💖💝BATUUL 38💖💝

6.4K 328 1
                                    





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



        Jiki a sanyaye ta mik'e ta fito daga ďakin ta sakko downstairs, ganinshi zaune a palo yasa ta jin daďin kimonon  da ta ďaura kan kayan dake jikinta, ďauke kanta tayi kamar bata ganshi ba tayi hanyan kitchen, da ido ya bita har ta shige tukunna ya ďauke idonshi daga wajen, tana shiga tace "Na'am Aunty, gani", tray da aka cika da snacks iri iri sai drinks da ruwa Aunty ta nuna mata tace mata "ďauki ki kaiwa Abuu", da sauri ta ďago zuciyanta sai faďuwa yake tana kallon Aunty dake ta aikinta tace "Aunty ni kuma", ba tareda da ta juyo ta kalleta ba tace "ehhh ďauki ki kai mishi tun ďazu yake zaune ban sani ba kuma babu wanda ya faďa min", zuciyanta duk babu daďi har  idonta ya fara hawaye ta matsa gaban Island ďin ta kinkimi trayn tayi waje, tunda ta fito yake kallonta har ta iso palon, ďan nesa dashi ta ajiye mishi trayn fuskarta daure ta juya tayi tafiyarta, murmushi yyi ya ci gaba da kallon tv da yake, kitchen ďin ta koma ta tsaya bata cewa kowa komai ba ta hau kan deep freezer ta zauna, juyowa Aunty tayi zata cewa Janet ta mik'o mata abu a Fridge taga Batuul zaune kan Fridge, kallonta Aunty ta tsaya yi da mamaki tace "Batuul meye hakan, mey kika dawo yi kika barshi shi kaďai a palon", kanta ta girgiza tana kallon Aunty tace "Aunty toh ai abinci zai ci kuma ma nifa.....", bata k'arasa ba ganin kallon da Aunty keyi mata ta sauko tace "kiyi hak'uri zanje", ta juya jiki a sanyaye ta fita daga kitchen din, da k'yar take ďaga k'afanta har ta isa palon, yana nan inda ta barshi yana kallonn Discovery channel, sau ďaya ya ďaga kai ya kalleta ta sadda kai k'asa tana ta fidgeting yatsunta, ya ďauke kai yaci gaba da kallonshi har ta k'araso ta zauna can nesa dashi, lokaci lokaci yake satan kallonta ita ma hka, sai da programm ďin ya k'are tukunna ya dubeta, ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta, sauk'a yayi daga kujeran ya janyo trayn yana kallonta murya can kasa yace "Baki faďa musu sak'ona ba knn har ynxu koh?" Kin cewa komae tayi kuma bata d'ago kanta ba, kallonta ya tsaya yi, ta dan sata kallonsa jin shirun yyi yawa, suka hada ido ta dauke kai da sauri, kallon hanyar kitchen yyi kafin yyi kwafa ya dauki glass cup ya bude lemon kwalin dake kan trayn da ta ajiye masa ya tsiyaya ya mayar ya rufe, ba tare da ya kalleta ba yana girgixa kai cikin sanyayyan muryarsa yace "Ni tausayin rayuwar ki da nake yasa ki ka ga ina maki kashedin kar ki yrda su makala min ke, yhu are too young to start facing challenges or rather I shud put it as problem, ni ina da matata kuma muna son junan mu like! har kika kuskura aka yi auren nn u will only end up shattering ur life, it's still not late for yhu...." Bata Bari ya kai karshe ba ta xamo kasa da sauri hawaye na bin kuncinta xuciyarta na tafasa tace "Kai wae me xae hanaka yin magana sae ni? Naga kai ma xaka iya gaya masu baka son auren ae koh?" Yyi wani murmushin da ta kasa fassara nufin shi yace "Ni baxan iya yi ma iyayena musu ba, ina ganin darajan su shi yasa kika ga har ynxu ban musa masu ba" wani mugun kallo ta shiga yi masa har lkcn tana hawaye ssae tace "Kai ne kasan darajar iyaye ni ban sani ba koh, toh kmr ynda baxa ka iya masu musu ba nima baxan iya ba, sae dae idan an makala maka ni ku kashe ni kai da matarka" tana kai wa nn ta mike tana kuka ssae ta haura sama da gudu, bin ta da kallo yyi yana murmushi, kafin ya fara shan drink din hannunsa, cake kawae ya dan ci ya mike yace ma Janet da ta fito daga kitchen ta ce ma Anty xae koma, fitowa Anty tayi bayan Janet ta bata sakon shi, tayi Mamakin rashin ganin Batuul a falon sae dae bata nuna ba tace "Har xaka tafi Abuturrab" Yace "Eh Anty, it's almost time for sallat ne" tace "Toh shknn, Allah ya tsare" fita yyi daga falon, ita kuma ta nufi sama don xuwa jin dalilin kin jin maganarta da Batuul tayi rai a bace, dakinta ta sameta kwance tana kuka har da sheshsheka, Anty ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta tace "Meye hkn Batuul?" Mikewa xaune tayi da sauri ta kuma fashewa da kuka tace "Don Allah Anty ku rufa min asiri a fasa auren nn wllh bana son ya Abuu shi ma baya sona ..." Harara Anty ta galla mata tace "Wnn kuma sae ki jira idan babanku ya dawo ki sanar da shi" tana kai wa nn ga juya ta fice daga dakin.



   Aunty na shigowa daki taji wayanta na ringing, kamin tayi picking taga har ya katse, ďauka tayi ta duba taga wa ya k'ira, missed calls biyu ta gani duk Ammah ce ta k'ira, zama tayi daga bakin gado zata k'ira kenan wayan ya fara ringing, Ammah ďince ke k'ira, ďagawa tayi tare da yi mata sallama, bayan sun gaisa Ammah ke tambayan Aunty "Maryam ya shirye shirye", murmushi Aunty tace "Alhamdulillah Ammah", ita har yanxu mamaki take na zata aurar da Batuul nan da y'an kwanaki, Ammah ce ta katse mata tunani da cewa "dama kayan Batuul ne nakeso a tambayar min ita inda akwai abunda take buk'ata dan Aliyu ya tambayeta tace ita bata son komai, toh ni ba yarda nayi dashi ba shine nakeso a bincika min sannan gyaran jiki zan turo a kawota gida sai ayi mata duk abinda ya kamata", shiru Aunty tayi har sai da Ammah ta kai aya tukunna tayi ajiyan zuciya tace "Toh Ammah zan tambaya miki ita, sai dai gyaran kamar zai fi tayi a gida nake gani ba sai taje can ďinba ai hidima zaiyi yawa, har nayi magana mai gyara gobe zata zo daga Ndjamena", cewa Amma tayi "toh shikenan hakanma yayi", da haka suka gama wayan, zaman tunani Aunty ta yi dan ita bata da wani shiri ma da zatayi na bikin, ko y'an uwanta ma bata faďa musu, waya ta sake ďauka tana k'iransu ďaya bayan ďaya duk ta sanar dasu auren Batuul, sai mamaki sukeyi ganin abun yazo da wuri.



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now