💖💝BATUUL 19💖💝

6.7K 356 0
                                    





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



    Ganin yana nufota ne tayi maza ra rik'e rigan cikinta, ray ban glass ďin dake fuskanshi ya cire , ido huďu sukayi da Batuul, kasa ďauke idonta tayi daga kallonshi shima hakan bai ďauke nashi ba, sai da ya iso har inda take sannan ya tsaya, idonta ta ďauke daga kallonshi shi kuma yaci gaba da kallon nata, a hankali ta sake rik'on da tayiwa riganta, ya buďe baki kenan zaiyi mata magana ta juya a guje ta bar wajen, ranshi ne yayi bala'in b'aci ya daka mata tsawa, " *Batuul*", ko juyowa batayi ba taci gaba da gudunta, sosai ranshi ya b'aci, ba sau ďaya ba yanxu tana mishi irin haka sai yana mata magana ta gudu, tunawa yayi da ranan da ya fara ganinta ranan idi, haka ya buďe baki kenan zai ce mata ta gyara gyalen kanta, gashinta na a waje tak'i ko da tsayawa jin mey zai ce mata ta gudu, ko ďazu ma haka tayi mishi ta gudu daga ďakin yana k'wala mata k'ira, inda tabi ya kafawa ido yana daga tsaye, ji yayi an dafashi ta baya, Massa ne ya zagayo gabanshi yace mishi "Yanxu amarya ta k'irani wai suna ciki tun ďazu, sun jiramu bamu zo shine suka shiga", juyowa yayi ya dubi Massan sannan yace "toh mu shiga", shi da tawagar sauran abokanshi da kana ganinsu kasan dagaske suke suja k'arasa ciki, fili ne babba zagaye da canopies sai kujeru daga ciki biyu aka kasa wajen, side ďin amarya da gefensu, k'awayenta da dangi, sun sha ankon atamfa maroon, sunyi kyau sosai kasancewarsu farare, ďayan side ďin dangin ango ne suma da ankonsu na irin kayan da Batuul ta saka, daga gefe side ďin amarya ne da ango anyi musu rumfan fulawa da kujeru biyu, mutanene cike a wajen wasu na zaune wasu na kai kawo, Kamal da Mansur ne daga tsakiya rik'e da mic suna ta rero wak'a, ganin ango da abokansa sun shigo ya sa mawak'an k'ara kaimin wak'arsu, k'anshin turaren wuta ke tashi ta ko wane angle,tuni wajen ya kaure da hayaniya, k'awayen amarya aka fara k'ira suyi rawa da danginta, sun shiga sun tattaka rawa sosai sannan aka k'ira Family ďin ango, Batuul na zaune ita da Farida duk ranta a b'ace, gaba ďaya bata so Aunty ta sata zuwa wajen nan ba, ta k'agara ayi abinda za ayi ita ta koma gida, k'iran y'an uwan angi ne ya sa Farida mik'ewa zata shiga wajen rawa tare da janyo hannun Batuul, warce hannunta tayi daga rik'on da Farida tayi mata tace "mey haka kike jana, mey zan tashi inyi miki", "rawa mana baki ji an k'iramu bane, ai ni komin rashin shirinmu da Yaa Abu sai nayi rawa, ba namu bama munyi bare na gida", ta faďa tana dariya, "A dawo lafiya", inji Batuul ta sunkuyar da kanta taci gaba da dannan wayanta, Farida ganin dagaske Batuul take ya sata juyawa ta shiga filin rawa, rawa sosai su Farida sukayi da sauran family, sai da suka gama lokacin aka k'ira ango da amarya su fito suyi rawa, mik'ewa sukayi a tare shi da Ajiddeh, sosai tayi kyau, bak'in lace ta saka da blue laffaya, anyi mata kéla yaskè(kitson gaba) da aka bi akayi mishi ado da gold sai ya k'ara mata kyau, ko ina a jikinta gold ne , har anklet sai da ta saka na gold da nose ring, hannayensu mak'ale cikin na juna suka tasi suka isa filin rawar, mutane ne suka shigo ana ta yi musu lik'i, abokan ango dollars, Euros suke zubawa amarya, sau ďaya Batuul ta ďago kanta ta kallesu ta mayar, wayanta ne taga yana ringing, Aunty ke k'iranta, jutawa tayi ta dubi inda Aunty ke zaune taga tana mata alama da tazo da hannu, tashi tayi ta isa inda Aunty ke zaune, sai da ta zauna a empty kujeran dake gefen Aunty sannan tace "Aunty gani", jakanta ta ďauko sannan ta ciro bandir ďin 1000 sabbi dal ta mik'awa Batuul, da ido Batuul tabi kuďin tana jira taji na meye na "Kije kiyiwa ango da amarya lik'i, ni bana son tashi saboda da Aabidĺ, Batuul gaba ďaya bata yi zaton abinda Aunty zata sata yi ba kenan, ranta ya b'aci amma ba tayi musu ba dan bata son b'atawa Aunty rai kamar ďazu, kuďin ta ansa sannan ta mik'e Kamar mai shirin yin kuka rai b'ace ta isa inda suke, y'an dubu dubun nan ta rik'a cirowa tana yiwa amarya lik'i dashi, wani mugun harara Ajiddeh tabi Batuul da, daga k'arshe ma barin wajen tayi ta koma daga gefe wajen danginta, Batuul bata sanma tana yi ba, kuďin da yake hannunta tabi da ido, ko rabi bata lik'a ba, juyawa tayi ta dubi Abutturab taga idonshi na kanta, sauri tayi ta ďauke nata idon, Aunty ta sake waigawa ta duba a inda take zaune taga tana kallon wajensu, babu daman ta bar wajen, kawai kuďin ta fara zara tana yiwa Abutturab lik'i da, ido ya kafa mata yana kallon yadda tayi kicin kicin da fuska tana b'ata rai, Massa ne ya hango Batuul tana yiwa Abutturab lik'i, zuwa yayi inda take ya fara mata ruwan dollars a kanta, gaba ďaya sauran abokan ango ma hankalinsu kan Batuul, lik'i suka dinga yi mata kamar itace amaryar, ba k'aramin haushi Ajiddeh taji ba, ji take kamar ta shak'e yarinyar nan ta huta, gaba ďaya bata sonta , hankalinta sam bai ďauki Batuul ba, wani irin b'ata fuska Abutturab ya rik'a yi ganin yadda abokansa ke yiwa Batuul lik'i bayan ga amaryar basu yi mata ba, niyya yayi yaje yace su dena wannan shirmen, A guje Batuul ta sake kuďin hannunta a jikin Abutturab ta fice daga filin dan ta tsorata sosai da yadda dukkansu ke mata lik'i ita da bama rawa tayi ba, wajen zamanta ta k'arasa ta zauna, tana zama Massa ya bita shima ya zauna a kujerar Farida dake gefen nata, wani irin murmushi yayi mata yace "Fatima ko", kai ta gyaďa mishi ba tare da ta ďago ta dubeshi ba, k'anshin turarenshi duk ya cikata har yana neman sa mata murya, juyawa tayi ta dubi inda Aunty take taga hankalinta baya ma wajensu, ita masu rawa take kallo, "masha Allah", yace sannan yace "ranan grads ďinku i wanted talking to you sai kuma ban samu chance ba, you know kin burgeni, ni ban tab'a sanin Su Baba nada yarinya babba haka ba sai ranan graduation ďin da naji sunanki, kin tab'a sanin Aunty ce ta yayemu ni da Aliyu,  ina zaki sani ai ba a haifeki bama lokacin", ďagowa tayi ta dubeshi , toh ita mey ruwanta da Aunty ta yayesu, ina ruwanta ma in a gidansu aka haifeshi shi da Aliyun, juyar da kanta zatayi taga idon Abutturab a kansu rai a b'ace, ďauke idonta tayi taci gaba da wasa da awarwaron hannunta, "Cutie, it seems your mind is totally not here, mayb you should share your contact with me, sai muyi magana anjima, nima ďin yanxu am busy", dariya ne ya kusan kufce mata na sunan da ya k'irata dashi wai cutie, da har zata bashi number ta na da sai kuma ta tuna ai zai iya tambayan Farida ma ta bashi, deciding tayi da ta bashi natan , ai ba lallai ne in ya k'ira ta ďauka ba, karanto mishi tayi numbers ďin ya rubuta a wayanshi, mik'ewa yayi tareda kai hannun zai shafi fuskanta rayi maza ta matsa da baya, idon Abutturab akansu duk abunda sukeyi yana kallonsu sai ma harara da yake binsu da, tashi yayi zai fita daga  filin ranshi b'ace, Massa ne ya hango shi zai fita yayi maza ya cewa Batuul "Aii cutie we will talk later", yayi maza yabi bayan Abutturab yaji lafiya  zai fita ana cikin event, daga waje ya tarar da shi wajen da sukayi parking motoci, zuwa yayi yacewa Abutturab"Ya ka fito ka bar amaryarka a ciki, ana ta event, wato halinka ko a ina sai ka nun.....", bai k'arasa ba ya katse shi da "Mustapha what is wrong with you, for Gods kaga abinda kuka dinga yi a wajen nan, duk kun wani juya kuna yiwa yarinya lik'i bayan amaryar ma baku yi mata wanda kukayiwa yarinyan nan ba, kuma da ta bar wajen ka wani bita a baya , wannan ai neman raini ne a wajen yara, mey zaka nema a wajen Batuul yarinya k'arama, k'annenmu nefa, y'ar Aunty ce inma baka sani ba toh ka sani, k'anwar kace", kasake Massa yayi yana kallonshi, wannan faďa da yake yi kuma na meye haka, ce mishi yayi "toh menene in k'anwata ce ko kuma y'ar Aunty ce, ai nan nema zanyi yadda nakeso ko akwai inda aka hanani nemanta, kuma right from day one na faďa muku ni k'aramar yarinya zan aura, manyan mata wannan sai ku, kuma Batuul is d right choice for me saboda abinda ya fara min tarbiya shi yayi mata tarbiya dan haka ana gama bikinka zan kai nawa maganan gaba sai dai in itace tace bata sona" ya faďa yana maida numfashi, wani irin kallo Abutturab ya bishi dashi ya rasa mey zai ce mishi, tsaki yaja ya koma cikin wajen Massa ya bishi a baya



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now