💖💝BATUUL 3💖💝

8.2K 452 6
                                    







Dedicated to *KHALLESAT HAYDAR*



Tuki yake cike da nutsuwa da kwanciyar hankali kan titin Kashim Ibrahim Road, ba a jin komai sai karar AC dake busa iska mai kanshi da sanyi har suka karasa masallacin suna ta fadin (Allahu Akbar Allahu Akbar Laillaha illalah Allahu Akbar kabira wal hamdulillahi kasira wa subhanallahi bukratan wa asilaah wa sallalahu ala nabiyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi wa sallama tasliman kabira) Abinda suke ta maimaitawa har suka isa masallacin kenan suka samu waje suka yi parking, da kanshi ya fito ya budewa Abui kofa Farida ma ta bude ta fito, ta miko mishi Sallaya daga bayan mota sannan ta kalli Abui tace bari in karasa side na mata, Abui yace "okay mamana, Allah yasa amsa ibadunmu yasa munyi a sa'a", tayi murmushinta mai kyau tace "Amin Abui", ta juya ta tafi

Bayan idar da sallah ne Aunty ta dauko jakarta ta ciro rafar yan dari biyar sabbi fil ta mikawa Batuul tace "gashi ki bayar sadaka, ai baba ya baki naki ko?", Batuul tace "ehh", sannan Aunty ta sake cewa "Ni zamu Je mota dasu Yusra dan Aabid ya fara jin yunwa in kin gama ki samemu" tace "toh Aunty", ta karbi kudin ta saka à jaka tace "I will soon be back" su kuma suka tafi

"....Hajiya Allah yasa anyi à sa'a Allah yasa muna da rabon ganin bad'i, Hajiya à taimaka Fisabilillahi"

Batuul ce ta karasa inda mutanen nan da Almajirai suke a zaune ta ciro kudi daga jakarta na bandir din dari biyar da na dari biyu ta fara rabawa bayin Allah dake wajen su kuma suna ta yi mata addua tana cikin rabawa ne wani iska mai hade da ruwa ya fara saukowa , take ba tare da shiri ba ta zube musu kudin dake hannunta ta juya zata bar wajen kenan taji tayi karo da mutum, ta dago kanta da iska ke kokarin cire gyalen da sauri take fadin "Hey am sorr.....", bata samu karashe maganar ba sabida yadda taga mutumin ya tsaya yana kallonta dogo ne sosai dan sai da ta mikar da kanta sosai kamin ta karashe ganin tsawonsa , kyakyawa ne sannan ba fari bane baqi ne amma baqin shi mai haske ne, yana da side burns sannan yana da long chiselled hanci da mitstitsin baki dake zagaye da millionnaires belt duk da akwai hula akanshi sai da ta hango curly gashin kanshi kanannadadde cikin hulan, bai rufe ba haka ma gashin gira da lashes dinshi bakake ne, cikin seconds da basu fi uku ba ta gama kare mishi kallo tayi sauri ta saukar da kanta kasa dan hawaye taf ya cika idonta, bugun zuciyanta ya karu kamar zai fito, sosai irin kallon da mutumin ke mata ya sata jin wani iri, ga mugun buguwa da heart d'inta keyi

ya bude baki kenan zaiyi mata magana cikin sauri ta matsa baya daga wajen bata tsaya jin komai ba ta juya cikin sauri sauri da dan gudu ta karasa inda tayi parking Mota ta bude ta shiga ta jefa jakanta baya , tana zama ta sauk'e ajiyar zuciya tareda da lumshe ido, mutumin nan ta gani kamar yanzu yake kallonta, Aunty ta juyo ta dubeta tace "lafiya kike ajiyar zuciya ?", Tayi maza ta bud'e ido tace "Aunty ruwan nan da nayi escaping bai jikani bane ya sani yin ajiyan zuciya", Aunty tace "toh ni yanxu karbi key mu tafi gida Yusra ta Ce min yunwa takeji, ga Aabid ma na rigima", Batuul ta juya bayan motar ta kalli wacce aka kira da Yusra tace "ba sai da nace kici abinci ba kamin mu fito ba kika ki wai ke sai kin dawo", Batuul ta juyo ta dubi Aunty tace "Janet fa har binta ta riqayi da abincin kamin ta saka mata kaya taqi, shine yanxu zata cewa mutane wai tana jin yunwa" bata ce komai ba Yusran sai zumburo baki da tayi, Batuul din ta sake ce mata "ki bude jakana akwai TWIX da cookies, ki dauko kuci ke da Hafix (Babich) ki bawa Fa'iza ma", sannan ta juya ta dauki tissue à gaban motar ta goge fuskanta da ya jike da ruwa, ta bude pidgin din motar ta dauko orbit mai flavor din pepper mint ta jefa à baki sannan ta gyara gyalen ta daura shi kamar dankwali sannan tayi igniting motar ta tada suka tafi

Tunda ta bar wajen yake tsaye yana kallonta har ta shiga motar suka tafi bai dena kallon wajen ba sai da yaji an taba shi ta baya ya juyo ya ga Wanda ya tabashi Ya kalli Wanda ya tabashin tare da Sakin Fuska yace "Massa ya akayi shehu ya bari ka bar wajen shi kuma ban ganka da shirin hawa ba", Massan yace "Man bari kawai ai bazan iya zama ayi hawan Durba dani ba, yanxu haka ma gudowa nayi", yace "kai mey kake yi anan kai kadai bayan naga Abui ma suna tare da Shehu", yace "yeah abu nazo yi amma banyi bama sai nan gaba", Massa yace "okay muje", sai da ya sake juyawa tare da sauk'e ajiyar zuciya kamin yabi hanyan da Batuul tabi tukunna suka juya suka tafi

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now