💖💝BATUUL 13💖💝

6.4K 361 1
                                    









      Sai da ya gama aikin da yakeyi ya sauk'o yaci abincin, bai wani ci dayawa ba ya tashi ya shiga toilet ďin dake k'asa yayi alwala ya fita masallaci dan lokacin 3:50,  da ya idar ya dawo gida, tunda ya shiga yaci gaba da aikinshi sai kuma sallah ke tadashi, bai kwanta ba sai after 12, yana kwanciya bacci ya kwashe shi, washegari 6 ya tashi bayan yayi sallah asuba yayi wanka, jeans blue  ya saka da farar rigar max n spencer sannan ya ďaura blue Tuxedo ta giorgio Armani daga sama, kayan ba k'aramin kyau suka mishi ba kasancewanshi dogo, agogon ciélo ya mak'ala sannan ya fesa turaren karenbkelly da versace eros, k'arfe bakwai daidai ya gama shirinshi ya fita, CLS rose gold ya buďe ya shiga ya fita daga gidan, office ya wuce, a nan yaci gaba da aiki har sai da minister yayi mishi waya suka tafi sighting area da zasu yi constructing, shi ya bada shawaran contractors ďin da ya kamata ayi aiki dasu, shi kuma yayi musu designing plan ďin yadda wajen ya kamata ya zama, satinshi ďaya yana aiki babu hutu, a ranar satin ne su Ajiddeh suka dawo, yana office  12:00 yaga k'iranta da number ta ta Nigeria, gaba ďaya ma ya manta da yau zasu dawo kuma yace mata zai ďaukota in sun dawo, tsaki ya ďan ja kamin yayi recieving call, kamin yayi magana ta riga shi da murna tayi mishi magana "Hello Baby mun dawo, we just landed, yanxu ma kai nake jira, bazan bi su Mum ba ni", sai da ta gama yace "olryt gani nan zuwa", key ya ďauka yayi magana da PA ďinsa akan duk wanda yazo neman shi ya tashi for d day sai gobe, cikin girmamawa ta amsa da "Okay sir, sai ka dawo", yana fita yayi hanyan airport, awa ďaya da rabi ya isa, side ďin international arrivals yabi, waya ya ďauko zai k'irata kenan yaji an sa ihu daga bayanshi "Baby am here" ko bai juyo ba yasan Ajiddeh ce, da gudu ta taho ta rungumeshi kamar za a k'wace mata shi, "i missed you soo so much baby" peck tayi mishi a kumatu sannan ta ďan sassauta rik'on da ta mishi ta ďan kwanta a kafaďanshi, shi mamakin halin Ajiddeh ne ya hanashi magana, duk y'an gidansu na wajen har Dad da Mum ďinta amma babu ruwanta haka tazo ta mak'aleshi, janyeta yayi daga jikinshi yayi mata magana a hankali "sweetheart baki ganin akwai jama'a a nan infact gasu Mum nan " zumb'uro baki tayi tace "ai dama nasan bakayi missing ďina ba,  komai nayi is not right to you, wata ďaya  we didnt meet, i was just happy, kuma su Mum ai sun san ina sonka ne" bai sake ce mata komai ba dan yasan she wont understand, k'arasawa yayi inda suke ya ďan risina ya mik'awa Dad hannu, gaisawa sukayi ya juya ya gaida Mum, da murmushi ta amsa sannan , juyawa yayi ya gaida Yaa xee, a dak'ile ta amsa mishi, bai bi ta kanta ba ya cewa Dad muje, Mum ce tayi saurin ce mishi "No ai drivers sunzo da su zamu tafi, sai dai kai ku tafi da Ajiddeh", cewa yayi okay, sai da ya bari suka isa inda driver yake sannan sukayi inda motanshi ke pake, unlock button ďin jikin key ya danna ya buďe, k'ofar ta buďe ta shiga shima ya shiga ta ďaya bangaren ya tada suka tafi, hanyar Wuse II yabi da ita, kalonshi tayi tace "baby kace zamuyi discussing wani issue in muka  dawo", ta tsaya tana duban shi tana jira taji amsa da zai bata, sai da ya ďebi wajen 30 seconds tukunna yace mata "Yeah , inaso ne in turo gidanku batun aurenmu, i dont want to take long so ki faďawa su Mum", har ya gama magana ita dai ji take kamar a mafarki take, shirun da yaji yayi yawa yasa ya dubeta ya ga kallonshi take yace mata "you there", da sauri ta girgiza kanta tayi hugging ďinshi a cikin motar, sai da ta sake shi tace, "Aliyu i cant believe my ears, you just said zaka tura gidanmu though bamuyi grand proposal ďinmu ba but its okay, am super excited, I love you soo much baby, ai yau ma zan faďawa Mum, sai ta faďawa Dad" peck ta k'ara mishi sannan ta zauna da kyau tana ta jero mishi abubuwan da zasuyi na bikin


     Batuul kam tana can gida tana shirin grads ďinsu, da kuma murnan yau Farida zata dawo, dukkansu biyun kaya iri ďaya tayi musu ďinki ne kawai ya bambantasu, har takalma iri ďaya sukayi, taso taga Farida yau amma babu time, kawai driver ta tura ya kaiwa Farida nata kayan, a washegarin graduation ďin taje saloon aka wanke mata gashinta, sai da ta gama ta k'ira driver yazo ya ďauketa, tana shigowa gida taga kowa a palo, k'arasawa tayi ciki ta cire gyalen abayar jikinta ta zauna a kan kujera, su Ahmad ne suka fara cemata" inyeh su graduate, shikenan daga gobe kin tashi daga pupil", dariya tayi musu tace "as in, yanxu sai university, ku ku tsaya ma tukunna, ticket tara aka bani a school that means mutanen gidan nan tara ne zasu" ihun kowa shi zaije suka farayi, dariya tayi musu tace "ai sai dai kawai wasu su hak'ura dan bazai ishe mu ba, we are eleven and nine tickets ake badawa, so excluding Aabid still mutum ďaya bashida ticket, and i want you all there", da taga babu wani da is willing to hak'urane ta ciro wayarta tayi dialling Farida, tana ďauka tace " Riri kinsan meye, i have only 9 tickets mu kuma we are ten, kuma i didnt invite kowa ma, so if akwai extra inaso for one of us", cewa Farida tayi "dama ni am not inviting kowa, zan bawa Yaa Abu 3, sai Abui, Ammah da Sadiq, kinga inama da extra 2, "Yawwa babe, na aika Baa liman da kayanki sunyi daidai ko" inji Batuul, "sosai ma wlhy , thank you soo much", katse ta Batuul tayi tace " I hear you, who are you thanking", dariya Farida tayi tace sorry i gat to go Ammah na k'irana we will talk later, bye" da haka suka katse wayan, cewa y'an gidan Batuul tayi ai ta samu ticket ďin mutum ďaya duk daďi sukaji suka ci gaba da hiransu, k'arfe tara ta tashi ta hau sama


       Da murmushi a fuskanta ta buďe ido, k'iran asuban fari ne ya sata tunawa da yau wace rana ce, a hankali ta tashi daga kan gadonta ta shiga toilet, wanka tayi da brush sannan  tayi alwala ra fito, nafilfili tayi, ta godewa Allah da ya nuna mata ranar gama makarantan ta lafiya, Addu'a sosai tayiwa iyayenta da al'ummar musulmai, da ta gama tayi karatun k'urani, tana gamawa aka tada sallah ta tashi tayi, komawa tayi kan gado bayan ta idar da sallah amma ba bacci take ba, itama bata san tak'amaimai abunda zatayi ba dan murna, wayanta ta jawo ta k'ira Affan, yana ďauka tace "cousin of life" a hankali ya amsa mata kamar mai jin bacci, "Hello best friend what is it kika tadani da sassafe haka", ido ta wara tace "Affan dont tell me you are still on bed sleeping , its our day fa yau, our graduation day", ce mata ya sakeyi "Batuul saifa 9 o'clock and its still 7, i have two more hours to do everything", ce mishi tayi "ai yanzu zan k'ira Maa ince mata ko tashi sallah bakayi ba, Affan get out of that bed and get ready", katse wayan tayi batajira mey zai ce ba, haka ta k'ira Farida ma, ita ma hira sukayi tayi dan ta kasa bacci itama, sai da takwas yayi suka katse sukaje shiryawa, ďakin su Ahmad taje ta tashesu tace kowa ya shirya kar su b'ata mata lokaci, Janet ce tazo tace mata wata mata tazo nemanta, cewa janet tayi ta hawo da matar ďakinta, ita kuma ta juya ta tafi, tana ďaki sukayi knocking tace su shigo, wata mata ce fara siririya da murmushi a fuskanta suka shigo, wani ďan madaidaicin akwati a hannunta ta ajiye, sai da ta zauna sannan suka gaisa da Batuul, matar ce tacewa Batuul "yanxu zamu fara ko dan kince 9 ne event ďin naku ko", da ehh Batuul da amsa mata sannan tace "Light nude make up zakiyi min, ko foundation bana so a sa min, just my brows then eyeliner, i just want everything nude" murmushi matar tayi tace mata "Na gane but brows ďinki are full, ko za a ďanyi carving", a ah Batuul tace sannan suka fara, takwas da ashirin da bakwai suka gama, ba k'aramin kyau Batuul tayi ba, matar ce ta ciro mata kayanta a closet ďinta da takalmi da duk abinda zata buk'ata, da kanta matar  ta taimaka mata ta saka kayan, dogon gown ne bak'i, mai buďaďďan k'asa, wani gold plated pendant da chain ďinshi matar ta saka mata a wuya na montinè da agogonshi sai pin earing da matching bracelet ďin sarkan, cashmere scarf bak'i mai golden crystals ta ďaura mata akai kamar turban, ga front hair ďinta da ya fito ya kwanta lub lub sai ya k'ara mata kyau, wani murmushi ta saka da taga kanta a mirror, ba k'aramin kyau tayi ba , takalmin karen kelly heel bak'i ta saka, a hankali take takawa har ta fito daga ďakin ta sauk'a k'asa, sai da Aunty tace "Masha Allah" da ta ganta , duk da Batuul bak'a ce bata kai sauran y'an gidan haske ba amma ta fisu kyau, Baba ne yace "Mamana kinyi kyau" da murmushinta mai kyau tace "nagode Baa", break fast sukayi dukkansu sunsa kaya sunyi kyau, matar da tayi mata makeup ďince ta sauk'o ta mik'o mata clutch bag ďinta shima golden shima na karen sannan tayi musu sallama, k'arfe tara da rabi suka isa international conference center inda venue graduation ďin yake, tun daga waje manyan motoci ke a pake, k'arasawa sukayi ciki, decoration ďin wajen yayi kyau kalan graduation gown ďinsu ne purple and blue, sai da suka shiga ta saka graduation gown ďinta da hula, side ďin da aka tanadawa graduants ďin tabi, kujeranta ta nufa seat number twelve, Affan ne daga hagunta sai na Farida daga gefen Affan, tambaynshi tayi Farida  bata k'araso ba, bai bata ansa ba ,Affan ne ya dubeta bayan ta zauna, mitsitsika idonshi yayi sannan yace "sorry this is my best friend's seat, can you kindly move to the next seat", dariya tayi ta ďan dungure mishi kai tace "Allah ya shiryaka Affan, in best friend ďin taka tazo sai in tashi", dariya shima ya saka yace "Besty you look gorgeous, i mean i cant say how much beautiful you look, am gonna miss you", ya fara share hawayen k'arya, dariya ma ya bata tace mishi "Farida fa, she isnt here....."bata k'arasa maganan ba ta ciro wayanta kenan zata k'irata taji bugun zuciyanta ya k'aru, a zuciyanta tace "No no, not today, let me be happy its my day" sannan ta fara ambaton "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", tana cikin addu'a taga Farida tazo kusa da Affan ta zauna, da harara tabi Farida da ido, Affan ne ya kare Farida da hannunshi yacewa Batuul "wannan kallo haka ai sai ta ji tsoro, Hayati ya akayi kikayi latti, i was waiting for you here all alone", ajiyan zuciya Farida tayi tace "baza ku gane waye Yaa Abu ba, wai fa girlfriend ďinshi ce mukaje ďauka shine take b'ata mana lokaci tana ta wani abu kamar yarinya,ni shima nake tausayi ansa aurensu nan da three weeks, ya mayi ya bar mana gida mu samu mu huta", dariya Affan yasa yace mata "babe you are too much, lets concentrate on what we are here for", suka maida hankali kan speech ďin da VP ďinsu keyi, ita dai Batuul kawai tayi shiru ne amma bugun zuciyanta k'aruwa yayi dan har hawaye ya fara taruwa a idonta

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now