💖💝BATUUL 74💖💝

10.7K 491 35
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



        Har ranshi ya dinga jin wani tausayin Ajiddeh, Sam ba ta haka yaso tasan wacece Batuul ba, yaso ya zaunar da ita yayi mata bayani yadda zata fahimta snn ya lallab'ata har ta hak'ura, shi kam yama rasa ya akayi taji zancen cikin nan dan yasan bata shigo office d'in doctor ba, toh ko lab'e takeyi har ta jiyo abunda suke fad'i, kafad'a ya d'aga alamar ita ta sani inma laben tayi, gashi gaba d'aya bayason ganin hawayen idonta dan its making him feel guilty, ji yakeyi kamar yaci amanarta da bai sanar da ita tun da wuri ba, Ajiddeh kam tsayawa kallonsa tayi ganin ya ki ce mata komai Sae ma barin wajen da yayi, zuciyanta ne taji kamar ya fito tsabar bugawan da yakeyi, shikenan yanzu ta sake tabbatar da gaskiyan al'amarin, lallai Batuul matarsa ce tunda har ya iya wuceta tana hawaye ba tare da yace mata komai ba, so take kawai taji wani ya tado ta daga wannan mugun mafarkin da takeyi amma ina bata samu hakan ba dan ba mafarki bane take, ji tayi k'afafuwanta na rawa baza su iya d'aukanta ba, da k'yar ta juya tabi bayanshi itama, zaune ta taddashi bakin gado ya dafe kanshi, zuwa tayi ta tsaya mishi aka kamar wacce ta hadi'yi tab'arya, a hankali ya d'ago kanshi yana kallonta, goge hawayen fuskarta ta shiga yi tana kallonsa a k'ek'ashe, duk wani so da tasan tana yiwa Aliyu yau ji tayi ya koma tsana lkci daya, kyan da take gani yanayi mata yau duk babushi sai tsanarsa da takeji kamar ta shakeshi, da k'yar ta iya bud'e bakinta tanajin wani abu tokare a mak'oshinta tace "Ka sallameni, ka bani takardata zan tafi gidanmu", kallonta yayi da kyau jin abinda take fad'i, hannayensa ya mik'ar zai kamo nata dasu ya zaunar da ita gefenshi tayi maza ta janye hannayenta tana mishi wani matsiyacin kallo tace "kar ka kuskura kayi gigin tab'ani, ni ba mazinaciya bace bare ka goga min najasar dake tattare dakai", ido ya rintse jin abinda Ajiddeh ke fad'a mishi, yasan koma dai menene shi yayi causing da tun farko bai sanar da ita ba, hannunta ya fizgo a karo na biyu ya zaunar da ita gefenshi, idonshi dake rikitata ya zuba mata tanajin yadda sonshi da ta dad'e tana dako da kuma tsanarshi da ya shigeta lokaci d'aya ke kokawa cikin zuciyarta, ta fashe da kuka tayi saurin d"auke idonta daga nashi dan har cikin ranta takejin kallon na piercing through her, k'ok'arin danne d'aya b'angaren zuciyarta dake son rinjiyarta akanshi tayi cikin dakewar murya ta sake ce mishi "nace maka bana auren, free me from this hell so called marriage, ai ba kaine kad'ai namiji ba a duniyan, kaje kuci gaba da zaman da kukeyi, ni dai saken....", bai bari ta k'arasa ba ya d'aura yatsunshi biyu kan lips d'inta, gaba d'aya pulses d'inta saida sukayi responding to abinda takeji gameda Aliyu amma yanzu ba shine gabanta ba, ji take komai zata iyayi kan Aliyu yanzu dan tuni tausayinshi ya fita daga ranta tun daga lokacin da ya bud'i baki ya fad'i mata matsayin Batuul, ko da rabasu da ransu ne ji takeyi zata iya a daidai wannan lokacin, matso da ita yayi kusa da shi yana kallon yadda hawaye ke zirya a fuskarta, hannu yasa ya shafe mata hawayen, kamar yayi electrocuting d'inta haka takeji jin hannunshi kan fuskarta, rintse ido tayi tana jin sabon al'amarin dake faruwa da ita a yanzu, a hankali yave "Ajiddeh open your eyes and look at me", Kin budewa tayi sai kukan da take har da shessheka, ya kuma maimaita abinda yace a karo na uku, a hankali ta bud'e rinannun idanunta ta sauk'e kanshi, cikin sanyin murya yana murxa hannunta dake cikin nasa yace "Everything happened so fast, naso fad'a miki tun farko but I don't know wat draw me aback from telling you, I....", yaja wani dogon numfashi snn yaci gaba a hankali "Just take it as our fate wife, kaddarar muce tazo da haka, bamu isa tsallake ta ba, Duk da ba haka naso ki San wacece Batuul ba, I wanted calming you, in nutsar dake da sanin who she is but yadda kikayi approaching d'inta was so stupid", ta fashe da matsanancin kuka jin abinda yake ce mata, wato dai this is real ba mafarki take ba, turasa tayi kamar mahaukaciya tace "abinda yafi stupid ma duk zaka fad'i tunda kaci amanata, ka cuce ni, ka yaudareni Aliyu, I won't forgive you for this", bai dakatar da Ita ba har saida tayi shiru yace "Hear me out Ajiddeh, its been over a year tunda mukayi aure, ban tab'a ce miki inason ki haifa min baby ba despite inaso amma nasan Allah ke badawa at d right time shiyasa ban tab'a bothering d'inki ba, get this Batuul is my wife and tana d'auke da d'ana a cikinta," kamar ya watsa mata mai mey zafi cikin ranta haka ta rik'a ji jin ya ambaci shegen dake cikin Batuul da d'anshi, shikenan tata ta sameta tana zaune wata can xata Haifa masa d'a ba Ita ba, matsowa yayi kusa da ita yaci gaba "I can't risk anything happening to my baby, Inaso ta haifamin abinda ke cikinta ko wane iri, am destined to auren Batuul, babu mai iya gujewa Destiny, there is nothing more for me to say saidai am sorry for hiding the truth from you all this while, nayi hakan ne dan kada in tada miki hankali a lokacin, I was waiting for d right to let you know of everything amma Allah yayi sai yanzu zaki sani, I promise you myself being married to Batuul bazai canza komai gameda Son da nake miki ba Ajiddeh, ki kwantar da hankalinki ki d'auketa as a sister, kinga yarinyace sosai, help in all ways you can, in kikayi min haka nasan son da kike min dagaske ne, I want to have that Baby Ajiddeh", ya k'arashe maganan tareda cupping fuskanta a tafin hannunshi, a hankali ta janye fuskarta daga rikon da yayi mata tace "Ka gama?", ta tambaya tana kallonshi a k'ek'ashe, shi da kanshi yasan he have wronged her ta kowanne b'angaren, babu matar da mijinta zaiyi aure ba tareda saninta ba har sai matar ma nada ciki snn ta Sani kuma ta yadda hankali kwance, bazai biyewa duk wani shirme da zatayi mishi ba yanzun dan yasan ranta ya gama b'aci, ta ja wani arnen tsaki tace "kai duk zamanka duniya ka tab'aji ance familyn mu mun zauna da kishiya?, toh ko tarar da ita mukayi sai ta bar mana gidan bare kuma har har tazo ita ta sameni in zauna da ita, bamai yiwuwa bane wlhy, gidanmu zan tafi, in ka tashi ka aiko min takaddar sallama ta dan ban zama da munafiki, ita waccan shegiyar da tayo shege daga waje kake ikirarin matarkace sai kayi zaman da ita amma badai ni ba" ta k'arashe tareda mik'ewa zata tafi, da sauri yasa hannu ya fizgota ta fad'o kanshi, idanun nan nashi da bata son gani su ya zuba mata, kallon da yake mata yasa ta d'auke kanta da sauri, hannu yasa ya juyo da fuskanta yace "babu saki a tsarina, nace miki am sorry for everything, ki fad'i min duk abunda kike so zan baki shi amma babu cikinku wacce ta isa tasa na rabu da d'aya, and mind you, don't try anything stupid dan duk lokacin da kikayi gigin barin gidan nan bada Sanina ba, you ain't gonna like it", kwace kanta tayi daga rikon da yayi mata ta fashe da kuka tace "munafiki mey xakayi da ya wuce wanda kamin, ai wlhy ka janyowa kanka, kwanciyar hankali ma ka rasa at this very minute, mugu kawai, sai meye in baka sakeni ba, ai ba kai kad'ai keyin auren ba, gidanka kuma sai na bar maka shi kaci uwar da zakaci da kaida karuwar taka", rintse ido yayi dan bayason losing cool d'inshi, amma yarinyar nan na d'aga mishi hankali har cikin ransa yake jin dacin sunan da take k'iran Batuul da, mik'ewa yayi bayan ya bud'e idonshi ya tashi ya bud'e side drawer d'in d'akin ya fiddo makulli yayi waje, dan yasan zamanshi d'akin zaisa yayi abinda bashi da niyya, yana fita yaja k'ofan ya kulle ta baya ya bar makullin daga jiki




         Yana fita ya waiga ya kalli d'akin Batuul, da hanzari ya sauk'a ya fad'a mota ya tada ya d'au hanyan Inda zaije siyowa Batuul abinda take buk'ata, cikin 15mins ya siyo komai ya dawo mota dan hankalinshi sam bai kwanta ba barin Batuul da Ajiddeh da yayi a gida tare su kad'ai dukda ya rufe musu k'ofa su biyun duka, yana parking a gida ya fito ya d'ebo wasu daga cikin ledojin yayi sama dasu, d'akin Ajiddeh ya bud'e ya lek'a yaga babu kowa cikinshi, da mamaki ya k'arasa shiga jin motsinta a toilet yasashi sauk'e ajiyar zuciya ya ajiye ledojin dake hannunshi ya fita ya sake rufe k'ofan ta baya yayi d'akin Batuul, a kwance ya tadda ta kan gadon, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin she is fine, wani irin feeling yakeji sauk'e idonshi da yayi a kanta, duk wannan stress da damuwar da ya kwaso gun Ajiddeh ji yayi duk ta b'ace mishi, idonta a kanshi har ya k'araso cikin d'akin, kwanciya yayi bakin gadon snn yasa hannu ya jawota jikinshi, ido ta wara zata b'ara mishi baki yayi saurin d'aura d'an yatsanshi kan lips d'inta yana kallon Idonta, da sauri ta rintse su hakan da tayi yasashi yin murmushi, y'ar crop top d'in dake jikinta yasa hannunshi ciki ya d'aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta bud'e idonta jin inda ya d'aura hannunshi, hannu tasa zata ture nashi hannun ya rik'o hannun nata da d'ayan nashi, a hankali yayi brushing lips d'inta da yasa gasp escaping lips d'inta, ta shiga k'ok'arin turashi, dariya yayi yace "Hey Babyna keh missing d'ina,  am just checking on him", baki ta zumb'uro mishi ta d'auke kanta tace "Ina abincin da zanci? yunwa fa nakeji", ta k'ara turo baki ta juya mishi baya, da hanzari ya mik'e yace "Damn, I was checking ko Babyna na lafiya that I forgot kinajin yunwa, sorry let's get going", jin har ya manta da yunwar da takeji yasa hawayen dake idonta silalowa, shi dai kawae ta haifa masa yaro, hannunta ya kamo yace "muje", tace "ni baxanje ba, ba babynka yasa ka manta inajin yunwa ba, ka bashi abincin yaci ni baxan ci ba", ta koma ta kwanta, dariya ta bashi ya mik'e cak ya d'auketa, ihu ta fara mishi ya sauk'eta tana cewa "Ka sauk'eni Yaa Abu, ina zaka kaini", daidai neck pulse d'inta ya rank'wafo har tana jiyo numfashinshi da ke kalar mint na bugun fatar jikinta yace "Babyna zanje inyi feeding, just stay still before in jefar dake downstairs", aikam kamar cewa yayi taci gaba haka ta dinga wuntsila k'afa, bai bi ta kanta ba ya ya bud'e k'ofa ya fito, har saida ya bud'e mota sannan ya sata ciki ya zaga ya shiga, tana zama idonta ya fad'a kan ledojin, da sauri ta janyo ta shiga bud'ewa ta ciro ice cream d'in ta shiga sha, zama yayi da murmushin da baisan sanda yayishi ba shimfid'e a fuskanshi yana kallonta, a hankali ta juyo da lumsassun idanunta ta sauk'e kanshi, ganin kallonta yakeyi yasa ta d'an tsuke fuska ta mik'a mishi robar tace mishi "you want some?", murmushi yayi ya d'auke kanshi yace "No, kisha kayanki", ta tab'e baki itama taci gaba da shan abinta, saida ya tada motar ya fara tafiya snn ya juyo ya kalleta ganin yanda ta dage sai shan ice cream d'in takeyi yace "bad manner", da sauri ta kalleshi jin abinda yace mata ta zumb'uro baki tace "mey nayi?", mirror dake gefenta ya jawo mata ta kalli fuskanta, dariya ta fashe da ganin abinda ke fuskanta, ice cream d'in ne gaba d'aya gefen fuskanta, ta kalleshi ganin baya dariya itama ta tsaida nata tace "toh ai sune basu saka tissue ciki ba", daidai nan yayi parking k'ofar d'aya gidan nashi, robar ice cream d'in nata ya jawo ya d'auki cokalin dake ciki ya shiga goga mata a lips d'inta, tsuke fuska tayi tace "you messed my face" tasa hannu zata goge yayi maza ya rik'o hannunta ya d'age mata girarshi yace "No you look cute", ta zumb'uro baki tace "ba yanzun nan kace min bad manner bane", yace "No ai yayi miki kyau", ta sake jawo  mirror tana kallon kanta ta fashe da dariya tace "kamar moustaches d'in santa ko?" shikam kallonta ya tsaya yi ganin dariyar da takeyi ya k'ira Sunanta a hankali, juyawa tayi ta kalleshi jin mey zaice, taji yace "You are cute", kallonshi takeyi ta kasa d"auke idonta kanshi, a hankali yayi leaning ya shiga kissing d'inta har saida ya lashe duk cream d'in da ya bata mata fuska, daga nan ya d'auketa cak yayi waje da ita.




      Suna barin gidan motar su Farida ya shigo gidan, saida tacewa David "Thank you" snn ta shigo gida, tun daga parlour take kwalawa Batuul k'ira taji shiru, kitchen ta lek'a taga bata nan, sama ta haura d'akin Batuul d'in nanma bata nan sai wayarta dake ajiye kan gado, tana fitowa d'akin taji ana bubbuga k'ofar d'akin Abu da k'arfi kamar ana shirin b'allashi, a tsorace ta k'arasa k'ofar d'akin, ganin mukullin a jiki yasa jikinta na b'ari ta kama ta bud'eshi, da k'yar ta iya sa hannu ta tura k'ofan, da mamaki ta tsaya kallon wacce ke cikin d'akin tana dukan k'ofar, wani dogon tsaki ta ja ta juya xata bar wajen, Ajiddeh da dama jira take ta fixgota da karfi tana huci tace "Uwar ki kike ma tsaki bani ba,"

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now