💖💝BATUUL 44💖💖

6.6K 358 1
                                    





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



         Juyawa Abuturrab yyi ya haura sama a fusace ya shige bedroom dinsa, tsaki yyi ganin hw untidy the room is, wae kuma mace ce ke rayuwa ciki, toilet ya nufa ya wanke baki ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, ya jima xaune kan darduma yana mamakin hali na Ajiddeh, hw wil she b insulting his family into his face kuma ya dinga tolerating hka, tsaki yyi a xuciyarsa yace na san maganin ki, mikewa yyi ya shiga toilet don yin wanka,    cikin kananun kaya ya shirya bayan ya fito, ya cire bedsheet din kan gadon, ya shimfida sabo, bae tsaya gyarawa ba yyi kwanciyarsa tare da lumshe ido, lkci daya ya bude ido ya mike xaune tuno Batuul da yyi, sauka yyi daga kan gadon ya fita daga dakin ya nufi wanda ya kai ta, tura kofar yyi ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadon dakin, ta jingina jikin gadon, kana ganin idonta kasan kuka ta gama, ya wani hade rae yace "Wato ni kike jira in xo in maki sllhn in maki wanka koh, are yhu okay?" A d'an tsawace ya kare maganan yana mata mugun kallo, mikewa tayi da sauri gabanta na faduwa ta fara waige waigen inda xata ga kofar toilet, taji yace "Over there" juyawa tayi tana kallon inda ya nuna mata snn ta karasa ta bude kofar ta shiga, vry neat toilet din me hade da bathroom, sae dae da gani kasan ba a amfani da shi, ba laifi yana da girma ssae, ta dde tsaye toilet din ganin bbu toothpaste bbu toothbrush, bbu sabulu da sponge, a hnkli ta juya a sanyaye ta tura kofan ta fito, dai dai lkcn da shima ya shigo dakin, kallo daya yyi mata ya dauke kai, sabon brush, da toothpaste ya ajiye mata gefen gado, da sabulai da shower gel, sae wani sponge me laushi, da brand new white towel duk lkci daya ya dire su snn ya juya ya fice, karasawa gadon tayi ta dauki wanda xata yi amfani da ta koma bayin, wanka tayi gaba daya bayan ta wanke baki, snn ta dauro alwala ta fito, ta dde xaune kan darduma hawaye na bin kuncinta tana rokon Allah ya yyi mata katanga tsakanin ta da Ajiddeh don har ga Allah tsoronta take ita dae, ko kadan bata ji haushin matsayin da Abuturrab ya bata a gidan ba gaban matar tasa na cewa ita cousin dinsa ce da ta xo karatu kawae, share hawayen idonta tayi tayi murmushi don ita ma ya saman mata saukin bala'in matar tasa, bude kofar dakin taji anyi ta d'aga kai da sauri tana kallonsa, fuska daure yace "ki sakko ki sama ma kanki abun kari" ganin yana tsaye har lkcn yasa ta Mike da sauri ta nufi kofar da dogon farin hijab din jikinta, juyawa yyi ta bi bayansa, a tare suka sauko downstairs sae dae duk a tsorace take, gabanta yyi mugun faduwa ganin Ajiddeh xaune har lkcn a falon idon nan nata duk ya kumbura alaman ba karamin kuka ta ci ba, ko kallon inda take bae yi ba ya nufi kitchen, Batuul kam kanta a kasa take bin bayansa kmr munafuka, Ajiddeh ta bi ta da wani mugun kallo cike da tsana, suna shiga kitchen din duk ya nuna mata food stuffs ba tare da ya kalleta ba yace "Sae kiyi duk abinda kike so," daga hka ya dauki mug ya hada Coffee don akwae ruwan xafi a E.kettle ya fice daga kitchen din, bin sa tayi da kallo a tsorace, kaddae tafiya xae yi ya bar ta daga ita sae Ajiddeh a falon ta xo ta risketa, tunanin hkn ya daga mata hnkli ssae, ta kasa motsi inda take, shi kam yana haurawa sama Ajiddeh ta bi sa da kallo hawaye na bin kuncinta, ita tasan tana son Aliyu tsakaninta da Allah ta rasa ynda xata yi ya xama sae abinda tace masa, ynxu duk kudin da ta kashe asirin nn bae yi tasiri kansa ba lallai da sake dole ta kira mummy ynxu ba da dde wa ba, kallon kofar kitchen din tayi xuciyarta na tafarfasa sae dae tana tsoron shiga ta riske Batuul don tasan Abuturrab xae iya yi mata komae ynda ransa ya baci, mikewa tayi rai bbu ddi ta haura sama tana tunanin mafita don ita kam wllh shegiyar baxata xauna mata a gida ba da sunan karatu ta dinga mata leken asiri, kofar dakinsa ta tura a hnkli ta shiga, kwance ta samesa idonsa lumshe, ta karasa kan gadon ta kwanta faffadan kirjinsa ta saki kukan kissa tace "Don ka ga ina son ka Aliyu shi yasa kke walakantani hka koh, ni bni na daura ma kai na sonka ba Allah ne ya daura min, kuma da xan iya da tuni na cire na huta...." Ta fashe da wani matsanancin kuka, d'ago kanta yyi yana kallon fuskarta da ya wanke da hawaye, ya sauke ajiyar xuciya ya rungume ta yace "Y xa ki dinga fadin bad things about my relative Ajiddeh, ni kuma ba hka nake ma naki ba, yhu are the cause of every fight btwn us, bakya daraja family na Jiddah," shiru tayi tana sauke ajiyar xuciya, a hnkli ya shiga shafa dogon gashin kanta dake ta kamshi, cikin sanyin murya yace "Yhu knw I love yhu babe, yhu are d cause of everything, Batuul will only b here for sometime, snn yarinyar bata da damuwa, nd of course she wil b of help to yhu ke da ba kya son aiki, idan kika sake mata xa ki ji ddin xama da ita, she's a Nyc gal" jin Ajiddeh bata ce komae ba yasa ya d'ago kanta yana kallonta, cikin shagwababbiyar murya tace "Toh shekara nawa ne karatun nata?" Yace "Ban sani ba babe, ni ban ma san me take karanta ba, dad dinta yace yana son ta xauna gun mu tayi karatunta kin ga baxan iya ce masa A'a ba, ni ma kuma burden aka daura min ynxu don dole wani abun na makaranta ni xan mata, don hka ba ke kadae abun nn ya shafa ba har ni babe" shagwabewa ta kuma yi ta shige jikinsa tace "Toh shine xaka nemi tijara ni gabanta babe, har kana....." Bae bari ta kai karshe ba ya hade bakinsa da nata, nn fa suka lula wata duniyar, ya shiga gwada ma Ajiddehn ynda yyi kewarta ita ma hka duk ta rikita shi.   Karfe sha biyu saura ta farka daga bacci, ta xame jikinta a hnkli daga nasa don bata son ta tada shi ta nufi bathroom, wanka tayi ta fito ta shirya cikin wasu sheggun kaya irin wanda ta saba sa wa, ta fito dakin ta sauko falo, pizzan dake ajiye har lkcn ta nufa.




💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now