*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Vote me on Wattpad @Zarah_bb*
_Rayuwa a kullum cikin canji take. Yaro zai girma babba ya tsufa, mai lafiya ya yi ciwo, mai ciwo ya warke, rayayye kuma ya mutu. Lokacin da ka samu wani zai rasa, idan ka fa d'i wani zai ta shi. Rungumi hukuncin Allah a cikin amincewa da yarda._
*BABI NA.....BAKWAI.*
Haka kuwa akayi washegari bayan Jawaheer ta dawo daga makaranta suka shirya suka tafi gidan Hajiya Indo dake unguwar Sarki anan garin Kano. Sosai Hajiya ta ji dad'in zuwan na su sai saka masa albarka take tana yi masa fatan gamawa lafiya, sun jima a gidan kafin ya yi mata alkhairi suka wuce.*******
"Mu'azzam me yasa bazaka cika D.E(Direct entry) form ba?"
"Uhmmm! Jabeer kenan ai ku haka ma sai na godewa Allah, yanzu idan na ce zan cigaba da karatu abubuwan za su yi yawa tunda ba wani k'arfi ne damu ba gashi kuma aikin ya yi wahala da ko da shi a rage zafinta mutum ya gama karatu amma ba aikin yi, sa'annan wa ya yi mani karatu wa ya yi mani aikin kafintar da na ke yi? Gashi ogan mu sam bayada mutunci idan ma mutum ya yi wasa zai iya korar sa"
"Hakane kam! Allah yasa hakan ne mafi alkhairi"
"Ameen Ameen Jabeer d'ina""Yauwa! Amma mutuniya ta za'a barta ta cigaba da karatu ko?"
"A d'akin mijinta ba""Haba dai! Baza tayi ku da diploma bace? Ko ta ta fi School of nursing tunda tana da k'ok'ari"
"Wlh Jabeer akwai ka da abin dariya, mu dai samu ta gama scondary school d'in, yanzu karatun boko ai sai y'ay'an masu kud'i"
"Insha Allahu idan munyi aure zata cigaba da karatun ta"
"Halan mummy ta yarda da zancen"
"Hmmmmm! Wallahi Mu'azzam har yanzu bata amince ba, ita ala dole sai dai na neme d'aya daga cikin yaran k'awayen ta ni ban san dalilinta na k'in talaka ba, ga shi sam mummy bata iya *ZAMANTAKEWA* ba because(Saboda) ko y'an uwanta wad'anda basu da kud'i wallahi bata son su abun yana matuk'ar damuna" Jabeer ya fad'a fuskar sa fal da damuwa.
Kafarsa Mu'azzam ya dafa kana ya ce
"Kayi hak'uri abokina ka barwa Allah lamarinka ka cigaba da addu'a kawai, kuma kayi mata biyayyah kasan iyaye dole abi su a hankali. Amma da zaka bi shawara ta ka hak'ura da Jawaheer kawai tunda har iyayenka sun k'i su yi amanna da zancen ta""Nooooo! Ka ma daina wannan zancen dan wallahi bazan iya hak'ura da ita ba kawai dan tana y'ar talaka ai wannan ba hujja bace, idan da adalci kamata ya yi d'an mai kud'i ya aure y'ar talaka ita kuwa y'ar masu wadata ta aure mijin da bayada sai a taimakawa juna amma saboda duniyar ta zama abin da ta zama kowa kansa ya sa ni. Sannan meye laifin talaka da ba za'a so shi ba? Ina ce ba shi ya yi kansa ahaka ba! Amma wasu dan kawai Allah ya yi masu wadata sai su rink'a wulak'anta talaka wanda hakan sam bai da ce ba".
"Hakene Jabeer amma ka manta abin da bahaushe ya ce _k'warya ta bi k'warya_ kuma ka san kowa da fahimtar da Allah ya yi masa haka zalika kowa da rayuwar sa dan haka yanzu ko da bazaka hak'ura da ita ba to ka nuna wa iyayenka kamar ka hak'ura sai ku rink'a mu'amalar ku a 6oye ba tare da sun sa ni ba, idan Allah ya nuna mana ka je service ka dawo sai a san abin yi"
"To idan su Baba suka zata na janye ne fa?"
"A'a ni zanyi masu bayanin komai sa'annan ba wai zaka daina zuwa wajenta bane a'a su mummy zaka nunawa kamar ka daina d'in, hope ka fahimce inda na do sa?""Yes abokina na gane, thanks alot for your caring(Na gode sosai da kulawar ka) Allahu ya bar k'auna da zumunci a tsakanin mu"
"Ameen ya rabbi! Nima nagode".
_3 day's later!._
*_08:30am._*
Baba ne zaune a d'akinsa yana jan carbi, sallamar da akayi ce ta sakasa dakatawa. Sallamar ya amsa tare da yi masa izinin shigowa. Cike da ladabi Mu'azzam ya shigo d'akin.
"Ina kwana Baba?"
"Lafiya k'alau Mu'azzam, ya akayi ne?"Nan take Mu'azzam ya zayyanewa Baba yadda suka yi da Jabeer. Shiru Baba ya yi sa'annan daga bisani ya ce
"Anya ayi haka kuwa Mu'azzam? Ina ga tun da iyayen sa ba sa so ya hak'ura mana."
Lalla6a Baba Mu'azzam ya shiga yi.
" Ka ga bawai nak'i amincewa bane, har ga Allah ina son Jawaheer ta aure Jabeer ba dan komai ba sai dan na yaba da kyawawan halayensa da natsuwarsa amma tun da iyayen shi sunk'i ya hak'ura kawai"
Da k'yar da sud'in goshi Mu'azzam ya shawo kan Baba ya yarda da plan(Tsari) d'in da suka yi shi da Jabeer.
******
*_04:25pm._*
Zaune take tana wanke-wanke Innah na cikin d'akinta Baba ya fita haka ma Yaya Mu'azzam gidan ya yi shiru. Sau biyu yana rangad'a sallama amma sam ba ta ji ba hankalinta ya raja'a ga aikin da take yi. Karan da ke hannunsa ya dogara mata a baya cike da tsoro ta zabura game da wulgi da cupin hannunta wanda take kan wankewa. Tana juyuwa karaf idanuwansu su ka sark'e wani sanyayyen murmushi ya yi mata game da cewa
"Sannu kura uwar tsoro"Langwa6ar da kai ta yi kamar zata yi kuka, ba ta ce da shi komai ba ta koma kan k'aramar kujera(kujerar tsakar gida) ta zauna had'e da cigaba da aikinta.
Du k'awa ya yi yana d'auraye kwanokan da ta wanke. Ganin har sun kusa gamawa ba ta tanka shi ba duk da surutun da yake ta faman yi, hakan ya sa shi mik'ewa tsaye tare da yarfe hannunsa ya ce
"Idan Innah ta fito ki gaishe ta ni na tafiyata tun da fushi ake yi dani"
Sai a lokacin ta d'ago ta dube shi sai da ta turo baki kana ta ce "Toh ai kaine"
Sai da ya murmusa domin komai Jawaheer d'in shi ta yi birge shi take yi ya furta "Kiyi hak'uri my queen bazan sake ba"
"Ba komai Yayana ya wuce and kaima ka yi hak'uri kar ka tafi"
"To my queen" Ya fad'a game da du k'awa, a tare suka gama wanke-wanken, shara ma cewa ya yi sai ya tayata sai da ta yi da gaske sannan ya barta ta yi. Duk wannan bidirin da suke yi Innah na jin su sai faman murmushi take yi ita kad'ai tana k'ara jinjina wannan son da sukewa junan su...
_Need ur prayer plz my luvly nd caring fans am in need of it._
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...