💖💝BATUUL 66💖💝

11.5K 460 15
                                    




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




         A firgice ta tashi daga baccin da ta kwanta dan bata san sanda tayishi ba, d'akin ta k'arewa kallo gaba d'aya, sai a sannan ta fara tariyo abunda ya faru jiya, ba karamin tsoro ne ya kamata ba, jikinta na rawa ta jawo wayarta da ta sa k'ark'ashin pillow taga 9 na safe, da sauri ta shiga dudduba kanta hankali a tashe, ajiyar zuciya ta sauk'e ganin bata ga alamar komai ba, d'akin ta sake examining taga jakanta a bude an barbaje kayan ciki, mik'ewa tayi ta isa inda jakar yake da sauri tana dubawa taga an yashe duka kud'in dake ciki, a guje ta fito daga d'akin, kalle kalle ta tsaya yi ganin d'akuna dayawa a Jere, a guje ta bankad'a d'aya ta shiga, gabantane ya fad'i ganin irin kwanciyar da yayartata tayi, Yaa zee itama na kwance lakad'an tana bacci abinta, duka ta d'aka mata a baya tace "Yaa Zee ki tashi dalla kin kwanta sai bacci kikeyi", da k'yar ta iya bud'e ido tana kallon Ajiddeh dake tsaye, kanta ta koma kallo, a firgice ta tashi tace "keh meye zaki zo kina min ihu?", wani irin kallo Ajiddeh ta dubeta dashi wani xufa na keto mata tace "dallah ki tashi kin kwanta bacci sai kace gawa, toh mutumin nan wllh Yahoo guy ne, in zaki farka ki farka kisan inda dare ya miki", a firgice ta sauk'o daga kan gadon, sai lokacin ta lura da kayanta dake zube a d'akin, a wulak'ance ta kalli Ajiddeh tace "toh kuma meye na hargitsa min kaya?", wani dogon tsaki Ajiddeh taja tace "dallah can bakiji mey nace miki bane?, wannan taqadarin da kuka kawo mu gunshi ba malami bane, macuci ne b'arawo", a rikice Yaa Zee ta shiga duba kayan nata dake zube, wani irin ihu ta kurma tana fad'in ta shiga uku, kafad'un Ajiddeh ta kamo tana ihu tace "Keh ya cuceni, mutumin nan ya cucemu, har golds d'ina da akwai cikin jakan nan ya kwashe, na shiga uku", tsaki Ajiddeh taja ta janye hannun Zee dake jikinta, a guje Zee ta juya ta bar d'akin, a bakin k'ofa suka ci karo dasu Mummy suma sun fito jin ihun da sukayi, Aunty Jainaba ce ta rik'ota tace "shinu?, bakal abuki, ki fad'amin ihun mey kikeyi?, babu abinda Zee ke yi in banda ihu sai cewa take "Ya anahe, mun shiga uku", Ajiddeh suka hango itama tana tahowa duk ta birkice, Mummy ce ta k'arasa gun Ajiddeh tace "keh shinu dige?", baki ta tab'e tace "Oho, wai malamin nan naku ne d'an 419, ya kwashe mana komai namu, ni dama tun farko ba yadda nayi dashi ba, tun farko ma wai wa ya hada ku da shi?", hannu Mummy ta d'aura aka sukayi ta kurma ihu, straight parlourn da aka fara kaisu sukaje, ko carpet d'inma da aka shimfid'a d'azun babu bare alamar mutum, wani sabon kukan suka sake sawa wannan karan harda Jainaba, dan takaici Ajiddeh kasa cewa komai tayi sai ido da ta zuba musu tana gumi, sunkai minti talatin suna abu d'aya, tsaki taja ta mik'e tana kallonsu daga karshe tace "in zaku tashi mu nemawa kanmu mafita ku tashi, don zaifi mana da wannan zaman kukan mara amfani da kukeyi", da rinannun idanuwansu suka d'ago suna kallonta sukace "toh ya zamuyi", a k'ufule tace "Ku zauna kuyita kuka", ta juya ta koma d'akin da aka sauketa, sauran kayan da ya bar mata ta kwasosu a akwatin ta fito janye da kayan, da ido suka bita su dukkansu har tazo ta wucesu, da hanzari suka miqe sukayi ciki suma suka tattaro nasu komatsan, kiciniyar bud'e gate d'in suka tarar da ita tanayi, juyowa tayi ta kallesu tace "D'an iskan ta waje ya rufemu, yanxu sai an samu wani ya haura ya bud'emu, Mummy duk keh kika janyo wannan abin da kika wani ce mishi har miliyan hamsin zamu bashi, ai ko yana da niyyan aikinma dole shed'an ya rud'eshi da tunanin muna da kud'i yayi mana sata (Lol, nikam nace ko ba shed'an ba), yanxu sai kusan yanda za ayi a bud'e mu fita daga nan", hawaye Mummy ta share tace "Wlhy Zainab da Janaiba ne suka samoshi, bansan a ina ba", shawara suka yanke da ayi hawa hawa sai mutum d'aya ya dira ta waje ya bud'esu, Mummy ce ta fara tsugunawa, Janaba ta haye kanta sai Zee, Ajiddeh ce ta samo ta dirqo, chain d'in aka rufe k'ofan da ta warware ta bud'e musu suka fito, ba a jin motsin kowa sai kukan tsuntsaye, a haka suka fito suka kama hanya, saida sukayi tafiya mai nisa duk sun galabaita har sun fara canza kamanni tukunna suka ga wata mota da aka kwaso bunsurai a ciki, tsaida mai motan sukayi sukace mishi ya kaisu cikin gari, cikin bunsuran  nan suka kutsa suka zazauna duk wari, Ajiddeh dae kasa kuka ma tayi don takaici, sai da ya kaisu cikin gari sannan Mummy ta ciro kud'in can ta bashi dan bai wuce d'ari biyar ba, sai da suka nemi abinci sukaci daga nan suka fara tunanin yadda zasu koma gida, Ajiddeh ce tace "Mum nifa ban kuma kwana garin nan, kusan yadda zanyi In koma dan in Aliyu ya gano k'arya nayi mishi to kowa sai ranshi ya b'aci", Aunty Jainaba da tayi tagumi tace "yanzu abinda za ayi, ni akwai kudi guna tunda shi d'an iskan can bai shigo ya tsiyata mu ba, amma kud'in ba masu yawa bane, ba zaiyi sponsoring mu duka ba, sai dai in zaki fara tafiya ke sai ki turomana mu koma muma, kamin nan zamu zauna wajen Ayyi har ki turo sai a San abin yi, da haka suka yanke shawara suka rakata airport suka yankar mata ticket, Mummy ta share xufa tace "Toh ae ynxu sai mu koma gun mai mana aiki da, don dama ba wai bae iya aikin bane, aikinsa daukan lkci gare shi kafin ya ci," ko kallonta Ajiddeh bata yi ba, don abun duniya sun taru sun mata yawa, ga uban asaran kudin da tayi.




💖💝BATUUL💖💝Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon