💖💝BATUUL 1💖💝

26.3K 962 21
                                    

💖💝BATUUL 💖💝




By phartiemarhk


All Thanks to Allah (SWT) for granting me d chance,ability , previledge and knowledge to write this story. I dedicate this story to *KHALEESAT HAIDAR* (Maijidda) ,you have been an amazing writer,you make time for it everyday. You have set realistic goals,embraced the ecstacy of writing. You followed your heart not the market and fame. You don't just Start stories,you finish them,you dream big. You learn the rules,follow the rules and break them because rules are meant to be broken😅.Constructive, Criticism,Solicit,Accept and Manage. Put your ego in your back pocket and sit on it. Writing is à Journey, not à destination. Enjoy the scenery and give back to the writing community. WRITE SCARED. Remember you are the master of inspiration, not its Slave. Set your stories Free. Send them into the world .
DON'T SLACK ON THE HARD STUFF.
*PHARTIEMARHK* LOVES ❤💝You😘


Sanye take da Abaya baqa da yasha aiki da Swarovski stones ta yafo qaramin gyalen abayar ba tareda da wrapping dinshi ba, kafarta sanye da slippers din vinci shima baqi mai Swarovski Stones din à jiki .Siririyace sannan ba doguwa ba tana da shape mai kyau, bata da haske kuma bata da duhu sosai, Irin dai mutanen da ake kira chocolate color ne ko kuma wankan tarwada, dan karamin fuskar ta zagaye yake da dan karamin baki, yayinda Dogon hancinta ya dace da mazaunin sa, Idan tai murmushi kuwa dimlpe dinta yake lotsawa ya Kara hasken annurin fuskar, idanun ta kuwa haka suke tamkar farin wata wajen haske yoh masu iya magana sukace Ga Wata 🌙👈 ga Zara 😀,hooo me kr2 Idan nace zan tsaya zayyano kyawun fuskar ta toh Lalle za'a dade ban gama ba, domin dai BATUUL mai kyau ce.

Riqe take da wayarta à hannun hagu yayinda dayan hannun take riqe da karamin yaro da bai wuce shekara uku ba, tafiya takeyi à hankali kuma cike da natsuwa, sannan ga hadari da ya rufe ko ina, ruwa ko yaushe kan iya saukowa sai iska mai dadi dake kadawa à hankali à filin Idin Ramat square dake Maiduguri ,ta juyo sannan ta kalli yaron dake riqe da Hannunta sannan tace "Babich kaga kasa su Aunty Sun tafi Sun barmu ko, ai shikenan in muka rasa sallah", yaron yayi dariyarshi mai kyau yace "ai zamuyi sallah har in roqi Allah ya bani irin CLS din Yaa Ahmad, Aunty tace komai nake so in roqi Allah zai bani" tace "to kaga muyi sauri sai mu yi sallahn ka roqi Allah" yaron ya dubeta sannan yace "Yaa Baatul ai kece bakya yin sauri inata Jan hannunki", tace "toh shikenan zanyi saurin muje mu samesu", haka suka karasa har wajen Sallahn daga gefen mata suka samu har an shimfida musu abun sallah sannan suka zauna wata farar mata mai kyau da baza ta wuce shekaru 35 zuwa 38 ba tana riqe da jariri ta juyo ta dubesu tace "a ina kuka sami hulan?" Baatul tace "Aunty a mota ya bari", matar da aka kira da Aunty tace "ai ke kika biye mishi da kin barshi yayi sallah babu hula tunda da gangan ya cire", Batuul tayi murmushi tace "Aunty ai da yanxu bamajin Khuduban nan da akeyi", Aunty tace "hakane kam", Baatul ta juya ta kalli wata yarinya da bata wuce sa'arta ba tace "Fa'iza kin dauko min jakata da nace ki fito min da ita dan inaso inyi sadaka in an idar da sallah", yarinyar da aka kira da Fa'iza tace "ehh yaa Baatul na dauko gashi nan ma", ta dauko wata jakar Hermès mai ruwan toka da kana gani kasan yana ihun luxury ta mikowa Batuul, Baatul ta amsa tayi murmushi sannan tace "na gode Fa'iza", daga haka suka zauna shiru suna sauraron khuduba har aka gama aka tada sallah Baatul ta dubi Fa'iza tace "tunda baza kiyi sallah ba ki karbi Aabid à hannun Aunty", tace "toh Yaa Baatul", ta sa hannu ta karbi jaririn daketa wasa sannan ta dan koma gefe su kuma sukayi kabbara suka nutsu dan su nuna godiyarsu ga Allah (swt) da yasa suka gama Azumi lafiya har yasa suka ga sallah.

Ahaka suke Zaune bayan idar da sallah har Imam ya gama hudubar bayan sallah da wa'azi da tunatarwa , nan Dubban jama'ar da suka hallaci sallar suka fara kokarin kama gabansu. Batuul na riqe da hannun Hafiz suka fito lokacin iskar ta fara yawaita

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now