BABI NA HAMSIN DA UKU.

609 54 4
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*









*Na Xarah~B~B.*










*{NWA}.*







www.zahrabb.blogspot.com





*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*







   
  _Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Masha Allah. Happy birthday wish you more years ahead Allah ya albarkaci shekarunka Waleedina(Alhasan Ameenu).#one luv._

    Happy birthday once again Waleedina.#ILYSVM.





     *BABI NA HAMSIN DA UKU.*







    Cike da tsananin mamaki Mummy ke kallonta.

"Kin san abin da kike fad'a kuwa Juwairiyya?"

   "Na sani Mummy"

"Hmmmmm! Lallai ma. Yaushe kika fara son wannan matsiyaciyar yarinyar ne?"

   "Ni fa Mummy ina jin tausayin Yaya ne"

"Meyasa?"

   "Mummy ya kamata ku fahimci Yaya ba k'aramin so yake yi wa Jawaheer ba. Mummy kun san yanayin tarbiyar Lubna sam bata da ce da Yaya ba meyasa kuke son takura d'an da kuka haifa a kan wata? Yanzu Allah kawai ya san halin da Yaya yake ciki. Idan wani abun marar kyau ya same sa fa? Mummy kuna tunanin Lubna zata so shi har ta zauna da shi? Mummy ya kamata ace zuwa yanzu kun hak'ura, kun rungume Jawaheer a matsayin sirikarku." Juwairiyya ta k'arasa maganar idonta na zubar da hawaye.

Sosai take jin haushin kanta akan abin da ta yiwa Jawaheer a baya tare da yin da na sani marar adadi. Nan ta ke magagganun da Amina ta fad'a mata ranar da ta kai mata ziyara a gidan su suka rink'a yi mata yawo a kai.

   "Juwairiyya ki ji tsoron Allah ki daina abin da kike yi, yanzu idan kece aka yiwa ko Yayar ki za ki ji dad'i? Ke da ya kamata ace kina lalla6ar Mummy tare da yi mata addu'ar Allah ya canza mata irin wannan halin na ta amma ke da kanki kike zugata? Haba Juwairiyya yanzu ki ajiye kanki a matsayin Jawaheer k'anwar mijinki ta zo tayi maki wannan cin kashin da kika yi mata tsakanin ki da Allah me za ki ji?"

Shiru Juwairiyya tayi ta kasa cewa komai.

   "Nasan ba za ki ta6a jin dad'i ba amma ke meyasa kika yiwa wata. Karfa ki manta imanin d'ayanku bazai ta6a cika ba har sai ya soma d'an uwan shi abin da yake soma kansa. Dan Allah ki fad'a man laifi d'aya da Jawaheer tayi maki wanda yasa bakya sonta?"

Nan ma Juwairiyya shiru tayi mata.

   "Wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba na san ba abin da ta ta6a yi maki na 6atanci. Shin ki tsaneta dan kawai suna talakawa su suka yi kansu a haka? Keda kuke da kud'in ku kuka yi kanku a hakan ko dubarar ku ce ta ba ku? Shin kin manta da dare d'aya Allah kanyi bature, yanzu idan Allah ya k'wace kud'in na ku ya ba su ya za ki yi? Bara ki ji ba ta rin dukiya keda amfani ba wadatar zuciya tafi komai a duniya. Sa'annan tsaf dukiyar mutum zata kai shi wuta idan har baiyi amfani da ita yadda ya dace ba. Duk mulkin ku ba ku kai Fir'auna ba haka duk kud'in ku ba ku kai K'aruna ba yanzu duk suna ina? Me kud'in da mulkin su ya tsinana masu? Shin wai bakya ma tunanin ki mutu da hak'k'in wannan baiwar Allah?"

Shiru Amina tayi na wasu mintina kafin ta nisa ta cigaba da cewa.

    "Yanzu idan kece aka jarabe ki da mugun son wani kuma shi wannan d'an talaka ne ga shi a duniya kina jin idan ba ki aure shi ba komai zai iya faruwa, bayan kin gabatar da shi ga iyayenki sai kawai Mummy ta ce ba za ki aure d'an talaka matsiyaci ba dan Allah za ki ji dad'i? Ko kuma ranki zai yi fari?"

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now