eh mana, kema kin san da dad'i"

"A'a nikam ban sa ni ba"

    Haka suka cigaba da firar su cike da aminci, tare da bayyanar da k'aunar da ke tsakaninsu.

Sai k'arfe shida da mintina sa'annan Maryam tayi sallama da aminiyarta ta wuce.


******

Zaune take a gefen katifarta, tunda ta dawo daga gidan su Waliyya take nazarin maganganun da suka yi.

    "Gaskiya Waliyya ta fad'a maki ya kamata ki natsu. Duk fa abin da Allah ya nufa ba makawa  sai ya faru, wayo ko dabarar ki ba za ta gushe ki daga k'addarar ki ba dan haka ki kwantar da hankalinki ki kuma cigaba da addu'ar Allah ya za6a maki duk abin da yafi zama alkhairi a rayuwar ki. Sa'annan duk yadda zamani ya sauya ba za'a rasa na kirki ba." Abin da zuciyar Maryam ta ce da ita kenan.

ZAMANTAKEWA!.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang