💖💝 BATUUL 99 💖💝

10.8K 508 40
                                    

Dedicated to KHALEESAT HAYDAR


Kai tsaye Aunty Kulthum closet d'inta ta nufa ta bud'e tana cewa "Ajiddeh ki tashi Allah maji rokon bayinsa ya amsa mana addu'armu, Allah gafarur rahim ya dubi niyyarki ta tuba kuma yaji kukanku, maza tashi ki shiryaki baqinki na guest parlour suna jiranki", kamar ba da ita akayi zancen ba ko juyowa batayi ba saima rintse ido da tayi tana maida k'afafunta k'ark'ashin duvet, Aunty Kulthum tafi kowa sanin matsalarta mesa zatazo ta dameta da surutun tayi baqo, ita ba kowa tayi da yaxo wajenta ba, koma wacece saidai ta tafi dan batajin tanada kuzarin da zai iya mik'ar da ita daga wannan kwanciyar, ita kanta ma ciwo yake mata, juyowa Aunty Kulthum tayi bayan ta ciro wani lace cikin closet d'in tace "Kehhh ashe haka Aliyun nake had'add'e, dole mana ki rikice kanshi irin wannan gayun haka da had'uwa, ai hotuna ma basa mishi adalci indai shine wannan", idanunta da ta rintse sbd sarawa da kanta keyi ta bud'esu a hankali daidai inda tasan zasu sauk'a kan d'aya daga cikin enlargements d'in Abutturab dake d'akin tanason sake ganin ko da wani sabon canji ne jikin hoton da sai yau Aunty kulthum d'in ke gani, dubawa tayi sosai bata ga wani sabon abun jiki ba, ganin Ajiddeh batada niyyan tashi ta k'araso bakin gadon ta zauna tareda yaye duvet d'in tace "Au inata magana kin barni ina zuba bazaki tashi ba, Aliyun naki nefa yazo gidan nan har yaga Daddynku kamin ya fita, yanzu haka yana guest parlour side d'innan shine ana ki tashi ki shirya kina kwance ke sarkin son jiki ko?, toh kwanta nan ki jawa kanki salalan tsiya", wani iri Ajiddeh ke jiyo magnar da Autyn nata keyi, yaushe ne Aliyu zaizo gidan nan, saidai in a mafarkanta da ta saba ko kuma in yazo kawo mata takardar sakinta, zumbur ta mik'e kamar wacce aka tsikara tunanin saki da tayi, hawayen taf idonta take kallon Aunty tana girgiza kai tace "Aunty Kulthum wlhy na yadda inyi ta zama da aurenshi koda bazai sake waiwayata ba amma kar ya sakeni, nashiga halin da ban tab'a shiga ba duk tsawon rayuwata, Allah ne ya jarabceni da son Aliyu, da inada yadda zanyi da tuni na cire na huta, son shine ya sani butulcewa Allah har ya kaini ga cutar wani, wlhy zan zauna da aurenshi koda bazai sake kallona ba a nan duniyan amma inason kasancewa matarsa a rayuwar da zamuyi nan gaba, yana bani takardata Dad zai aurar dani ga duk wanda yaga dama ina gama idda kamar yanda yayiwa Yaa Zee, nasan nima cemin zai yi in nemi wani uban idan har yayi min wani auren na kuskura na kashe, kuma na tabbata auren wani ne zai zame mini ajali, Dan Allaah Aunty kije ki bashi hak'uri ya koma da takardarsa, alfarmar da kad'ai zaimin kenan duk da nasan ban cancanci ayi min alfarma ba, ya barni da rad'ad'in da nake kwana in tashi dashi, kinji Aunty", sosai Aunty Kulthum ta tausaya mata ganin yanda ta gama rud'ewa har wani rawa jikinta keyi ta rungumota tace "Hauwa bana tunanin takardarki yazo kawo miki, ga dukkan alamu salama(Peace) yake nema ba akasin shi ba kuma inma hakance ta faru haka Allah ya qaddara miki, haka Allah yayi ke ba matarsa bace, hak'ura zakiyi ki rungumi kaddara, ki sa a ranki Dan Allah kika tuba badan ki samu kyakyawan sakayya ta hanyar samun Aliyu ba", girgiza kai takeyi tana hawaye jin maganganun Aunty Kulthum ta d'ago daga jikinta tace "Aunty so kike ki kwantar min da hankali ko?, so kike kawai inji dad'i, ni nasan wasa kike min", hannayenta duka biyun Aunty Kulthum ta riqo cikin nata tace "Hauwa tun ranar da na fara ganinki Allah ya samin sonki dukda bansan wacece ke d'inba amma na karanci damuwa k'arara a fuskarki, ban d'aukeki a matsayin y'ar miji saidai kallon k'anwa da nakeyi miki kullum, kullum fatana shine inyi abinda zai faranta ran Daddyn ku kamar yadda nima ya faranta min, ya cika min burina da nayi niyyan na mik'a azzaluman da suka cucemu nida y'ay'ana ga hukuma, ya sani cikin farin ciki har nake ganin nafi kowa sa'a, bazan so ganin jininshi cikin k'unci ba, Allah ma muna mishi laifi yana yafe mana, kisa Allah a ranki ki tashi ki shirya kije ki samesu, daga gani yaron d'an babban gidane yanada dattako da mutunci, kiyi fatan Allah ya zab'a miki duk abinda yafi alheri, ke dai ki tuna duk abinda zakiyi da Allah na nan, kinji?" jiki a sanyaye Ajiddeh ke jin duk wani abu da Aunty Kulthum ke fad'a mata, maza Aunty Kulthum ta sata ta shirya cikin lace mai kyau, ta sata ta gyara fuskarta tayi kyan gani, wardrobe d'inta ta bud'e ta ciro mata hijab d'aya cikin hijaban da ta d'inka mata, kallon Aunty Kulthum kawai takeyi har ta gama zira Hijabin, Aunty Kulthum tayi murmushi tace "Masha Allah, kinyi kyau abinki kamar amarya", d'ago ido ajiddeh tayi tana kallonta, Aunty Kulthum taci gaba "Ahap na manta, ashe amarya kike yau tunda za a wajen ango", sunkuyar da kai tayi dan jin kunyar maganar, turaruka ta feshe ta dashi snn tace mata ta k'arasa wajensu, in banda bugu babu abinda k'irjin Ajiddeh keyi, duk wata addu'a da ta kama ma sub'uce mata yakeyi, ta dad'e tsaye wajen kamin tayi shahada ta d'age labulen kanta a k'asa, Abutturab dake zaune duk yacika sbd yana son gano halin da Batuul da Babynshi ke ciki duk ya gaji da jira ya mik'e zai fita kenan ta sako kai, dafarko bai gane ko wacece ma saida yaji Massa yace "Madugu Uban tafiya ai sai ka dawo tunda gata nan gimbiyar taka da kasa hak'urin ta k'araso zaka bita nan ta shigo", dukda gabanta na fad'uwa maganganun Massa sun sa taji dad'i har ta samu k'warin gwiwa sake d'aga k'afa ta k'araso cikin d'akin, jin maganar Massa yasashu juyowa yana k'arewa halittan dake tsaye gabanshi kallo, ya rasa gane me ke bashi mamaki, hijabin da ya gani har k'asa jikin Ajiddeh ko kuma yanda ta koma, Idanunta a k'asa ta kasa d'agowa ta dubesu kuma ta kasa tsayuwa, shi d'inma kallonta yakeyi har saida yaji Muryan Massa yace "ina laifin kace ta zauna sai kaji dad'in kallon nata, amma ka barta tsaye duk k'afarta tayi tsami?", duk da tasan Massa nada barkwanci amma na yau Sam bata jinshi, wani irin relief kawai taji ganin ba kawo mata takardarta sukazo yi ba , wani kallo Abutturab ya jefawa Massa kamin ya samu waje ya zauna, ganin bashida niyyan cewa Ajiddeh ta zauna yasa yace "Uwar gida shine aka guje mu bamusan laifin da mukayi ba,  toh nidai bari in baku waje dan wannan kallon da angon naki kemin zai iya sa hannu ya makeni, kema in na fitan sai kiji dad'in zaman tunda kin qi ki zaunan", ya fad'a yana mik'ewa tareda exiting d'akin, cikin masculine husky voice d'inshi da take muradin ji ko da yaushe taji yace "tsayuwar ke miki dad'i ne da baza ki zauna ba?", jiki a sanyaye hawaye taf idonta ta samu waje ta zauna a gefen kujeran daga k'asa, kallonta kawai yake kamar ba ita bace Ajiddeh da ya sani, sarkin gayu da kwalliya, fuskarta da kullum cike yake da rigima yau duk babu hakan, saima wata nutsuwa da sanyin dake shimfid'e kan fuskar, har wani dogon hijab ta zira abunda bai tab'a ganinta dashi, ko guntune bare yau har k'asa, ko a da in ya matsa mata da tayi Sallah wata riga take zirawa tayi Sallarta da ita sab'anin yau da ta sanya hijab, cikeda nutsuwa yayi maganarsa yace "kinyi laifi amma shine baki iya bada hak'uri ba ko?", hawayen da ya taru mata ne ya shiga silalowa ta d'ago y'an fici ficin idanunta da suka rine ta kallleshi, sai yanzu ta kalleshi for the first time tun d'azu, har wani d'an haske ya k'ara da kyau, janye idonta tayi daga kanshi tana jin nauyinshi da kunyan abinda ta aikata, cikin siriyar muryarta dake cike da kuka tace "I know I was never a good wife, I wasn't a good daughter Inlaw, duk abinda nayi doesn't deserve a second chance, komai nayi nayishi ne sabida son da nake maka, na manta da Allah na nan, na manta shike biyawa bayinshi bukatunsu na alheri, na manta sai da yardarshi abu zai faru, sai da izinin zaka sami abu, na manta da ba komai mutum ke so zai samu ya zame mishi alheri ba, wani hanin ga Allah baiwa ne, son da nake maka yasa na butulcewa ubangijina duk da ya bani komai na rayuwa, nasan I don't deserve your love, Aliyu nasan zuciyarka tsarkakkiyace, fushinka da alhakinka ya kamani, badan halina ba kayi hak'uri ka yafemin, av learnt a lot, na koyi darussa da dama da a ada nake ganin bazan iya yinsu ba, zanje in har gida ince Fatima ta yafemin, Ammah ma zanje ince musu su yafe min, I promise you am not repeating such a mistake, In sha Allah baza ka sake facing problem dan ni ba, everything happens for a reason, kuskurena happened for me to change to a better person, av changed for the good, forgive me plss", ta k'arashe maganan cikin matsanancin kuka da nuna tayi nadamar abinda ta aikatan gaba d'aya abinma mamaki yake bashi, wai Ajiddeh ce ke magana haka a nutse, gaba d'aya jikinshi sanyi yayi, da yaso yi mata fad'a sosai ya nuna mata kurenta kan abinda ta aikata amma gaba d'aya sai yaji tausayinta ya cikashi, a hankali yaji yace "Hauwa", gaba d'aya jikinta saida ya amsa k'iran da Abutturab d'in yayi mata, kamar yaune ta fara jin sunanta daga bakinshi, a hankali ta d'ago rinannun idanunta jin ya sake ambaton sunanta ta sauk'e kanshi, hannunshi d'aya ya mik'a mata alamun tazo ta zauna daga gefenshi, in banda bugawa babu abinda zuciyanta keyi, batayi musu ba ta tashi ta isa kujeran dake gefenshi ta zauna a d'arare, hannunshi d'aya yasa ya kamo d'ayan hannun nata, rawa kawai hannun keyi har saida ya sake sa d'ayan hannun nashi ya rik'e mata hannun duka biyu, a hankali kukan nata ya fara sassautawa, saida yaga rawan jikin nata ya dena tukunna ya d'ago hab'arta da hannunshi d'aya yana k'arewa fuskarta kallo yace "I need not say a lot Hauwa, idona ya gama ganemin komai akanki yanzu, I can clearly see the better changes in you, ina fad'amiki hakan ne bawai dan inason kisan how worthy and valuable Fatima is to me ba, nasan tun kamin wannan lokacin kinsan ya take a wajena, am telling you this dan ke kisan worth d'inta, am here because of her, tamin kuka, tamin magiya duk dan in maidaki tun bata san mey kika aikata ba har bayan ta sani hakan bai hanata yimin magiyar in yafe miki ba", hawayen da take ta k'ok'arin maidawa kar su zubo suka shiga zarya, kuka takeyi na nadaman abinda tayiwa Batuul d'in, ta cutar da ita amma ita da alheri take binta, yaci gaba "babu amfanin maida abinda ya wuce, Marrying her was never her choice, I married her tun bataso but sbd iyayenta, she obeyed them, she sacrificed her happiness for them to be happy and satisfied with her, it was never her fault, keh kinsan I had no intention of keeping a second wife, but yaya zanyi, you caused everything, you made me fall into it, bani kad'ai ba, har parents d'ina saida ya shafa, I can't say no to them, I had to do it a lokacin da suke so inyi d'in, everything happened so fast, I know you will be furious in har kika ji zancen, dukda ban san ya zanyi ba a lokacin nasan babu yadda za ayi in rabu da Batuul, badan ma su Ammah ba sai dan she had been a part of me tun kamin in san da zancen ita zan aura, I wanted telling you a lokacin, I couldn't get how, ban taba sawa a kaina ta haka zaki san matsayin Batuul ba a wajena, am sorry for everything", kukanta ta tsananta tana nadamar duk wani mugun abu da tayi tun kamin zuwaan Batuul gidan har lokacin da tasan matsayinta, murya cikeda kuka tace "Ni zance kuyi hak'uri, wacece ni da zan hana abinda Alllah ya hallata, na d'auka komai nakeso zan samu at my own disposal, nayi watsi da rahamar da Allah yayi min naqi bin umarninsa ai dole inga ba daidai ba", sam ya kasa yarda da Ajiddeh ce gabanshi yau take maganan masu hankali, ajiyar zuciya ta Sauk'e tace "How is she?", girarshi d'aya ya d'age alamar tambayn wa kenan?, a hankali ta furta "Batuul", wani wide smile ta gani shimfid'e kan fuskarshi jin ta ambaci sunan Batuul, tun d'azu yake son yaje ya sake ganinsu itada Babynshi, itama murmushin tayi ganin yanda murmushin yayi mishi kyau yace "She gave birth today, yanzu hakaR tana asibiti, I came to fulfill her promise", ido Ajiddeh ta wara tana dad'a widening smile d'inta tace "Aliyu dagaske?, yaushe ta haihu?, Ya Allah mey ta samu?, plss muje in ganta kaji?, plsss" murmushi yayi yana mik'ewa yace "d'azu, su nake son zuwa in duba, we will talk ltr", kamin tayi magana har yayi gaba kamar wanda ake turawa, har yaje bakin k'ofa ya tuna da Mum, juyowa yayi suka kusa cin karo yayi maza ya rik'ota, ko bata fad'a ba response d'in da jikinta keyi ya isar ya nuna mishi tayi missing d'inshi, murmushi yayi a hankali yayi leaning yayi kissing d'inta, saida ya saketa yana maida numfashi yace "Zaki sani yin abin kunya gidan surukai ko", murmushi tayi tareda lumshe ido tana godewa Allah da ya dawo mata da Aliyu tace "kaima ai gidankune", yace "Mum fa?", take murmushin dake fuskanta ya b'ace, a sanyaye tace "Its been seven months tunda Mum ta kwanta ciwo, ka tuna lokacin da nake ta k'iranka baka picking, I tot I dd lose her, inaso ko sau d'aya ka ganta ka yafe mata itama kai da su Fatima but duk inda nabi bana samun nasara", hannun ta dake hannunshi ya damqe yace "Tana gidane har yanzu?", ta kad'a kai tace "Yeah tana side d'inta", ya jawota gabanshi yace "Muje in dubata before I go", ba musu ta bishi a baya har side d'in Mum, saida ta fara shiga kamin ta fito tace ya shiga shima, Mum zaune cikin wheelchair duk ta rame kamar ba ita ba, tana ganin Abutturab hawaye ya fara zaryo mata, akan cutar da wannan bawan Allah taga ishara, gata nan zaune babu abinda zata iya yiwa kanta saidai ayi mata dashi, tana ji tana gani, har k'asa ya tsuguna ya gaida ta cikeda girmamawa, sosai ta nemi da su yafe mata su dukkansu tace kuma har gida zatazo ta samu su Batuul su yafe mata, Abutturab kam kasa cewa komai yayi, wai wannan itace Mum da last time da ya ganta tana ta bambamin anyi y'arta sharri baza ta yadda ba yau itace zaune haka bata iyawa kanta komai, dama in baka godewa Rahamar Allah ba ai ka godewa azabarsa, tun da lafiyarka baka more shi ba gashi yanzu kana nema ma babu hali, mik'ewa yayi bayan sun gaisa ya fad'awa Mum abinda ya kawoshi snn yayi sallama da ita akan anytime suka gama shirya Ajiddeh sai ayi mishi magana, murna fal ran Mum ta dinga mishi godiya, har mota Ajiddeh ta rakashi kamar kar ya tafi ta dinga ji, so yake kawai ya ganshi kusa da Batuul, a mota ya tarar da Massa yana jiranshi, sallama sukayi suka wuce, a hanya Massa ke fad'a mishi Ammah ta kirashi akan anyi discharging Batuul, da sauri ya ciro wayarsa cikin aljihu, missed calls ya gani nasu Ammah da sauran mutane kasancewar wayan na silent, number Batuul kawai yayi dialling dukda baiga missed call d'inta ba, bugu biyu ta d'aga, cikin siririyar muryarta tace "Hello", ajiyar zuciya ya sauk'e yace "Glitterrr", jin yanda yaja sunan nata tasan something is wrong, kamin tace wani abu yace "Glitter sun tafi min da ku ko?", murmusshi tayi kaman yana gabanta a hnakali tace "All thanks to Aunty, tace da nan da can d'in duk d'aya ne, duk care d'in da zata bani Ammah will give me better, taqi a tafi dani gidanta, I know you will be happy shiyasa banyi insisting ba", wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauk'e yana fad'in "Alhamdulillah, Glitter! Allah ya k'arawa Aunty tsawon rai, lafiya da Imani, Aunty is the best kin sani ko", sosai Addu'ar tayi mata dad'i tace "Amin Yaa Abu", yace "Twinkle fa?, bacci take ko?", d'an yatsina fuska tayi dan bata gane wa yake nufi ba tace "Waye kenan?", yace "Glitter mana, bayan ke akwai wanda zan tambaya at this right moment bayan Babyna?", kai ta kad'a tana dariya tace "Ohhh sunan da ka saka mata kenan?", yace "Yeah, she twinkles kamar yadda kike glitter, she so cute, dama na fad'a miki I want a baby just like you, God has answered my prayers, Thank you kinji, Allah yayi miki albarka", dariya tayi tace "Amin Amore, Kaji Ammah na cewa in huta", yace yanzu zan k'araso ne ai, babu mai hanani ganinki, you rest well kinji, take care of yourself and twinkle for me", ido lumshe  ta amsa da "sure I will do that", ajiyar zuciya ya sauk'e tareda sauk'e wayan ya juya yana kallon Massa da gaba d'aya hankalinshi ke kan driving, hira suka shiga yi har suka isa gida dab da magrib, saida suka fara yin sallah masallacin dake jikin gidan kamin su shiga gida, har mamakin matan dake gidan yayi kamar yau ake taron sunan,  kukkutsawa ya riqayi suna gaisawa har ya samu ya shiga d'akin da ya San Batuul na ciki, wani irin serene and peaceful k'anshi d'akin yake, ga wani d'umi da d'akin yake, manyan burners d'in turaren wuta na k'asa a angle d'in d'akin har biyu, Batuul na kwance kan gadon itada jaririyarta, jingina yayi tareda k'ofan yana kallonsu tareda ajiyar zuciya, duk wani numfashi da zaiyi yana jin so da  k'aunar halittun nan na Allah guda biyu da suka zama part of rayuwarshi cikin lokaci kad'an, a hankali ya tako ya k'araso bakin gadon tareda zama yana kallonsu, jin mutum kan gadon ya sata bud'e lumsassun idanunta ta sauk'e kanshi tareda mishi murmurs hi, murmushin shima yayi mata yana matsawa kusa da ita, tashi tayi tazauna tace "sannu da zuwa", baisan mey zai mata ya nuna mata farin cikinshi ba, hannu yasa ya zagayeta tareda rungumota jikinshi, murmushi tayi tareda yin lamo jikinshi tana jin dad'in d'umin dake jikinshi, kamar wacce ta tuna da wani abu tayi maza ta tashi daga jikinshi tana kallonshi, kallonta shima yakeyi dan wannan kallon nata bayason irinshi, langab'ar da kai yayi tareda d'age girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, a hankali har idonta ya fara kawo ruwa tace "your scent?, ban sanshi ba", gaba d'aya ya manta da ya rungume Ajiddeh, k'anshin turarenta ne dake jikinta ya kama mishi kaya shine Batuul taji yanzu, marairaicewa yayi kamar shima zaiyi hawayen shima yace "Fatima I went to her, ba kince in dawo da ita ba?", wani irin fad'uwa gabanta yayi, wlhy ta manta da tayi mishi zancen ya dawo da Ajiddeh, hannunta dake zagaye jikinshi ta k'arasa warwarewa, hannayen yayi maza ya rik'o yana girgiza mata kai yace "No Fatima, kefa kikace in dawo da ita, I gave you my word and I honoured it, for you, for your happiness", a hankali ta sauk'ar da idonta hawaye na gangarowa tace "I didn't say anything", ta fad'a tana kawar da kanta, hannu yasa ya tallabo fuskarta yace "Look at me kinji, plsss", a hankali ta dubeshi yace "ya kikeso inyi Fatima?, I want you happy, mey kikeso inyi to keep you happy?", jiki a sanyaye tace "just love me, always", ta fad'a tana lafewa jikinshi, hugging d'inta yayi yana kissing goshinta yace "In sha Allah Fatima, to the best of my ability kinji?", kai ta gyad'a mishi kawai, saida aka k'ira isha kamin ya fita bayan yayita kwantar mata da hankali lokacin Farida da Aunty Amna sun shigo d'akin, Ranan Suna da asuba a masallalci bayan an idar da Sallah aka rad'awa Baby suna A'eesha(Fareeda), Sadiq ne ya fara k'iran Fareeda ya fad'a mata sunanta aka sawa Babyn, ihu ta saka, ta rasa ina zata saka kanta dan murna, duk wani angle d'in gidan saida tabi tana fad'awa kowa sunanta aka maidawa Baby, kasa hak'ura tayi su dawo daga Masallaci ta tafi bakin gate  tana jiran dawowansu, yana shigowa yaji an rungumeshi, kuka ta fashe da jinta jikin Abu, ta dad'e da sanin son da yake mata amma bata san har ya kai haka ba, da murmushi a fuskanshi ya d'agota yana kallon yanda hawaye ke zarya, ya had'e rai yace "zakisa twinkle ma ta zama cry baby ko, to zan fasa", dariya tasa tana girgiza kai tace "Na daina, kaga ko, nayi shiru", ta fad'a tana share hawayenta, dariya shima yayi yana shafa kanta yace "that's my lil sis", dariya tayi ta sake komawa jikinshi tace "Yaa Abu I love you for being the best brother ever", "I love you too", ya kama hannunta suka shiga ciki, a d'aki Batuul ta fito wanka kenan Ammah ke fad'a mata sunan Fareeda aka maidawa Babyn, sosai itama taji dad'i, a nan take bawa Batuul lbrn Abu ne ya sawa Farida inkiyarta ta Farida lokacin da aka haifeta sbd son da yake mata, yaso Farida ya zama shine ainahin sunanta amma lokacin Abui ya mata hud'uba da A'eesha, shine sai Faridan ne ya bita, yanzu haka ba kowane yasan asalin sunan Faridan ba, Addu'a tayi musu Allah ya k'ara musu zumuncinsu, Farida ce ta shigo riqe da wani k'aramin chest box, Batuul ta mik'awa box d'in tace "You know I love you ko?", dariya Batuul tayi tana saka kayanta tace "sai yau kike jin tunamin da son da kike min?", Farida ta mik'a mata akwatin tace "This is for Lil Farida", karb'a tayi taga golds ne ciki, mirmushi kawai tayi ta ajiyeshi gefe dan batasan mey zatce mata ba, tare suka gama shirinsu, sosai akayi shagalin suna, Batuul da Baby suka samu kyaututtuka sosai, sai ranan Ammah ke jin Komarwa Ajiddeh ganinta tazo sunan itama da kyaututukanta, Ammah sam ba haka taso ba, amma jin Batuul  ce tayi insisting dawon nata ta hak'ura, dama dan ita take k'in komawan Ajiddeh, bayan wata hud'u suka tarkata suka koma UK har Ajiddeh

*FOUR YEARS LEAP*
     EPILOGUE

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now