BABI NA TALATIN DA TAKWAS.

561 55 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*










*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com

*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*



_Ina mai ba wa masoyana hak'uri akan jina da ku ka yi shiru kwana biyu, hakan ya faru ne akan wasu dalilai amma yanzu Alhamdulillah! Komai ya zama normal insha Allah. Sa'annan ina k'ara godiya da kulawar ku game da k'aunar ku agareni Allahu ya bar mu tare Ameen. Zarah~B~B na gaida duk wasu masoyanta na nesa da na kusa. #one luv._


*BABI NA TALATIN DA TAKWAS.*



    "Yayana congratulation once again, yadda ku ka gama wannan jarabawar lafiya Allah yasa result ya yi kyau sosai."

"Ameen Ameen k'anwata kuma matata insha Allah"

   Murmushi kawai Jawaheer tayi masa ba tare da ta ce da shi komai ba. Shima shirun ya yi mata da tunani kala-kala a ranshi, sun d'auki lokaci a hakan kafin Jabeer ya katse shirun da cewa

"Ni zan wuce"
      "Da wuri haka Yaya?"

Kai kawai ya gyad'a mata alamar Eh.

   "Haba! Meyasa za ka tafi tun yanzu bayan baka jima da zuwa ba?"

"Saboda yau na ga alamar gimbiyar tawa bata son yin magana kuma bana son na takura ta" Ya ce da ita idon shi k'yam akan ta, wani sonta da k'aunar ta na k'ara bin jinin jikin shi.

Dariya tayi had'e da rufe fuskar ta da tafin hannuwanta kana ta ce "A'a my sweet J kayi hak'uri bahaka bane"

   "Ai bakya laifi uwar gidana"

"Wace ce amaryar?" Jawaheer ta ce da shi tana zarar ido.

    Yadda tayi maganar ya ba shi dariya, duk yadda ya so ya had'iye dariyar kasawa ya yi sai da ya yi ta.

Sake da baki Jawaheer ta bi sa da kallo, ganin haka ya sa ya yi saurin yin shiru.

   "Meyasa ka yi shiru? Ai ka cigaba da dariyar tun da ka samu y'ar dariya" Ta fad'a cike da shagwa6a.

"Toba nake ranki ya dad'e ayi hak'uri"

   "Bazan yi ba"

"Haba! My queen karfa a ji mu"

   "Ni ka k'yaleni ka je can wajen......."Sai kuma tayi shiru.

Cikin sakin fuska Jabeer ya furta "Kin ga queen ni fa ba ki fahimce ni ba ne, ke ce uwar gida kuma kece amarya da yardar Allah ke kad'ai ce matata kuma uwar y'ay'ana. Dan Allah ki daina 6ata ranki kin ji amarya ta" Jabeer ya k'arasa maganar ya na mai kanne mata ido.

Kishi kumallon mata jin abin da Jabeer ya ce ya sa Jawaheer yin murmushi wanda har sai da fararen hak'oranta suka bayyana.

   Haka dai suka cigaba da firar su cike da so da k'auna.

_Two(2) days later!._

    *BAYAN KWANA BIYU!.*

  *_10:30am._*

"Kin ce sai Jabeer ya gama exam d'in shi ga shi yau wajen kwana biyu da kammalawa amma ban ji kin ce da ni komai ba"

   "Wai meyasa kike ta da hankalin ki ne haka?" Mummy ta ce da Hajiya Ladi.

"Dole na ta da hankalina dan kuwa Lubna kullun cikin yi man kuka take ta ce ko kiransa tayi a waya baya d'agawa wani lokacin ma rejecting yake yi" Cewar Hajiya Ladi.

   "Ki dai k'ara hak'uri insha Allah komai zai dai-daita"

"Hmmmmm! Maganar ki kenan ai"

   "Ni dad'i na da ke gajen hak'uri" Mummy ta ce da ita.

"Au! Hakama za ki ce?" Inji Hajiya Ladi.

   "Allah ba ki hak'uri ranki ya dad'e."

Sun d'an ta6a fira kafin Hajiya Ladi ta yiwa Mummy sallama ta wuce.

******

"Yauwa Jabeer daman abin da yasa na ce ka zo shi ne d'azu munyi waya da Kawo Adamu ya ce gobe yana nan zuwa insha Allahu"

  "Haba dai?"

"Wallahi kuwa"

   "Kai Alhamdulillah! Allah na gode maka, Allah yasa k'arshen wahalar ta zo" Jabeer ya fad'a fuskar sa cike da annuri.

"Ameen Ya rabbi Jabeer"

    Godiya sosai Jabeer ya yiwa Aunty Halima kafin ya bata kud'i da ni kaina bansan ko nawa bane sa'annan ya fice daga gidan. Direct(Kai tsaye) gidan Baba Al'ameen ya nufa cikin sa'a kuwa ya same sa a gida. Bayan sun gaisa Jabeer ya labartawa Baba Al'ameen duk abin da ake ciki har tafiyar su Rano da Aunty Halima da kuma zuwan da Kawo Adamu zaiyi gobe idan Allah ya nufa.

"Kai masha Allah! Amma na ji dad'in wannan zancen, Allah yasa adace. Ni ma ka mik'a man godiya ta ga Halimatu, mungode sosai da wannan k'ok'arin da tayi mana." Baba Al'ameen ya furta cike da jin dad'in labarin da Jabeer ya zo masa da shi.

*****

"Kin ga ki kwantar da hankalinki idan ta san wata ai bata san wata ba, da yardar Allah sai mun cika k'udurinmu akan Jabeer, yanzu ki bani nan da kwana uku idan har batayi wani abun akai ba to zan je wajen boka cika aiki" Hajiya Ladi ta ce da y'ar ta Lubna.

  "Allah ko Hajiya ta?"

"Allah kuwa! Ni dai kawai ki cigaba da abin da na saka ki"

   "To Hajiya ta angama"

Dariya suka yi a tare game da tafa hannu kamar wasu sa'anni sam ba za'a ce uwa da y'a ce ba.



   Don't forget to Vote and comment on Wattpad @Zarah_bb.


      Muje zuwa........




*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now