💖💝BATUUL 79💖💝

7.7K 428 6
                                    




Jin muryar Ammah ya d'aga kai yana kallon Ajiddeh, a fusace Ammah tace "Kana ji na ka min shiru Aliyu" yyi kasa da kai yace "A'a Ammah ina yini?" cike da fada tace "Rike gaisuwar ka, maxa tun muna mu biyu gobe ka taho min da Batuul gida, ai tun ba yau ba nasan kai shashasha ne, uwar ka cikin ya tsare maka kake son a cire" kasa cewa komai yayi, Ammah tayi ta bambami ya bari tayi mai isarta sannan a hankali yace "Ammah tana wahala ne, ki tambayi farida in ta iso gobe" Ammah tace "Ya baxa tayi wahala ba kana xaune da makira a gida a matsayin mata sun sa min ita a gaba, ina me tabbatar maka xaka ga the other side of me idan abu ya samu Bitti, maxa ku bar asibitin nan gobe ku biyo 1st flight ka dawo min da ita Nigeria" Ammah na kai wa nan ta katse wayar, ya daga kai yana kallon Ajiddeh dake jingine jikin bango duk jikinta a sanyaye, ajiye wayar yayi yace "Why did you call her?" Bata ce komai ba ta juya ta fice daga ward din, juyawa yayi a hankali yana kallon Batuul dake bacci, dawowa yayi kusa da ita ya daura hannunsa a hankali kan fuskarta, sosai ta rame daga jiyan xuwa yau, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace "Get well soon wife" mikewa yayi jiki ba kwari ya koma gun likitocin don dakatar da su, A asibiti suka kwana ranan don gani yake suna komawa gida ciwon xai tashi, sai dai throughout daren ko farkawa Batuul bata yi ba, a spare bed din dake dakin Ajiddeh ta kwanta, sai dai kwata kwata ta kasa bacci ta rasa me ke damunta, Abuturrab dake xaune kan darduma a dakin yana kula da yanda take ta juye juye sai dai bai ce mata komai ba, da asuba suka bar asibitin don bai son suyi missing 1st flight kamar yanda Ammah ta bukata duk da he is not sure xa su samu, a mota yana driving ya d'an kalli Ajiddeh yace "We will be leaving for Nigeria, xan maida Batuul gida, you take care...." Bai karasa ba ta katse shi tace "Nima xan je" kallon ta ya kuma yi sai dai bai ce komai ba ya ci gaba da driving dinsa yana yi yana kallon Batuul da har ta koma bacci a bayan motar. Ba tare da bata lokaci ba duk suka shirya, Batuul dama shi ya taimaka mata tayi wanka ta shirya don yaga alamar in suka biye ta nata bacci kawai xata yi tayi, Biyar saura suka isa airport yayi masu booking, biyar da rabi suka yi set off for Nigeria, duk motsin da Batuul dake rungume jikinsa xata yi idonsa na kai don waje daya suka xauna har lokacin kuma bacci take, lkci lkci kuma ya kan juya ya kalli Ajiddeh dake gaba ta saka earpiece, sai a sannan ya fara tunanin sudden change dinta is it for real, maganganun da Ammah ta fadi masa jiya suka fado masa, wai sun sa Batuul a gaba, ya sauke ajiyar xuciya don shi bai yrda da wannan belief din ba, a hankali Batuul ta bude ido tana kallonsa, ganin yanda ta bata fuska gabansa ya fadi a hankali yace "What?" Ta rike hannunsa tace "Ya Abu cikin xai fara" hankalinsa ne ya tashi ya daura hannunsa a cikin yace "No, no baxai fara ba idan Allah ya yarda" runtse ido tayi jin kamar ana murda mata cikin ta sakar masa kuka tace "Wllh ya Abu ya fara" ya rungume ta sosai yace "Noo wife baxai fara ba in'sha Allah, ko yunwa dai kike ji..." Ta fashe da wani kukan tace "Wayyo ya Abu cikin ya fara min" Kallon su kawae Ajiddeh ke yi, can kuma ta maida kanta kan wayarta, ganin kuka sosai Batuul ke yi jikinsa tana rike da cikinta ya kalli Ajiddeh suka hada ido, dauke kai tayi, ya sake Batuul ya mike ya tafi gunta cike da damuwa yace "Babe kin ji wai cikin ya fara, how are we going to do it, gashi ba muyi rabin journey ba har yanxu fa" ba tare da ta kallesa ba tace "Ba sai kayi ta tofa mata addu'a ba" yace "Yea haka ne kuma" juyawa yayi da sauri ya koma gun Batuul da ta hade kanta da gwiwa har ta hada xufa don axaba ita kanta baxa ta ce ga yanda cikin yake mata ba, ya xauna ya dagota ya kwantar da ita jikinsa yace "Sorry wife xai daina in'sha Allah" a hankali ya dinga tofa mata addu'a tana jikinsa, sun kusa awa biyu a haka har dai yaji ta daina kukan da take a hankali, ya leka fuskarta ya ga bacci tayi, ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido ya manna mata kiss a forehead dinta, yana bude ido suka yi ido hudu da Ajiddeh dake kallon su, dauke kai tayi da sauri, ya ji wani iri shima ya dauke nasa kan. Shidda na yamma jirginsu yayi land a Nnamdi Azikwe Airport, ya kunna wayarsa ya shiga kiran layin Sadeeq, yana d'agawa yace "Hello Bro, ka taho kayi picking dinmu muna airport" daga haka ya katse wayar, ya kalli Batuul dake kwance jikinsa idonta lumshe duk da ba bacci take ba and he can see how happy she is to be home, ko bata fadi ba, Ajiddeh kam nesa da su ta xauna, bude ido Batuul tayi da sauri, yace "What?" Kallon matar dake xaune daga gefensu tana cin popcorn tayi ta bata fuska tace "Bana son kamshin xai sa ni amai" mikewa yyi da sauri ya d'agata suka bar wajen, Ajiddeh ta bi su da kallo, wani gun ya koma suka xauna, boye fuskarta tayi da sauri a kirjinsa yace "What again?" Kamar xata yi kuka tace "Bana son kamshin turaren mutumin nan" juyawa yayi ya kalli Mutumin dake xaune gefensu, ya mike ya dagota suka kuma barin wajen suka koma wani gun suka xauna, plantain chips taga wani yaro na ci ta kallesa da sauri tace "Ya Abu xan ci" yace "Me za ki ci?" Ta turo baki ta nuna masa chips din, kallon ta yayi, sai kuma ya mike ya nufi inda yaron da Mamarsa ke xaune yayi masu sallama yace "Don Allah a ina ku ka siya chips din nan Anty" matar tace "Ai kam ba nan muka siya ba" yace "Toh nagode" juyawa yayi ya koma gun Batuul ya xauna yace "Ki bari idan xa mu gida in siya maki a hanya suma ba nan suka siya ba" kamar xata yi kuka tace "Noo Ya Abu yanxu nake so wllh, kila anjima baxan iya ci ba xai fita raina" murmushi yayi ya jawota jikinsa yana shafa cikinta a hankali yace "Shi babyna yake son ci yanxu koh?" Bata fuska tayi, yayi dariya ya manna mata kiss ya cheeks dinta yace "Don't worry, it's nothing don babynmu yasa mu roko a airport" mikewa yyi ya koma gun masu chips, yana d'an Shafa kai yace "Anty ko xaku d'an san mana chips din k'adan, matata ce wai shi ke ranta taki bari mu fita mu siya" dariya matar tayi tace "Allah sarki duk mun cinye a jirgi amma bari in dibar mata na Kamal" yayi murmushi yace "Toh mun gode" ta karbi na hannun yaronta tace "Kamal idan mun fita xan siya maka wani ka ji" ya gyada mata kai, ta d'an dibar masa k'adan ta mika ma Abuturrab sauran na ledan ya karba yana murmushi ya shafa kan yaron yace "Toh mun gode kwarai Anty da kamal" tayi dariya tace "Babu komai, Allah dai ya raba lafiya" murmushi yayi ya juya yace "Toh Ameen" duk wannan abinda suke Ajiddeh na kallon su kuma tana ji, ya koma gun Batuul ya d'ago kanta yace "Oya ga chips Maman twins" hararansa tayi ta fada kansa ta shagwabe murya tace "Ni Allah bana so" dariya yayi ya dauki chip daya yace "toh na daina, bude bakin" ba musu ta bude ya d'an gutsura k'adan ya saka mata sauran a baki. Mikewa Ajiddeh tayi ta fice daga waiting room din ba tare da ya lura da hakan ba, haka yayi ta ba Batuul chips din har tace ya isheta, wayarsa ya shiga ring ya fiddo ya ga sadiq ne, mikewa yayi ya dagota yace "Sadeeq na jiranmu" sai a sannan ya kalli inda Ajiddeh take ya ga ba ta, waige waigen inda xai ganta ya fara yi amma bai ganta ba, yana rike da Batuul suka fita.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now