💖💝BATUUL 5💖💝

8.2K 455 4
                                    








Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




Tana shiga daki ta nufi inda towels dinta ke rataye, ta janyo daya sannan ta cire kayan jikinta da suka jiqe, ta daura towel din a kirjinta, ta nufi toilet din dake dakin nata, bayan minti goma ta fito tana kanshin shower gel da sabulu,da towel a jikinta, daya kuma a daure a kanta kamar turban, gashin goshinta ya kwanta lub lub, fuskanta ya kara haske da kyau, ta karaso gaban mirror dake cike da turararruka da yan kayan kwalliya da na shafa , ta jawo stool din mirror ta zauna sannan ta dauko man Makari, a hankali ta riqa shafa man kamar baza ta gama ba, bayan ta gama ne ta karasa gaban closet din kayanta, ta bude ta dauko peplum blouse da skirt din atamfa baqi mai pattern din purple ta saka à jikinta, kayan ba karamin kyau yayiwa jikinta ba, komawa gaban madubin tayi ta shafa powder a fuskarta sannan ta saka kwalli a idonta, ta shafa nude lipstick a bakinta , ta bude costume box dinta dake kan madubin daga gefe ta dauko dankunne da sarka silver masu duwatsu a jiki, sai abun hannu da zobe shima silver, sannan ta fesa turare, ta kalli kanta a madubin tare da murmushi sannan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da d'aukan wayanta,



bayan ta d'an daddana wayan ne ta kara à kunne tare da fadin "Hello Riri, shine kikace min a Ramat Square zakuyi sallah koh? kuma bakije ba",
Daga daya bangare aka amsa ana dariya tare da fadin

"Yo babe nan naje mana, i wanted calling you inji inda kike sai da na duba wayana naga ban fito dashi ba, You know anytime Yaa Abu na gida toh komai nawa doesnt go ryt"

Batuul tace "babu wani Yaa Abu, anytime kika samu matsala sai kice shine, toh duk ranar da zan ganshi sai na fada mishi"

Riri tayi dariya tace mata "dan baki sanshi bane ai, koh face dinshi idan kika gani zakiga ko smiling bayayi, brows dinshi kullum a hade, bayayiwa mutane ma magana wai surutu na saka mishi ciwon kai, kuma ko bashi zaiyi ba wai baza ayi a kusa dashi ba"


Batuul tace "all these apart, ni zanzo yau dan Baa yace nan da kwana hudu zamu koma dan yana da aiki sosai kuma gobe da jibi zamuje wajen su Yayya da sauran Family"


Riri tace "yawwa bae of earth,daman ina ta tunanin yadda zan ganki, I missed you soo much wlhy, kizo yanxu i have have So many things for you alone", Batuul tayi dariya tace
"You are not serious, ai sai na fadawa Baba tukunna, sai yayi approving zuwana"


Riri ce ta marairaice murya hade da cewa "nasan Baba zai barki sai dai in kece bakison zuwa, pls kizo, am bored over here, kuma kinsan Yaa Abun in yana nan ba a yawo "


"Batuul ce ta cemata ni ba ruwana and i told you zan fada mishi whenever i meet him"

"Ai bazaki iya ba nasanki, I wish zaki zo yana nan shima yaga wanda ya fishi rashin magana,ai mantawa ma nayi halinku daya nake fada miki"

"Ni dai yanxu a bar maganan, yanxu zanje in fadawa su Aunty zanzo wajenki" ,

"Aii sai kinxo"

sannan suka katse wayan, tashi tayi ta jona wayan a caji ta juya ta fito daga dakin har ta karaso kasa, ta sauka daga benen ta jiyo muryoyin yan gidan a dinning suna cin abinci, karasowa tayi wajensu, Mahir na ganinta yace "Yaa Batuul kinyi kyau", Hafix ma yabishi yace "kinyi kyau", tayi murmushi tace musu "nagode, kuyi shiru ku gama cin abinci, bad manners, talking while eating"

kujera itama taja ta zauna a gefen Baba daga hagu, Baba ne ya ce mata

"kinga kayan nan yayi miki kyau amma ba kiyi ta saka baqin kaya ba a kowane occasion",


Aunty ce tace "ai Y'ar kauye ce,"

ta juyo ta dubi Baba tai raurau da ido, yana ganin haka ya yace

"À ah Mamana ba y'ar kauye bace, ai kayan nayi mata kyau ko ?" ya tambayeta ,murmushi tayi sannan ta dauki plate, ta janyo wani babban tray da aka rufe da foil paper ta bude,Danderu ne na kaza yana ta tiriri da kanshin kayan yaji, fork and knife ta d'auka ta yanko kadan ta saka à plate din sannan ta sake janyo wani food flask din ta dauki masa daya a ciki tare da miyar masa, a hankali ta riqa ci ba tare da cewa komai ba har suka gama


Sun gama cin abincin ne suka tashi suka koma palo, Fa'iza da Janet ne suka zo suka gyara dinning din tare da kara turaren wuta à duka electric burners din gidan

Sai da kowa ya zauna ya nutsu sannan ta dubi Baba tace

"Baa inason inje wajen Farida tunda gobe da jibi we Will ne busy",

"Okay what time zakije ?" ya tambayeta

Cewa tayi "ko yanxu tunda naga its already after 12"


" Tunda su Baa Liman(Driver)suna hutu sai Ahmad ya kaiki dan ya fiki iya driving kuma bana Son kina driving ke kadai especially a Maiduguri da ba a bin régulations din driving "

"Okay Baa nagode, " Aunty dai bata ce komai ba tunda Baba ya yadda shikenan. Tashi tayi ta k'ara haurawa sama ta dauko jakarta ta chanel purple shima irin kayan da karamin gyale shima purple amma light, ta kara duba fuskanta a mirror sannan ta sauko

Tana saukowa taga Ahmad riqe da key din mota a hannunshi yana jiranta, karasowa tayi ta ce wa su Baba zasu tafi,

yayi musu a dawo lafiya sannan yace mata idan ta gama sai ta kira a zo a dauketa, tace "toh",


Tacewa Aunty sai Sun dawo, Aunty tace mata "ki gaishe da Ammah kice mata nima zanzo ko bayan mun koma Abuja ne", Toh tace sannan suka fita suka nufi inda akayi parking motocin gidan suka shiga wata Audi fara sol, Ahmad ne ya tambayeta anguwan da zasu bayan yayiwa mai gadi horn kamin yazo ya bude mishi kofan, ce mishi tayi Old GRA ne in munje zan nuna maka hanya, Ya juyo yace mata


"Yaa Batuul Allah kwatancanki akwai wahala yanxu sai mu kai two hours muna neman wajen da baifi muje a 20 mins ba "

"Tace toh ka bani inyi driving"

baice mata komai ba yaja motan suka bar gidan bayan mai gadin yayi musu a dawo lafiya







Tafiyan minti goma sha biyar suka isa gidansu Farida a old GRA ,Horn yayi aka bude musu gate suka shiga, suna shiga gidan bugun zuciyanta ya karu, ambaton Allah ta riqa yi har sai da taji ya dan ragu sannan ta bude motan ta fito daga ciki tare da yiwa Ahmad sai anjima akan in ta gama zata kirashi


Farida na Jin tsayuwar mota ta fito daga cikin gida a guje tazo ta rungume Batuul ta na ihun i missed you so much babe,


"Batuul ce tace mata sakeni kar ki ballani Baba ya hanani zuwa nan gaba"

Dariya tayi sannan tace "nasan Baba bazai hanaki zuwa ba, sai dai in ke zaki min halin naki ki qi zuwa", Batuul batace komai ba har suka karasa ciki ,tacewa Farida "Ammah da Abui da Sadiq fa ?"



"Ammah da Sadiq basu dawo ba inaga Sun tsaya wajen Ayyi, Abui yana Shehuri, Nida Yaa Abu ne a gida kawai shi kuma yana sama",

Batuul tace "okay",

sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta à fridge din, "kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke), Farida dake tidyn din Novels din ta dake baje kan gadon tayi dariya tace "kinsan ni bana shan Fanta, ki sauka downstairs ki bude fridge din falo xa ki samu fanta, lemme finish tidying this, I have a gist for you besty" Juyawa Batul tayi ta fita daga dakin tana sauka falo ta bude fridge taji ana saukowa a stairs ta dago da sauri kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take, ya karaso falon yace "Get me bottle water, Waye ya shigo gidan nn da mota Farida?" Shiru Batul tayi bata ce komai ba kuma bata dago ba, hka kawae gabanta ya fadi, ta rufe fridge din bayan ta ciro fanta da bottle drink din da ya bukata, lkci daya ta juyo suka yi ido hudu da shi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba ta ajiye masa ruwan kan center table snn ta haura sama da sauri, bin ta yyi da kallo lkci daya ya shiga kwada ma Farida kira, A bakin kofa Batul ta kusa cin karo da Farida, Farida tace "Kinga abinda nake gaya maki, I wonder y he is calling me ynxu" bata jira cewan Batul ba ta sauka kasa tace "Gani yaa Abu" a nutse yace "Who is she? I mean that girl that just left here, a gidansu ba a mata tarbiyan gaisuwa bne, is this the kind of frnds yhu are mingling with?"

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now