💖💝BATUUL 46💖💝

6.7K 359 2
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



     A hargitse ta tura k'ofan ďakin, yana kwance kan gado ya lumshe  ido kamar ba shine ya shigo yanxun ba, dai dai kanshi tazo ta tsaya tana huci, ranta b'ace har wani gumi takeyi ta shiga yi masa magana, "Aliyu nifa bazan yadda da wannan abinda kuka tsira ba, wlhy ni bazan yadda da zamanta ba a cikin gidan nan, inma kai baza ka iya faďawa iyayenta baka son zamanta gidanka ba sai ka kama mata hostel ďin da kanka kawae, amma ba dai tayi ta zama min a gida ba dan dama nasan munafirci ya kawota", sai da yaji tayi shiru tukunna ya buďe lumsassun idanunshi dake rikitata yace "tunda gidanki ne sai ki koreta", ido ta wara tana kallonshi hawaye na bin kuncinta, cikin rashin damuwa da hawayen nata yaci gaba da cewa "tsabar rashin hankali da rashin sanin ciwon kai shine ki kaje kika tsareta a kitchen kina gaya mata maganganu koh, toh duk kika yrda ta raina ki baxa ki ji da dadi ba kuma bbu ruwana baxan kuma ce mata don me ba ", hankalinta ne ya k'ara tashi wai yau ita Abu ke k'ira mara hankali akan wata can y'ar iskar, wlhy Allah sai tasan yadda tayi da Batuul, sai ta wulak'anta ta fiyeda tunaninta, k'wafa tayi ta juya a fusace ta banko mishi k'ofar ďakin a xuciyarta tana cewa xaka rashin hankali kuwa, tabe baki yyi ya sake lumshe idanunshi ya gyara kwanciya yana shak'ar k'amshin Batuul da ya mannne mishi a kaya da yayi hugging ďinta.



     Tana fita ďakin tayi hanyan ďakin Batuul a fusace kamar wacce zata tashi sama, kai tsaye ta tura k'ofar ďakin da Batuul ke ciki, tana zaune kan gadon a takure ta haďe kanta da guiwa, bata ďago kanta taga ko waye ba dan tasan shine ya dawo, ji tayi ance "tashi ki fita dan ubanki tunda ba ubanki  ya gina min gidan ba", a tsorace Batuul ta ďago tana kallonta da mamaki shimfiďe a fuskanta, gani tayi tana k'ara shigowa ďakin, da sauri Batuul ta mik'e tana kallonta, inda akwatinan ta ke ajiye Ajiddeh ta nufa ta ďauka tana watsarwa, a tsorace Batuul ta tsaya tana kallonta, hawaye ya taru a idonta, ita wane irin masifa ne wannan yake tunkarota ko kwana daya bata yi ba, hawayen dake k'ok'arin zubo mata ta maida ta sauk'o daga kan gadon tana ganin yadda Ajiddeh ke watsar da kayan tayi hanyan waje, wai wannan ma fa dan bata san matarsa bace ita, hanyan waje tayi zata fita daga ďakin, hannu Ajiddeh tasa ta rik'ota tana cewa "ga y'ar iska na miki magana koh, toh dan ubanki kisan inda dare yayi miki dan gidana ba gidan ajiye y'an iska karuwai bane", ido Batuul ta rintse jin abunda Ajiddeh ta kirata dashi, zata iya rantsewa gaba ďaya rayuwanta bata tab'a jin an ambaci wannan word ďin a gidansu ba wai sai yau gashi ita ake k'ira da word ďin, hawayen dake idontane ya shiga gangarowa, hannunta tasa ta goge fuskanta, tasa hannu ta murďa k'ofan zata fita, wani irin force taji Ajiddeh ta tunkuďata dashi , ido ta rintse tana k'iran sunan Allah lkci daya ta fasa ihu tana jiran jinta a k'asa, amma ta ji akasin hka don jikin mutum ta faďa baya tayi zata faďi yayi hanzarin rikota ya rungumeta, shigewa jikinshi tayi tana boye fuskanta a kirjinsa, sai a lkcn ta fashe da kuka   jikinta na rawa tsabar tsorata da tayi, kuka sosai ta shigayi tana cewa "Yaa Abu dan Allah ka maidani gida, dan Allah inaso inga  Aunty, hannu yasa ya daďa haďe jikinsu dan yasan tsorata tayi ba da wasa ba, neman kukan da takeyi tayi ta rasa jin kanta faffaďan k'irjinshi, sai da yaga ta fara nutsuwa sannan ya saketa yana kallon fuskanta da hawaye ya gama wankewa, saketa yayi ya matsar da ita gefe ya zaunar da ita kan kujeran dake tsakanin ďakunan biyu, mutuwar tsaye Ajiddeh tayi ganin Aliyu ya kare Batuul, sam ba haka taso ba, taso koda Batuul bata mutu ba ta nakasa ta in yaso iyayenta suzo su ďauketa amma wannan jarababben ya taimakota, juyowa yayi ya shigo ďakin yanayinshi da ta gani ne ya sata tsorata, baice mata komai ba yasa hannu ya rik'o hannayenta tana binshi a baya kamar wata doluwa yayi ďakinshi da ita, kallonsu Batuul tayi hawaye cike idonta, ita dama tasan abin tausayi zata zama a gidan nan, duk abin nan da matarsa tayi baice mata komai ba sai ma rikota da yayi su tafi abunsu, kuka sosai ta kifa kanta kan cinyarta tanayi, sai sunan Aunty take k'ira da Baba, yana shiga ďakinshi da ita ya sake mata hannu, magana ta fara mishi cike da masifa "wllh Aliyu yarinyar nan ta barmin gidana dan....."  bai bari ta k'arasa maganan ba ya wanka mata mari lafiyayyu guda biyu, a gigice ta ďago kanta da idonta da ya rine yayi ja tana kallonshi, wani shegen murmushi ta saki tana hawaye tace "koh baka dakeni ba nasan karuwarka ce ko daga yadda ka rik'eta a jikinka, ni za a yiwa bariki a wani ce karatu tazo yi, munafiki kawai azzalumi, Kuma wlhy kaji na rantse sai na illatata, mugu kawai.....", wani irin fixga da yayi mata yasa ta kasa k'arasa  maganan da takeyi, idonshi ya sake yin jaa, yana kallonta yace "ai ke gidan na ubankine koh, dan bakida hankali kashe y'ar mutane zakiyi xa ki hankaďata hka, kinsan zaki iya barin gidan nan ita ta zauna, jahila kawai wacce bata aiki da hankalinta, kika sake min shirmen nan a gidana sai na b'ata miki yadda baki zato ba, mahaukaciya jahila", yana kai wa nn ya jefar da ita ya fice daga ďakin, inda ya barta kan kujeran nan ya dawo ya sameta sai kuka takeyi, ce mata yayi "kukan mey kike ma mutane ke kuma har ynxu", bata ďago ta dubeshi sai kukan da ta ci gaba dayi, cikin tsawa ranshi b'ace yace "ba magana nake yi miki ba", rinannun idanunta ta ďago ta kalleshi cikin sanyi hawaye nata zuba tace "Yaa Abu dan girman Allah da Annabinshi ka mayar dani wajen Aunty", hararanta yayi ya kamo hannunta, komawa tayi baya da sauri ta janye hannunta, tsayawa yayi yana kallonta yace "you thought all i was telling is lie huh, gashi nan kin fara gani tun ba aje ko ina ba, its just your first day and you have already faced soo much, sai da na faďa miki babu ruwanki da ita, mesa kika nemi magananta", haushi ne ya cikata ta tsananta kukanta tabi ta gefenshi zata shige ďakin yayi saurin rik'ota, wayantane taji yana ringing, fixge hannunta tayi tayi ďakin, bayanta yabi a hanzarce, hannu yasa ya rigata ďaukan wayan yana kallon mai k'iran, Affan ya gani rubuce in bold da hrt emoji daga gaban, kin bata yayi har sai da wayan ta katse, batare da ya kalleta ba ya jefa wayan kan gado, tsayawa tayi tana kallonshi , Juyawa yayi yana k'arewa ďakin kallo yadda kayanta ke zube a k'asa, ce mata yayi "da kika zauna kina yiwa mutane kuka waye zai tattare miki kayan da aka zubar garin neman faďanki, kinsan baki da k'arfi kika nemi tsokananta", bata ce mishi komai ba ta nemi waje ta zauna daga bakin gadon tare da janyo wayarta, dubawa tayi taga wa ya k'irata, ganin Affan ne ya sata ajiyan Zuciya, cikin kakkausar murya yace mata "ba magana nake yi miki ba, waye zai tattara miki kayan", zumb'uro bakinta tayi ta juya tana gyara zamanta kan gadon tace "Ai ba ni na zubar ba, suna zamansu ta shigo ta watsar, a k'irata ta gyara mana", da mamaki ya ke kallon yadda take mishi magana, matsowa yayi gaban gadon, da sauri ta shige cikin bargon tana cewa "nikam in ka tab'ani zan faďawa Ammah", ce mata yayi "tashi ki tattare kayanki", ba musu ta yaye bargon ta taso ta shiga kwashe kayan, juyawa yayi zai fita daga ďakin, har yaje bakin k'ofa ya juyo yace "kin nemi abinda zaki cin ko kuma baki gama jan maganan ba", ganin batace mishi komai ba ya fita daga ďakin ya barta anan



       Tana zaune ďakin har k'arfe 8 ďin dare, ga yunwa da ya addabeta, tsoron fita takeyi dan batason ko sake kallon Ajiddeh tayi, ta rasa mey zatayi kuďin wayarta ma ya k'are da ta k'ira ko su Aunty taji daďi, Affan ďinma da ya k'ira ďazu yaki k'ira har yanxu, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala ta tada sallah isha, sai da ta idar ta gama addu'anta tasha kuka ta tashi ta hau gado ta kwanta bayan ta kashe wutan, ta gwammace ta kwanta da yunwa da ta fito su haďu da Ajiddeh, jin an murďa k'ofan ďakin yasa ta k'ara tsorata, a hankali ta sauk'o daga kan gadon zata shige toilet taga haske ya gauraye duka ďakin, tsayawa tayi a tsakiyan ďakin ta kasa motsi, k'arasowa yayi cikin ďakin ya ajiye mata daya ledan dake hannunshi yace "in kin gama tsayuwan naki ga abinci ki ďauka kici, you get ready gobe by 11 zan kaiki school and mind you kina rufe k'ofar ďakinki da makulli", wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin shine, bata juyo ba har ya gama maganan da zaiyi sai ji tayi an juyo da ita, "kina jina ina magana kika min shiru, na fara wasa da ke koh", a hankali tace "Ai naji", saketa yayi ya juya ya fita daga ďakin tare da kashe mata wuta.    Dakin Ajiddeh ya nufa rike da wani ledan ya murda kofar ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadonta idon nn nata ya kumbura tsabar kuka, ya ajiye ledan hannunsa tare da sauke ajiyar xuciya ya nufeta, tana ganin hka ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin rikota tare da hade ta da jikinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa tace " let me be Aliyu, ka kyaleni, 1st thing tomorrow morning am leaving yhur goddam house, with or without my divorce prove, bna auren kuma, ae ba kai kadai bne namiji a duniya, sae ka xauna da 'yar uwar taka....." Ya runtse ido yace "Stop this Jiddah, yhu pushed me into behaving the way I did, meyasa baki saurarata ne wae, na gaya maki Batuul is only here for sometime, karatu ta xo yi tana gamawa xata koma Nigeria, I love yhu Jiddah bana son duk abinda xae bata maki rai, had it been we are not this close da iyayen Batuul da baxan yrda da xaman ta gu na ba coz it's also a burden to me, plss nd plss Ajiddeh kiyi hkuri ki bar ta tayi karatun ta, her being here is nt for ever, if yhu love me do me this one favour pls babe," tsuke fuska tayi ta kauda kai, ya marairaice yace "Plss babe!" Kuka ta fashe da tace "Shine xaka mareni Aliyu" ya kuma rungumeta yace "Ohh! Am srry babe sharrin shaidan ne plss, idan kuma baki hakura ba ki rama" shiru tayi bata ce komae ba, kissing wuyanta ya shiga yi a hnkli yace "Say something mana babe" lumshe ido tayi don kiss din Aliyu na rikitata, cikin sarkewar murya tace "Naji" bae daina abinda yake mata ba yace "kin amince ta xauna gidan ki har ta gama karatun?" Runtse ido tayi tace "Yeaa!" Yace "Promise!" Da kyar tace "I do love" Kiss din bakinta ya shiga yi passionately tana mayar masa da martani, kan kace me sae ga su kan gado.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now