💖💝BATUUL 9💖💝

6.8K 382 2
                                    





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



        K'arfe biyar 5:00 daidai adhan din  sallah Asuba ya fara dai dai lokacin Abutturab ya farka daga bacci, addu'ar tashi daga bacci yayi, k'afafuwanshi ya sauk'ar daga kan gadon a hankali, tashi yayi ya isa inda comfy fararen towels dinsa ke rataye , guda ďaya ya janyo, kayan baccin dake jikinshi ya cire sannan ya ďaura towel din ya shiga toilet, brush yayi ya watsa ruwa  sannnan ya haďa da alwala ya fito, closet ďinshi ya buďe ya ciro farar jallabiya ya saka bayan ya goge ruwan jikinshi da towel, gaban mirror ya koma ya fesa turaren jéan pául Gaultiér ya k'ara da Hugo sai Arabian oud ya shafa, abin sallah ya shimfiďa yayi nafilfili, bayan ya idar ya karanta suratul Mu'minun cikin murya mai daďi, tashi yayi ya fita masallacin dake manne a jikin gidan daga waje, yana k'arasa yayi raka'atul fajr sannan ya zauna jiran Ladan ya tada sallah su fara, k'arfe 5:40 ladan ya tayar suka fara sallah, suna idar da sallah bayan y'an azkar suka fito daga masallacin, Abui da Sadiq ya hango ya k'arasa inda suke, "Nda wattu" yacewa Abui tare da mik'a mishi hannu, Abui ne ya amsa mishi da kélewa sélai, Sadiq ne shima ya mik'o wa Abutturab hannu suka gaisa, suna tafiya Abui ya k'ira sunan Abutturab, "yaushe ne tafiyanka" Abutturab ya amsa da "Na so in tafi on monday but naga i have things to cover before meeting dina da minister on tuesday, so i have decided to leave tomorrow monday", Abui yace "okay sai kayi rescheduling flight dinka to gobe, kuma ka fad'awa Ammah dan bata sani ba, mu sai next week dawwanmu inaga" yace "okay Abui" sannan suka k'arasa cikin gida kowa yayi ďakinshi


     
       Hasken ranar da ya hudo window ďakinta ne ya sata buďe idonta a hankali, ranan da ta gani ne ya sa ta wara y'an madaidaitan idonta ta dubi agogon dake kan bed side drawer taga 6:30, da tsalle ta tashi daga kan gadon, gashinta mai tsayi da shek'i da ya baje tana bacci ta kama ta haďe su in a messy bun, toilet ta shiga ta kuskure bakinta da Listerine mouth wash tayi maza tayi alwala ta fito, sallah ta tada , bayan ta idar tayi azkar ta fito daga d'akinta ta bud'e ďakinsu Ahmad, fridge din ďakinsu ta buďe ta ďauko ruwan sanyi ta shiga kwara musu, a firgice kowannensu ya tashi suna mitsitsika ido, Sa'eed ne yace mata "haba Yaa Batuul yanxu kuma mey mukayi kika tashemu da ruwan sanyi", dukkansu ransu a b'ace suna kallonta suna jiran suji mey sukayi da ta katse musu bacci, "Y'an rainin wayo kunga ban fito sallah ba shine babu wanda yayi knocking min k'ofa, ai tunda baku ganni nazo gaida Baa ba sai kuzo ku dubani, amma kowanne da yaje masallaci dawowa yayi yaci gaba da baccinshi, sai yanxu nayi sallah asuba, yan rainin wayo kawai, Khalil ne yace " toh mu mun san baki tashi bane, kuma ai Aunty ma munsan zata tasheki" Harara ta watsa mishi, Ahmad kam ko uffan baice ba dan ya san harda haushin jiya yasa ta zuwa da watsa musu ruwan sanyi suna bacci, Mus'ab ma baice komai ba, tana faďan dalilinta na watsa musu ruwa yaja bargonshi ya kwanta dan inda sabo sun saba da masifanta, saida ta gama faďanta sannan ta juya tare da banko musu k'ofa ta fita, k'asa ta sauko taga babu kowa ta koma d'akinta


     
       11:00 ta sauko cikin abayar Al layl tayi kyau sosai, fuskanta ba komai sai kwalli da ta saka, duk y'an gidan na parlour, Su Ahmad ne suka bita da kallo ransu a b'acen abinda tayi musu ďazu,itama palon taje bayan ta gaida Baba da Aunty ta sami waje ta zauna, Baba ne yace mata "Batuul tafiyanmu gobe ne dan haka yau zakuje ku gaida su Yayya da kowa da kowa, meeting dina tuesday ne so dole mu tafi gobe, kuma kinga graduation ďinki saura two weeks, sai ki fara shirye shirye ko" tace "yo Baa", Aunty ce tace mata "kan naki ya dena ciwon", ita ta manta ma gaba ďaya da tayi ciwon kan k'arya, tunowa tayi da abinda ya sata yin k'arya, ďan k'aramin tsaki tayi daga ciki, a ranta tace wannan mugu ne dagaske shiyasa Farida bata sonshi tafi son Sadiq, da sauri tacewa Aunty, " eh da nayi bacci na tashi ya dena", "sai kije kici abinci ki fito mu tafi dan muna da wajen zuwa dayawa a yau" toh tace sannan ta nufi dinning ta bubbuďe food flaskses da kwanunkan dake kan dinning ďin, plate ta ďauka ta saka pancake guda ďaya da strawberry syrup sannan ta ďauki Fanta ta zauna ta ci a hankali har ta gama ta dawo palon tace ta gama, Aunty ce tacewa yaran "toh ku tashi mu tafi Baa Liman na jiranmu shi zai kaimu", dukkansu sukayiwa Baba sallama suka fita, wata range rover 2013 suka dosa dukkansu, Baa Liman ne ya buďe kofan driver ya shiga, motan duk ya hargitse da surutu kowa yana faďin ga wak'an da yakeso a sa, daga k'arshe ne Batuul tace a saka musu wak'okin Wael Jassar, ana sawa duk suka fara bin wak'okin shi na farko a album din 7aareg damohom, motar cike da hayaniya ba a jin abinda wani ke faďi har suka isa gaban wani gate sukayi horn, mai gadi ne ya buďe musu su ka shiga, basu bari an gama parking ba suka buďe k'ofofin motar suka fito, da gudu suka shiga gidan suna faďin *yayya ishena*, *yayya ishena* Yayya munzo, Yayya munzo)da kanuri,  wani ďaki suka buďe suka shiga, ďan madaidacin parlour ne mai kyau sai k'anshi turaren wuta yake da sanyi, suna shiga suka nufi wajen wata tsohuwa fara sol, dukda ta tsufa amma kyanta na nan, anyi mata kitson gaba da ya zubo daga gefe, na bayan kuma ta tufke shi, murmushi tsohuwar tayi ta rungeme yaran, Batuul na shigowa taje wajenta ta ture yaran daga jikin tsohuwar tare da cewa "Ku ďaga min takwara kar ku ballamin ita, tunda kuma bana yiwa takwarorinku haka", rungume tsohuwar tayi sannan tace mata Yayya *tussuna nya rukéi*, (na daďe ban ganki ba, nayi missing ďinki), Yayya tace mata " *nda rui sha, jirem géi*(dubeta kamar dagaske ban yadda ba), Aunty ce ta k'araso ďakin ta zauna sannan suka gaisa da Yayya, cikin girmamawa suka gaisa sannan yayya ta k'ira daya daga cikin masu aikinta, "ki kawo musu abinci da kayan sha ki jera a kan dinning,cikin kanuri ta faďi maganan don bata jin Hausa, sunajin abinda yayya ta faďa kowa ya fara faďan choice dinshi na abinda zaici, duk saida aka kawo musu abinda sukace sunaso aka jera musu, a gidan suka wuni har dare



       k'arfe goman dare Baba ya iso gidan yayya shima, bayan sun gaisa da yayya sun ďan tab'a hira yace su tashi su tafi dan gobe flight dinsu eleven ne,tsaraba dayawa yayya ta haďa musu ta saka masu aikinta su kai musu mota, bayan kowa ya gama shirinshi zasu fita daga ďakin yayya ta k'ira Baba ckin ďakinta, zama tayi a kan gado shi kuma ya zauna a k'asa kanshi a duke, magana ta fara kamar haka "Batuul tace min ta gama sashen karatun nan nata amma zataci gaba, kuma har waje naji tana cewa zata, toh ni bance kar taci gaba ba amma ban yadda har waje ba, in kuma har wajen zaka fita da ita toh lallai saida mijinta , haba wane karatu ne haka da tunda aka haifi mutum yakeyinshi bai k'are ba, yarinya shekara sha shida zata shiga na bakwai amma babu abinda takeyi sai boko, toh inma uwarta ke zugaku da kai da Batuul ďin ni bazan ďauka ba, bazan yadda yarinya tayi ta girma babu aure ba, ai uwartata ma abinda ya sa na k'i ta kenan lokacin aurenku wai tana boko, toh mutane da dama ma ai sunyi bokon a gidan mazajensu, dan haka Batuul baza ta ci gaba ba sai tayi aure", duk maganan nan da tayi cikin kanuri tayishi, tunda ta fara magana Baba bai ďago ba sai da ta gama, a sanyaye ya ďago kanshi yace mata "In sha Allah yadda kikeso za ayi Yayya, nima ďin bana son fitanta waje karatu babu muharrami, dan haka zan duba yadda za ayi", Yayya tace "yawwa gara a duba , Allah yayi muku albarka, toh yaushe ne tafiyan naku gobe" yace "11" tace Allah ya kaimu ya kiyaye hanya sannan ta fito yana biye da ita a baya har suka k'araso parking lot, yaran nata tsokananta har Babansu ya tayar da motan tana ďaga musu hannu har suka fita daga gate ďin

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now