💖💝BATUUL 70💖💝

10.8K 521 47
                                    



Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*








         Wani mugun kallo yake yi ma Farida yace "kin wuce kin bar nan ko sai na zo na sameki, are you stupid ku ke min ihu haka a gida", duk da tsoron da taji hakan bai hanata dakewa tayi kamar ba da ita yake kamar ba, ta d'aga kai ta kalli su Ajiddeh da ido ya k'ank'ance da masifa, harara ta galla mata daga haka ta kuma maida dubanta kan Batuul tana washe baki tace "keh kin ga gashinki kuwa yadda ya wani dad'a cika yayi tsawo, meye sirrin 'yan mata, sea foods da salads kike ci ne? Kai Amma gaskiya gidan Yayana ya......", bata k'arasa ba taga yana tunkarosu, hanjin cikinta ne suka kad'a ganin haka, Batuul kam ko a jikinta sai dariya take, yana zuwa yasa hannu ya fincikosu a tare yayi hanyan stairs yana rik'e da hannunsu, ko lura da Ajiddeh da yayarta bai yi ba a sama, Batuul ta finciketa nata hannun daga rik'on da yayi mata ta tsaya cike da masifa tace "meye haka kake wani jana kamar igiya, ni nace maka inason zuwa sama ne?", da mamaki ya tsaya kallonta da har bai san lokacin da ya sake hannun Farida ba ta sulale a guje tayi sama abinta tana 'yar dariya, abubuwane kawai ke mishi yawo a kai, badai har yarinyar nan ta raina shi ba, ita kanta Ajiddeh da yayarta sakin baki suka yi suna kallonsu, juyawa Batuul tayi zata tafi ya fizgota gabanshi yana kallon fuskanta yace "Are you stupid?, ni kike ma magana haka, are you out of ur senses?" sauk'owa Ajiddeh ta shiga k'ok'arin yi daga saman da take tsaye dan bataji zuciyarta zata iya jure wannan abinda take gani gabanta, Aunty Jainaba ce tayi saurin riketa a hankali tace mata "keh shashasha tsaya, ki bari muga iya gudun ruwansu, ai inaga ma lokacin maganinta yayi a gidan, kema dai kinyi sakaci, meye na barin budurwa haka a gidanki", da mugun kallo "Ajiddeh ta dubi Jainaba tace "dalla can toh da duk abinda nake gaya muku Kun zata wasa nakeyi, toh yau koma menene, k'arshen xamanta yazo wllh" Batuul kam turashi ta shiga yi tana murgud'a d'an k'aramin bakinta tace "Ni ka rabu dani", duk wannan abinda sukeyi baisan su Ajiddeh na sama ba, matseta yayi jikinshi ya murd'a mata hannu yace "sai kin fad'a min sudden change of behavior nan naki, wato na fara miki wasa shine zaki rainani", had'e rai tayi hawaye taf idonta  ta turashi daga jikinta  tace "Ni kam ka sakeni", sauk'owan da yaji ana yi daga stairs ya sa ya daga ido da sauri, Ajiddeh ya gani tana sauk'owa furiously, with full rage a fuskanta, tura Batuul d'in yayi yana mata mugun kallo yace "b'ace min daga nan", juyawa tayi a fusace ta nufi stairs, karo  suka kusa yi da Ajiddeh ta koma baya da sauri ta raba ta gefenta xata wuce, a zuciye Ajiddeh ta fincikota ta hade ta da bango tana huci tace "Keh dan ubanki nayi miki kama da sa'ar uwarki da har zaki dinga min isa a gidana, to wllh xaman ki ya kare yau a gidana yanxun nan kuma ba sai anjima ba" turata Batuul tayi tace "kar ki sake ki sake gigin tab'ani wllh, zagi kuma wannan training din da aka maki kenan gidan ku, banida time d'inki", da haka ta juya ta haura sama ta bar ta nan tsaye, kwalalo ido jainaba tayi, Ajiddeh kam mutuwar tsaye tayi gun ta kasa kwakkwaran motsi, bata tab'a tunanin Batuul zata iya yin abu kamar wannan ba, a zuciye ta k'araso wajen Abu har wani rawa jikinta ya shiga yi sai hargowa take tace "Aliyu wlhy wlhy, kadai ji na rantse koh, toh yarinyar nan sai ta bar gidan nan yanxun nan, in kuma bata bari ba ni zan bar maka gidanka, ai dama nasan wannan kareta da kakeyi duk sabida kana samun wani abun gunta ne, wa ya sani ma ko zagayawa kakeyi gunta da daddare zaman dadiro kakeyi da ita, in ba haka ba, yaushe har zata rainaka ta rainani, dubi yanda ka wani rungumeta yanxu, ni za a rainawa hankali a wani ce  karatu tazo yi, toh koma meye ta zo yi ni bazan zauna da ita gidan nan ba , kuma in ba karuwanci takeyi ba Meye ma'anar aman da naga tana kwararawa jiya kamar mai ciki, ko daxu sai da naji kakarin amanta har sau biyu a daki, ohh wato karuwa ka kawo min gida ka.....", bata k'arashe maganan ba ya d'aga hannu ya sharara mata mari da ya gigitata, har Aunty Jainaba saida taji tsoron jin irin marin, Aunty Jainaba ce tayi saurin saukowa ta rufe mata baki tace "ke don uwar ki Meye haka kike yi, yaushe ne zakiyi hankali Ajiddeh, jibi fa irin maganganun dake fitowa bakinki, mijin naki kike yiwa magana haka?, dama bakida hankali ashe", tana yi tana k'iftawa Ajiddeh ido tayi shiru, fincike hannunta tayi daga rik'on da yayi mata, idonta har ya canza kala duk ya k'ank'ance hawaye na xuba idonta tace "ai ka mari aurenka Aliyu, akan gantalalliyar y'ar iskar nan kake mari na, ai ba sai ka mareni ba zansan mey ke tsakaninku, kuma yau zan bar maka gidanka", ta juya fuuuu tayi sama, Aunty Jainaba ce ta kwantar da murya tace "Aliyu ashe haka kake fama, ai ni ban tab'a sanin haka yarinyar nan take mara hankali ba, Dan Allah kayi hak'uri ba sai ka daka ta tata ba, kasan hankalinmu ba d'aya da naku ba, kayi hak'uri kaji?, zanje yanzu in ci uwarta, Allah ya k'ara maka hak'uri", kasa cewa komai yayi tunda yaji abinda Ajiddeh tace "wai cikine jikin Batuul, ciki kuma? toh wane irin ciki", a hankali ya maida dubanshi kan Aunty Jainaba yace "Ba komai", da haka ya barta nan tsaye ya haura sams, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye, bud'e k'ofan d'akin yayi ya shiga rai a had'e, Farida dake zaune tana ta zuba bata san lokacin da ta fasa ihu ta mik'e tsaye daga kan gadon ba tana yarfe hannaye, sau d'aya Batuul ta kalleshi ta d'auke kanta tana kallon Farida tace "Keh wai meye haka kika hau gado kina wani tsalle, ko ce miki akayi bouncing castle ne?", kallonta Farida tayi sannan tayi mata nuni da Abu dake k'arasowa cikin d'akin da baki, kallonshi tayi ta tab'e baki tace "toh mey zai miki?", fuska a daure yana kallon Farida yace  "get down", sake matsawa tayi jikin gadon tace "Dan Allah kayi hak'uri Yaa Abu, bazan sake ba", k'arasawa yayi bakin gadon ya fizgota yana mata mugun kallo, ihu ta fasa ta rintse ido tana jiran jin sauk'ar mari, "ni nayi kama da sa'an ko koh? all those warning I made clear to you basu shigeki ba?", a hankali ta bud'e idon jin bataji sauk'ar mari ba, kamar munafuka tace "Yaa Abu nifa bance komai ba, kawai cewa nayi ai ka Iya reno, Batuul tayi kyau", tsaki yayi ya hankad'ata har sai da ta fado daga kan gadon yace "Baxa ki kwana min a gida ba yau"



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now