💖💝BATUUL 37💖💝

6.2K 328 1
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



        Daga gaban gadon Abdallah ya tsaya a tunaninsa Abuturrab xae basu waje sae ya ga otherwise, don kujera gogan ya ja  yyi xaman sa yana facing dinsu, Abubakar na ganin hka ya xauna gefenta ya shiga mata magana murya can k'asa da damuwa, Batuul ta k'asa ďago kai ta kalleshi, sake matsowa yayi kusa da ita yace "Habibty tok to me mana, mey doctor yace na damunki", a hankali kamar bata son aji mey take faďi tana wasa da fingers dinta tace "nima ban sani ba, but i think doctor ya faďawa su Aunty, ni ban sani ba", ta k'arasa maganan tare da ďago kanta, ido hudu suka yi da Abutturab dake kallonta ko kiftawa bae yi, ya watsa mata wani irin kallon da ya sata saurin sadda kai, haka Abdallah yaci gaba da yi mata tambayoyi da yi mata sannu da damuwa, bata cewa komai daga "um", sai "um um", banging k'ofa suka ji suka juya, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ganin shi ne ya fita, juyowa Abdallah yayi yace "Habibty who is he? your uncle", girgiza kai tayi tace mishi "brother ďin Farida ne", juyawa yayi ya sake kallon k'ofan sannan ya mik'e tsaye yace " Shknn Habibty i will b going, Mum na mota tana jirana get well soon, i will b back tomorrow in'sha Allah", yayi mata wani lallausan murmushi da itama maida mishi, daga haka ya fita yana waigen ta, a bakin k'ofa ya tarar da Abutturab na waya, tsayawa yayi ya gama wayan su yi sallama, ganin ya kusa minti biyar tsaye kuma ya ki k'are wayar yasa ya ďaga mishi hannu ya wuce, Abuturrab  na ganin ya wuce ya katse wayan ya tura k'ofar ďakin, hawayen dake idonta take gogewa da tissue, tsayawa yayi yana kallonta daga bakin k'ofa, snn ya shigi tare da tura k'ofan ya rufr, jin k'aran k'ofan ne ya sata ďagowa da sauri, duk da rashin k'arfin jikinta hkn bai hanata mik'ewa cikin sauri tayi hanyan toilet ba, da gudu taje zata buďe k'ofan, taji ya fixgota, tsayawa tayi a wajen ta kasa motsi gabanta na faduwa, ya juyo da ita yana kallon yadda ta rintse ido hawaye na zubowa, fuskanta ya tsura ma ido da ďan k'aramin lips ďinta da ya koma ja, hannunshi ya ďaura kan kafaďunta ya matso da ita gabanshi yana kallonta da kyau yace "waye shi?" Kin cewa komae tayi har lkcn idonta a runtse, ya daga kafada yace "As if i care, kina jina dama Aunty na shigowa ki ce mata kin warke a maidaki gida kuma ke kina da wanda kike so, nasan wannan da yazo ya saki gaba yana miki surutu kmr radio saurayinki ne, toh dama kice musu shi kikeso kuma keh shi zaki aura, is dat clear?", sai da taji yayi shiru har lokacin tana hawaye ta buďe ido a hnkli tace "kai mey zai hana ka faďa musu, kaima ai kasan su kuma zaka iya samun su ka faďa musu kace kana da matarka basai an sani aurenka ba dan ni bbu abinda xanyi da mai mata, sabon jini dama ai sai sabo, mey ma zanyi da......", ganin yadda ya zuba mata lumsassun idanunshi yasa ta maida sauran  maganan tana gogewa hawayen dake fuskanta, bin fuskanta yayi da kallo har idonshi ya sauk'a kan k'irjinta dake ta heaving, dariya abun ya bashi amma ya dake, yasan duk maganan da tayi a tsorace take, saketa yayi yana mata wani irin kallo yace "Really?, Fine then, zamu haďu ne tun da bakiji abinda na faďa miki ba, ki yadda ayi auren, xagi gane mai mata kuma tsohon jini kika aura yarinya", yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ďakin, a nan wajen ta tsuguna ta sa kuka kamar wacce aka aikowa lbrn mutuwa, a nan Aunty ta shigo ta sameta, da gudu Aunty tazo ta ďagata tana tambayanta mey ya sameta, kasa magana tayi sai kukan da take tayi, Anty ta maida ta kan gado ta rungumeta hankali tashe tana lallashin  ta, a nan tayi bacci jikin Aunty.


    11 o'clock bayan doctor ya dubata yayi discharging ďinsu akan zai na zuwa har gida yayi mata alluranta da suka rage sannan yace a guji duk wani abu da zai rik'a b'ata mata rai kuma kar a rik'a faďa mata maganan da bata expecting har ya rik'a shocking ďinta tana zama unconscious, Baba ne yayi magana yace zasu kiyaye, da haka suka yiwa doctor sallama, suna komawa gida tace ita baza taje ďakinta ba a ďakin Aunty zata zauna, wanka tayi bayan ta shiga ďakin sannan ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai k'arfe biyu, tayi alwala ta tada Sallah, tana idarwa Aunty ta shigo rik'e da tray a hannunta, ajiyewa tayi ta zubawa Batuul abinci sannan tace mata ta sauk'o taci, da kyar taci kaďan tace ta koshi, 


💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now