💖💝BATUUL 76💖💝

11.4K 493 30
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




       Har jirginsu Aunty Jainaba ya sauk'a Nigeria hankalinta yaqi kwanciya kan abinda Ajiddeh ta fad'a mata, inko gaskiya ne ai da sun kad'e dan kishiya ba abar so bace ko cikin mafarki, bazai ma yiwu bane, Aliyu ya raina musu hankali, amma koma menene zasuyi maganinshi maci amana kawai, so take kawai ta isa gida ta fesawa Mummy lbrn cin amanan da d'an matsiyatan nan yayi musu, Dan ba Ajiddeh kad'ai yayiwa ba, ko jiran driver batayi ba ta tari Taxi tayi hanyar gida, suna isa tacewa driver taxi ya jirata a kawo mishi kud'inshi ta shige cikin gida jikinta sai b'ari yakeyi kamar ita aka yiwa kishiyar, a hakimce ta tadda Mum d'in Ajiddeh zaune a parlour, da mamaki Mum ke duban Jainaba da ta fad'o cikin d'akin ko sallama babu tace "Keh kuma daga ina haka kamar ana tunkud'oki, mey ya faru kika dawo da wuri haka keda zakiyi har sati biyu", waje ta nema ta zauna jiki na b'ari, Mummy ta gyara zama tace "Keh ko lafiya haka, Ya Ajiddehn take?", gumin da takeyi ta goge snn ta shiga korowa Mummy bayanin duk abinda ya faru tun zuwanta har zuwa zancen cikin dake jikin Batuul da kuma abinda Ajiddeh ta fad'a mata kan cewa Batuul matar Aliyu ce, wani irin zabura Mummy tayi daga kan kujerar da take zaune ta dafe k'irji tana rafka salati tareda cire d'ankwalin kanta da ya bayyana gashin kanta mai tsawo da shek'i tana fifita dashi dan wani irin zafi takeji duk da Acn dake aiki, tace "Jainaba bana son zancen banza, wane Aliyun ne yayi aure?, ba dai na Hawwa ta ba, ina ba Aliyun Ajiddeh bane ya k'ara aure" Jainaba dake zaune ta mik'e tace "Shi d'in ne kuma ma dan wulak'anci irin nasa har ciki ke gareta yanzun, wannan tsinanniyar yarinyar wai itace matarsa duk ba a sani ba", Cikin d"aki Mummy ta shiga sai gata rik'e da gyale da jaka tana ta sababi tace "Ni Bilkisu zata wulak'anta, duk burin da naci kan Ajiddeh? Su da zaman lafiya saida su ga wasu nayi, shima munafikin Aliyun shine harda dukar min y'a ko?, toh duk sai sunci ubansu gabaki d'ayansu dan sai nasa sunyi kuka da idanunsu munafukai kawai, wannan ciki sai ya zama sanadin rushewar farin cikinsu baki d'ayansu, sai na nuna musu kan kishiya babu abinda bamayi, munfi k'arfin zama da ita koda tadda ta mukayi bare kuma an kawo mana ita a munafurce" ta fad'a tareda wani d'an guntun murmushin takaici ta kalli Jainaba da ta koma ta zube kan kujera tsabar gajiya tace "Yaya ina kuma zamu? Ni wlhy duk na gaji, in na huta sai mu tafi", ta watsa mata wani irin kallo tace "bakida hankali inaga, ace miki anyiwa Ajiddeh kishiya keh har lokacin hutu ke gareki?, ai in kinga mun huta to sai naga na d'agawa Bilkisu hankali itada Zuri'arta baki d'aya naga sun wulak'anta sun d'and'ani bakin cikin da suka jefa y'ata snn zaki samu damar hutawa, kan y'ay'ana biyun nan babu abinda bazanyiwa mutane ba, bare ma Ajiddeh wacce tafi komai soyuwa a gareni, duk burina yana kanta, sun jawowa kansu, maza ki tashi muje", Rai b'ace Jainaba ta mik'e da k'yar dan duk jikinta ciwo yake mata ga gajiya suka fita waje, Sadi driver na ganin Mummy ya washe baki tareda k'arasowa wajenta  yace "Hajiya fita zamuyi kenan?", tace "Ehhh maza d'auko mota, Kuje zamu yanzun nan", Jainaba batace komai ba sai bin Mummy da takeyi a baya kamar wata doluwa, saida ya fita da motar bayan sun shiga sun zauna ta dubi Mummy tace "wai gun wa zamu a Kuje?" Mummy ta kad'a kai tace "wajen wani Malamin zamu mana, wannan ma yafi kowa iya aiki danshi baima San Allah ba, Matsafine sosai na bugawa ma a Jarida snn shi ba kowa yakewa aiki ba sai in kanada connection, kin dai San y'an cikin k'auyen garin Abujan nan da basu San wani Addini ba, toh gunshi zamu, Hajiya Ramatu ta dad'e da cemin zata kaini gunshi ban samu munje ba sai kwanaki ne dana rakata kuma naga aikinta ya kammalu in no time kinga har ta samu ta auri wannan Ambassador, matanshi kuma sun shiga gari yanzu daga ita sai y'ay'anta da ta kawo suke zama a can, y'ay'an mijin nata ma ta koresu kuma mijin bai isa cewa komai ba  , yanzunma can d'in zamu, dan ni na tabbata banida mak'iyi kamar wanda zai tab'amin  y'ay'a", a bakin gate suka tadda driver d'in taxi shida Mangal yanata mishi zuba, Sadi Aunty Jainaba tacewa ya bada kud'in motar ya ciro ya mik'a suka d'au hanyar Kuje, saida suka shiga can cikin k'auyen snn tacewa Sadi sun kawo, nan yayi parking suka fito suka isa y'ar bukkar hatsabibin bokan nasu mai suna Namurje




💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now