BABI NA SITTIN DA SHIDA.

598 55 5
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*







*Na Xarah~B~B.*


*{NWA}.*





www.zahrabb.blogspot.com



*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*

      _Fatan alkhairi ga duk masoyana na nesa dana kusa, sak'onnin ku sun riskeni na gode sosai Allah ya bar so da k'auna a tsakanin mu. Ku sani Zarah na yinku kamar yadda kuke yinta. Allah ya had'a fuskukinmu a aljannar firdausi Ameen. #one luv._


        *BABI NA SITTIN DA SHIDA.*

     Yau kusan kwana hud'u kenan da dawowar su amma duk wani tunani da ya kamata suyi dan ganin sun sakawa Jabeer magani da turaren da boka ya ba su amma abin ya faskara, kullun haka suke zama suyita sak'e-sak'en su amma ba nasara. Yau ma kamar kullun zaune suke akan tabarmar dake shinfid'e a tsakar gida kasancewar yanayi na zafi da ake ciki.

"Yanzu Hajiya ya kike ganin za mu yi wallahi abubuwan nan sun fara ba ni tsoro kada fa na zo na rasa Jabeer" Lubna ta fad'a tana kallon mahaifiyarta.

   "Ba za ma ki rasa shi ba" Hajiya Ladi ta ce da ita cikin muryar lallashi.

"To Allah ya sa."

   "Zai ma sa."

"Amma Hajiya ance da na tsare shan maganin nan a bisa k'a'ida cikin nan zai zube amma gashi har yau shiru."

   "Lubna dad'ina dake kin fiye azarb'ab'i wallahi, duka-duka kwanan ki nawa kina shan maganin nan ne da har za ki fara k'orafi?"

"To ba cewa......" Ringing d'in wayarta ya hana mata k'arasa maganar da ta fara. Ganin Alhaji Mati ne yasa ta jan wani k'aramin tsaki game da danna wayar silent.

   "Wa ke kiranki ne da ba za ki d'auka ba?"

"Alhaji Mati ne, yau wajen kwanan sa biyu yana kirana game da turomin sak'onnin amma bana d'aga kiran jiya har akayi sallar magrib yana k'ofar gidan nan amma na k'i fita."

   "Meyasa Lubna?" Hajiya Ladi ta tambayeta.

"Sai na gama wahalar da shi ko zan kulasa sai ya san bana cikin matan da ake yiwa wulak'anci."

   "Hakan ya yi kyau ai."

"Allah ko Hajiyata."

    "Allah kuwa y'ata."

"To ni dai ya za mu yi da zancen Jabeer?"

"Karki damu zan san yadda za'a yi"

   "To" Kawai Lubna ta amsa mata da shi.

******

*_THREE WEEKS LATER!._*

    *_BAYAN SATI UKU!._*

yau ta kama laraba(Wednesday)kuma yau ne za'ayi baikon Zaid da Maryam. Misalin k'arfe goma sha d'aya na safe(11:00am)y'an uwa da abokanin arziki duk sun hallara a wajen. Tarba mai kyau y'an uwan Zaid suka samu daga dangin Maryam, anyi komai cikin mutunci da girmama juna, an saka ranar biki nan da wata biyu kacal. Daga nan kuma suka yi sallama da juna aka rabo cikin girmamawa.

   Murna wajen Zaid da Maryam ba'a cewa komai, kowa sai taya su murna yake yi tare da yi masu fatan alkhairi. Nima dai Zarah ina yi masu fatan alkhairi a rayuwar su Allah ya nuna mana ranar bikin lafiya Ameen.

******

Kwance take akan gado ta k'udundune da bargo sai rawar sanyi take yi.

   Sun fi minti uku da shigowa gidan suna ta rafka sallama amma shiru ba'a karb'a masu ba.

ZAMANTAKEWA!.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang