💖💝BATUUL 56💖💝

8.1K 396 0
                                    








Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





       Ba karamin rudewa Batuul tayi ba a lkcn, duk jikinta ya dau rawa sae tutturasa take tana neman kwace kanta amma ta kasa, gajiya tayi ta tsaya ganin ba saketa xae yi ba, banda hawaye babu abinda take, duk jikinta yayi sanyi, ko lura da halin da ta shiga bae yi ba don idonsa a lumshe suke, yakai minti biyar yana abu d'aya kmr wanda ya tuna abu ya xame bakinsa daga nata a hankali, sae dae ya kasa kallonta, kuka ta fashe da ta xame jikinta daga nasa tayi saurin janyo towel dinta ta rufe jikinta, bae bari sun hada ido ba ya mik'e ya fice daga d'akin da sauri, kuka sosai ta shiga yi bayan ya fita, takai minti goma tanayi daga baya ta mik'e da kyar ta koma toilet ta wanke fuskanta, vanity stool d'in ta jawo ta zauna jiki a sanyaye, kallon lips d'inta da ya koma ja  ta tsaya yi jikin mirror, a hankali ta d'aura babban yatsan ta kai tare da lumshe ido hawayen dake makale idonta ya gangaro, bud'e ido tayi ta janyo man shafanta, jiki a sanyaye ta gama shafa man taje ta sako kaya, har ta gama ta kwanta jin lips d'inta take ba daidai ba, gashi bata daina jin taste din bakinsa a nata ba, lumshe ido kawai tayi ta kwanta.




       Ajiddeh kam na xaune dakinta bayan ta watsar da kwalaye da ledan da ta shigo da, duk abun duniya ya taru yayi mata yawa, banda huci babu abinda take yi ita kadae, wannan wace irin jarabace aka turo mata gidan ta, anya ma kuwa zata iya ci gaba da yin wannan abinda Mummy ta fad'a mata, wai dan wulak'anci Aliyu har shi zai wani tashi ya zaga ya bud'ewa y'ar iskar nan k'ofa bayan ita ba yi mata yake ba, to me hakan ke nufi, fad'awa tayi kan gado tana maida numfarfashi, da tun farko tasan zuwansu Nigeria da Abutturab zai zama haka da bata barshi ya tafi ba, ko ita da taje ta dawo, wani hawayen bak'in ciki ne ya shiga zubowa daga idonta, ta mike xaune ta fashe da kukan takaici, ita kam ya xata yi da Batuul? wayanta ne ya shiga ringing, jawowa tayi da sauri ta kara a kunnenta, jin mai k'iran ya sata share hawayenta da sauri, daga d'aya b'angaren Mummy tace "Ajiddeh Jiddeh, jiddum fi khair ana, useki  y'ar albarka, naga abin kirkin da kika turo, ba b'ata lokaci yanxu zan turawa su Zainab, daga can za a turo miki ba sai sun dawo gida ba, zamuyi maganan duka details d'in in suka iso", toh kawai ta iya cewa dan wani irin tuquqi da zuciyarta keyi mata, Mummy ce taci gaba da ce mata "kuma kici gaba da yi kamar kina son nata, dan komai yazo mana da sauk'i, ko meye ya sameta kinga baza ayi zarginki ba dan babu wanda yasan kina k'inta, shi kuma sai sun dawo d'in sai muji yadda nashi abun yake", tace "toh Mummy duk zanyi", da haka suka katse k'iran dan maganar ma wahala take bata, turo k'ofar d'akin yayi ya shigo, da ido yabi kwalayen da ice cream packs d'in dake zube a k'asa har wasu sun fara malalewa, tattarewa yayi yazo bakin gadon ya zauna, hannu yasa ya d'agota kanta yana kallon yadda idonta ya canja, "kina da lafiya kuwa, zaki d'ebo abincin kixo ki watsar dasu anan kamar a bola na tsinto kudin, kina ma da hankali kuwa?", zuciyarta ta shiga dannewa tasa hannu tana d'an murza kanta tace "Baby kaina ke min ciwo, har jiri jiri nake gani shiyasa ma kaga komai a k'asa, ba zubarwa nayi ba", kallonta yayi yana examining d'inta gabaki d'aya sannan yace "kin fad'amin? ko kuma kinada maganin sha ne", kai ta girgiza ta shige jikinshi tace "c'mon babe, kasan banso kana damuwa shiyasa ban fad'i maka ba, I will b fine, you don't worry", ta k'ara shige mishi jiki, hannu yasa kanta yana shafa gashinta mai d'an karan laushi ya lumshe ido sae dae ji yake kmr har lkcn bakinsa na cikin na Batuul, a hankali yace "tashi kici abinci sai ki kwanta", ba musu ta tashi ta janyo kwalin pizza, har ta bud'e ta d'au d'aya zata kai baki, ta kalleshi da wani irin murmushi fuskanta ta wara ido tace "babe", d'ago kai yayi ya kalleta tareda d'aga mata giranshi d'aya yana jiran jin mey zata ce mishi, "our Sister, bari inje in kai mata share d'inta, nasan she is famished, daga school ma take kaga dole taji yunwa", k'ok'arin mik'ewa tayi yasa hannu ya dawo da ita ta zauna tana kallonshi, murmushi yayi yace "rabu da ita, in tana jin yunwa zata sauk'o ta samarwa kanta abinci", kai ta shiga girgiza mishi zatayi magana ya sa hannu kan lips d'insa yace "shhhh, eat and get some rest, bakya jin dad'i you shouldn't bother, she will b okay", wani irin murmushi tayi murna fal ranta kamar tayi yaya, bata damu da ko yanaci ba, haka ta dinga tunkud'a abincinta, tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Batuul kawai yakeyi yana kallonta don tun da yake kissing dinta bae taba samun natsuwa irin wanda ya samu gun Batuul yanxu ba, it was just amazing, lumshe ido yayi ya kwanta kan gadon Ajiddeh, gaba d'aya komai dawo mishi ya shiga yi a hankali, hotunan Ajiddeh dake kan wayar da ta goge ya tuna, baisan lokacin da wani slight murmushi yayi escaping lips d'inshi ba, then why did she delete the pictures ita da ba ma son shi take ba what made her jealous, wayanshi dake gefen Ajiddeh ne ya shiga ringing, zuciyanta ya bada sautin dam, ganin mey k'iran, jiki a sanyaye ta d'au wayan, wani zuciyan ke ce mata ta katse wayar dan ita tsoro takeji, kamin tayi abinda zuciyarta ke kissa mata ya bud'e lumsassun idonunshi, a tsorace ta mik'o mishi wayan ganin ya bud'e ido, tashi yayi daga kwance ya risina ganin mai k'iran ya karba wayar, a kunnenshi ya kara a nutse ya amsa da sallama yace "salamu alaikum, nda dubdo Ammah", amsa mishi sallamar tayi tace "Ya kuke Abu, yasu Hauwa'u", kallon Ajiddeh yayi sannan yace "suna lafiya Ammah, ya gida ya k'arfin jiki?", tace "Alhamdulillah, kana jina, kayan Batuul da aka turo yau zasu iso, dan haka in suka iso kaje ka karb'o su sannan sai inyi magana da ita, inaso in mata explaining abubuwan dake ciki da yadda amfaninsu yake, mik'amin Hauwa'u inyi magana da ita in tana kusa", Ajiddeh ya mik'awa wayan sai muzurai takeyi da ido don gaba daya hankalinsa ya tashi don bae san me Ammah xata ce mata ba, jiki a sanyaye ta karb'i wayan tasa a kunne, xuciyanta sai double flip yakeyi, sai da Ammah ta k'ira sunanta sannan ta amsa, a daburce kamar mara gaskiya tace "Na'am Ammah ina wuni", sau d'aya Ammah taji muryarta tun bayan aurensu da Abu, ba yabo babu fallasa Ammah ta amsa mata da "kuna lafiya Hauwa, ya y'ar uwarki", har cikin ranta take jin yadda Ammah ta k'ira Batuul y'ar uwarta, kamar munafika tace "muna lafiya", Ammah tace "yayi kyau, ki kula da ita kamar yadda zaki kula da taki k'anwar kin ji, nasan Batuul batada Matsala, nasan abin yazo miki bazata, ki d'auka kaddara ce, tun can da rubutacce ne, ki barwa Allah komai sai kiga yazo miki da sauk'i, Allah yayi muku albarka, ya kad'e duk wata fitina cikin zamanku, kuyi zaman lafiya keda Y'ar uwarki, Allah ya baku zuri'a d'ayyiba ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka", har Ammah ta gama maganan da zatayi k'wak'walwarta ta kasa processing maganganun da takeji, gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, suyi zaman lafiya ita da y'ar uwarta, wannan magana ai kishiyoyi ake fad'awa, maza tayi ta cire tunanin daga ranta tace "Toh Ammah mungode", daga haka ta mik'awa Abu wayan tana kallonsa, bayan sun gama maganan da zasuyi da Ammah sukayi sallama, kallon Ajiddeh yayi, she wasn't looking herself anymore dan abincin ma ta denaci, yana bud'e baki zaiyi mata magana wayarshi ta sake ringing, bai d'auka ba har ya katse dan lamba ce bak'uwa, sai da aka sake k'ira a karo na biyu ya dauka, muryan namiji yaji yace "This is Daniel speaking from Birmingham port authority, we call to notify you d arrival of your cointainer, we would like you to come and claim your property", ajiyar zuciya yayi, kayan da Ammah ta fad'i kenan, cewa yayi "Aiit, I will be there surely soon", "Thank you", mutumin yace mishi sannan suka katse wayan, Ajiddeh dae ta kafa mishi k'ananan idanuwanta ko kifta wa bata yi, iska ya hura mata yace "what are you thinking about wife, obviously me", a hankali ta kalleshi har lokacin hankalinta tashe tayi murmushi tace "Ba komai", ta juya taci gaba da cin pizza ta, ba wai dan ya yadda ba ya k'yaleta, mik'ewa yayi yana kallonta yace "I will b back soon, take care", da haka ya fita daga d'akin da ido kawai ta bishi dan ba daidai take jinta ba, sai da ya kalli kofar d'akin Batuul kamin ya sauk'a k'asa, d'akinshi yaje ya d'auko key ya fita, tafiyar minti 25 ya isa gun port authority, container number ya fad'a musu bayan ya k'ira Ammah ta sanar dashi number, da mamaki yake kallon kayan, bai tab'a tunanin haka kayan keda yawa ba, ta ina ma zai kai kayan nan gidanshi, kana gani kasan lefe ne na aure, idea ne ya fad'o mishi kawai yasa akayi loading kayan a babban mota, yana gaba babban mota na biye a baya, gaban wani gida da rabinshi duk glass ne suka tsaya, nan aka sauk'e kayayyakin, mutanen ne suka shigar da komai ciki, sai da suka gama ya sallamesu suka tafi, shiga yayi ciki ya kwanta kan sofar parlour, wayanshi ne ya shiga ringing, Ammah ce take k'ira , yana recieving tace "Ka amso kayan?", hannu yasa cikin gashin shi a hankali yace "Ehhh Ammah, but ban k'arasa gida ba", yasan tunda Ammah tace zatayiwa Batuul magana yau d'innan sai tayi, ya lumshe ido yace "In sha Allah Ammah, ina komawa zan bata wayan ", bata tsaya jin komai ba ta katse wayan, bai bar gidan ba sai bayan 30mins,




     Kai tsaye d'akin Batuul yaje da ya koma gida, kwance ya tadda ta tana bacci abinta hankali kwance, daga ita sai d'an bum short da crop top ta takure waje daya ga xanin ta a gefenta, yafi minti biyu tsaye yana kallonta daga baya ya janye idonshi ya bud'e closet d'inta ya Ciro mata dogon hijab, hannu yasa cak ya d'auketa, baki ta bud'e zata sa ihu ya matseta jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e jin k'anshin turarenshi tayi lamo jikinshi sae dae gabanta faduwa yake, har sai da ya kaita mota sannan ya bud'e ya direta ya jefa mata hijab d'in da ya d'auko mata shima ya zaga ya shiga daga gefen driver ya tada ya bar compound d'in, kallonsa take a tsorace sae dae ta kasa cewa komae, a hankali ta saka Hijab dinta da ya jefa mata.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now