💖💝BATUUL 20💖💝

6.9K 345 1
                                    





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



    K'iran Ajiddeh ne ya fara shigowa wayanshi, ansawa yayi tare da yi mata sallama, "salamu alaiki zawjati", tare da wani irin murna takeji kamar ta ganta a gabanshi, wani murmushi ta saki haďe da cewa "baby an ďaura, am officially yours now", murmushi yayi tareda girgiza kanshi yana mamakin Ajiddeh ko kaďan bata jin nauyinshi ko kunya, "In sha Allah forever" yace, zata sake magana kenan yace wasu mutane suka zo yi mishi murna, ce mata yayi "hold on wife, zamuyi magana anjima, am busy over here", da murnan sunayen da ya k'irata yau ta katse wayan, gaisawa yayi da mutanen dake gabanshi, jama'a sai k'aruwa sukeyi suna mishi murna tare da yi mishi fatan alheri a rayuwan aurenshi, walima suka wuce daga wajen ďaurin auren a state hotel, k'arfe ďaya suka gama walimarsu suka wuce airport daga nan, a airport sukayi azahar gaba ďayannsu, 1:45 sukayi boarding plane, k'arfe uku dai dai sukayi landing a Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, basu isa gida ba sai biyar saura, a gajiye ya shiga bayan an gama kai mutane masaukinsu,



   Bayan su Batuul sun gama cin abinci, wajen k'arfe uku Aunty ta ce su shirya suje gidan Ammah, ita yau baza ta samu zuwa ba, in sunje su gaisheta kuma zasuyi waya, dan gudun magana Batuul ko attempting saka abaya ma batayi ba, wani peplum blouse da skirt na atamfa ta saka, ta samu k'aramin pearl pebdant ďinta da stud masu kyau suma ta saka, ta ďauki k'aramin mayafi ta yana a kanta, Addua take a gama bikin nan ko zata huta da yawo, Baa Liman suka sa ya kaisu, k'arfe huďu suka isa gidan, gidan a cike yake da mutane kowa nata hidima, gaishesu suka rik'a har suka isa ďakin Ammah, basu sameta ba a ďakin ba, ďakin Farida sukaje , da sauri Farida ta janyo k'ofar dan kamar ba ďakinta ba, side ďin Abui ta jawo hannun Batuul sukayi tana cewa Batuul "ni in zanyi aure baza a zauna a gida ba, dubi fa gidan kamar ba shi ba kuma fa masu aiki na ta gyara amma kamar basayi", "dama haka taro yake, sai an kwana biyu zakiga gidan ya koma daidai", suna isa side ďin Farida ta murďa k'ofan ta shiga, Ammah ta tarar ita da Aunty Amna suna zaune a ďakin bak'i na side ďin Abui tana yi mata bayanin wani abu, ga robobi nan manya manya a gabansu cike da kaji da snacks, k'arasawa sukayi daga ciki, Farida ce ta fara gaida Ammah da Aunty Amna, sai Batuul, bayan ta amsa gaisuwan ne tacewa Batuul "Bitti sai yau na ganki tunda aka fara bikin nan, lafiya bakya zuwa", kai ta sunkuyar sannan tace mata "Ammah ina zuwa, shekaran jiya ma naje wushe wushe", " toh yayi , madallah, ďazu tela ma ya kawo kayanku na dinner na sa a ďinka muku, sai kuyi shiri anjima kuje kunji", toh kawai Batuul tace amma ba wai dan ta saka zuwan a ranta ba, suna zaune su Ammah kuma nata bayanin yadda za a kai kayan nan gidan amarya, mik'ewa Farida tayi ta fita, shigowa tayi ita da wata yarinya ďauke da plates a hannayensu na abinci, ajiyewa tayi ta zauna yarinyar kuma ta fita, cewa Batuul tayi ta taso suci abinci, mik'ewa Batuul tayi tazo kusa da ita ta zauna, ďan kwalin dake kanta ta cire ta ajiye daga gefen gadon sannan suka fara cin abinci, sallama akayi a k'ofa, Sadiq ne ya shigo ďakin , sai da ya gaida Ammah da Aunty Amna sannan ya zauna, Ammah ce ta dubeshi tace "kun dawo Sadiq, ya hanya, anyi lafiya babu matsala dai ko", kai ya girgiza tare da cewa "Alhamdulillah Ammah kunyi k'ok'ari mutane kamar turo su akayi a wajen ďaurin auren nan, komai ya tafi lafiya", cewa tayi "Alhamdulillah , dama haka nake son ji, Allah ya sanya Alheri, Allah ya basu zaman lafiya" dukkansu suka amsa da Amin, Farida ce tace "Yaa Sadiq shikenan yanxu Yaa Abu zai bar zama a gidanmu, shikenan daga nan sai kai gidanmu zai zama daga Abui sai Ammah sai ni, zanyi abinda nakeso", dariya ma ta bashi yace mata "zama gadin gidan zakiyi ashe, ai nima sai kin rigani barin gidan nan, waye ma zai barki ki zauna, next year kema by now munje maiduguri har mun dawo", b'ata rai tayi tare da zumb'uro baki tace "Ammah kin ga Yaa Sadiq ko", kamar ba ita ta fara hiran ba, "Sadiq ka dena damun ta tana cin abinci", mik'ewa yayi yace "Ammah bari inje in dawo", tace "okay sai ka dawo", Batuul ji tayi sun birgeta, inama tana da yaya itama, amma irin Sadiq ba iri Yaa Abu ba dashi bama a ganin dariyanshi, Sadiq na fita yayi hanyan su ya haďu da ango, tsaidashi yayi yace "Abui ya shigo gidane naganka a side ďunshi, ce mishi yayi "No Ammah na ciki, daga wajenta nake, yace "okay let me get to her", k'ofan falon Abui ya buďe, yana saka k'afa Batuul dake ciki taji gaba ďaya ta zama restless, bugun zuciyan ya fara, a hankali ta rik'a tauna abincin dake bakinta, k'ofar ďakin da suke ya tura ya shigo, cak komai ya tsayawa Batuul dan batayi expecting ďinshi ba at this time,  k'anshin turarenshi ya cika ko ina na ďakin, da sallama ya k'araso ďakin ya zauna a gefen gado, Gaisheda Ammah yayi sannan ya gaida Aunty Amna tana ta yi tsokananshi, Farida ce ta gaisheshi , ba yabo ba fallasa ya amsa mata, sau ďaya ya kalli inda Batuul take ya ďauke kanshi, ita dai bata ce mishi komai ba gashi nan dab da ita ya zauna, xame hannunta tayi daga plate ďin ta cewa Farida ta k'oshi, ccewa Ammah yayi "Ammah béri manyin, (Ammah inason abinci) banyi breakfast ba yau throughout bare inci lunch ga yamma tayi", Aunty Amna ce tace "wannan duk ďokin zama angon ne ya hanaka cin abinci" tana dariya, bai ce mata komai ba dan ya saba da tsokanar Aunty Amna, shi bai tab'a haďuwa da Aunty ďinshi mai tsokana kamar ita ba, Ammah ce ta dubi inda su Farida ke cin abinci ta lura da Batuul bata cin abincin, tambayanta tayi "bitti ya akayine bakya cin abincin", murmushi Batuul ta k'irk'ira tacewa Ammah "Na k'oshi Ammah", ce mata tayi "Bitti ďauko wa Abu abincinshi a palo, yana nan na shirya akan tray", a sanyaye ta mik'e tare da cewa toh, ida ta ajiye ďankwalinta ta duba zata ďauka taga akai ya zauna, bata ce mishi komai ba tayi hanyan palo, binta yayi da kallo har ta b'ace sannan ya ďauke idonshi a ranshi yace batason rufe kanta,dan yasha ganin gashinta on several occasions , mik'ewa Ammah da Aunty Amna sukayi suka fita dan sun gama abinda zasuyi, turowa kawai zasuyi a zo a ďauki kayan, inda Farida take zaune ya duba yaga tana ta faman dambe da k'ashi, ďauke kanshi zaiyi daga kallonta, sake dubanta zaiyi yaga abinda takeyi still kenan, tsayawa yayi yana kallonta yaga baza ta dena ba bayan ga wasu a plate ďin, harara ya zabga mata yace "ke in baza ki ci abinci nan ba tashi ki fita, kin zauna kina ta kokuwa da k'ashi ko ina zaki kai na cikin plate ďin" zumb'uro baki tayi tareda kinkiman plate ďin abincinta tayi waje a ranta tana faďin "ohh masifaffe, mutum ran aurenshi ma sai yayi masifa", ta fice abinta



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now