💖💝BATUUL 69💖💝

10.7K 487 14
                                    




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*









         Washe gari da safe kamar yadda ta saba tashi haka ta tashi, sai da tayi Sallah tukunna tayi wanka ta gyara d'aki, ta koma toilet ta wanke sannan ta fito tayi kwanciyarta kan gado saboda jirin da take ji, jin jikinta ya d'anyi dama dama yasa ta mike ta fita daga dakin ta sauk'o k'asa yin breakfast kamar yadda ta saba, a gurguje ta shiga gyaran parlour dan bata son yin latti, lecture 11 ne da ita, gashi jiya ma bata samu taje ba, kitchen ta shiga ta harhad'a kayan abincin da zata dafa grilled fish da salad ta shiga had'awa, tana jin saukowan sa parlor da Ajiddeh ta tabe baki ta ci gaba da aikinta, kunun gyad'a ta dama sannan ta shiga baking musu chicken pie, Oven d'in da kifin ke ciki ta bud'e zata duba ko yayi, tiririn dake fitowa ciki yasa taji kanta ya fara juyawa ga tashin da zuciyarta ya fara, ba shiri ta yadda hand napkin dake hannunta jin amai na yunk'urin zuwa mata ta fito daga kitchen din da sauri, yana kwance a parlour ya lumshe ido, Ajiddeh na kwance jikinshi duk ta wani kanainayeshi, abubuwane kawai suke mishi yawo akai, duk he was just confuse, Ajiddeh kuma ba hankali ta cika ba da komai zaizo mishi da sauk'i, dan ko jiya shirmen da ta dinga mishi darajar Auntyn ta dake gidan taci da yayi maganinta, gaba d'aya bayajin zai iya yin nesa da Batuul, she has become part of him, duk da shi dai yasan ba wai sonta yake ba amma har cikin ransa yake jin ta, dole ne ma yasan yadda zai sanar da Ajiddeh dan bazai iya cigaba da b'oyewa ba, inma ya b'oyen to dole attitude da movements d'inshi su nuna, lumsassun idanunshi ya bud'e jin motsi kamar an fito a guje, inda yaji motsin nan yabi da ido, Batuul ya gani bakin staircase ta durkushe wajen tana kwarara amai, baisan lokacin da ya ture Ajiddeh dake jikinshi ba ya mik'e a rud'e ya iso inda take, rik'ota yayi ya jawota jikinshi yana rik'e da ita har saida yaga ta gama aman, Ajiddeh ce ta k'araso wajen ta rik'e k'ugu sai karkad'a jiki take taja wani dogon tsaki tace "iskancin banza, ke iskancin naki har ya kai da yi min k'azanta a parlour, jibi yadda kika b'ata min gida da amai, toh wlhy sai kin gyarashi tsaf, nan yayi maki kama da toilet", ko ta kanta Abu baibi ba ya d'aga Batuul da ta gama galabaita cak yayi sama da ita, bai ajiyeta ba sai da ya shiga toilet d'in d'akinta sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta, tana rik'e jikinshi har lokacin, suna fitowa ya kalleta with care yace "mey ki kaci ya saki amai?", ko kulashi batayi ba saima k'ok'arin k'wace jikinta da ta shiga yi daga hannunshi, suna zuwa bakin gado ya saketa, kamar jira takeyi yana saketa ta sulale tayi kwanciyarta kan gadon ta lumshe ido tana maida numfashi, ganin ta lumshe ido yasa kawai ya k'yaleta ya gyara mata kwanciyarta yayi waje, k'asa ya sauk'o ya tarar Ajiddeh bata nan, kitchen ya shiga ganin stoves a kunne duk ya kashesu sannan ya d'auko Vacuum cleaner ya shiga gyara gun da tayi aman, d'akin ya koma yaga alamun tayi bacci, ya sauke ajiyar xuciya yaja k'ofan ya rufe, toilet d'in d'akin da ya kwana ya shiga yayi wanka ya canja wasu kayan, key d'in motarshi ya d'auka ya fita daga gidan yaje eatery siyo musu breakfast, har lokacin baiga Ajiddeh ba, d'akinshi da yasan zai samesu yayi knocking, ita ta taso ta bud'e mishi k'ofa, tana ganin shine cike da masifa tace "inji dai ta fito ta gyara min parlourn dan ni I can't withstand wannan K'azantar," wani mugun kallo ya sakar mata sannan ya dungure mata ledan ya juya ya barta nan tsaye baki a sake, kwafa tayi ta  d'auki ledan ta juya ciki, d'akin Batuul ya koma da sauran ledojin dake hannunshi yaga tana bacci har lkcn, bakin gadon ya zauna ya zuba mata lumsassun idanunshi, tausayinta ne gaba d'aya yaji yana ratsashi, har ta d'an fad'a, to wai ma me ke damunta haka, deciding yayi idan ta tashi still not ok su tafi hospital kawai, hannu yasa ya gyara mata gashin da ya zubo mata fuska sannan ya d'an shafi fuskan nata ya miqe ya fita waje, yunwa yakeji amma baijin cin abincin waje at all, kitchen ya shiga yaga kunun data fara, k'arasawa yayi ya ciro kifi da meat pie d'in da tayi baking, ya nufi dining ya zauna yaci, sai lumshe ido yakeyi yana cin abincin, a ranshi kuwa cewa yakeyi "She is angel, always different", addu'a samun sauk'i ya dinga yi mata har ya gama cin abincin shi, parlour ya koma ya kwanta dan bai tunanin yau zai iya fita ya bar Batuul, duk bayan 30mins sai ya shiga ya dubata, Sallah azahar ma yau a gida yayi baije masallaci ba, baiso ta tashi baya nan, mamaki ne ya kamshi ganin har la'asar tayi amma bata farka ba, kuma baccin nata normal, yasan bata irin wannan baccin haka, ita kuwa da ta tashi wani baccin ke dauketa, bayan yayi sallahn magrib a gurguje ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya fara kaiwa Ajiddeh nata sannan ya shiga d'akin Batuul har lokacin tana bacci, deciding kawai yayi ya tasheta sabida baccin yayi yawa, a hankali ya shiga tashinta bayan ya hau kan gadon, da k'yar take iya bud'e ido tana maidasu ta lumshe, d'agota yayi ya jinginar da ita jikinshi yace "Hey wake up, wannan wani irin bacci ne, tashi kici abinci, its already late, bacci tun safe", a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta k'arewa d'akin kallo, a kanshi ta tsaida kallonta tace "Farida bata iso ba?", tana sake lafewa a jikinshi, d'agota yayi yace "tashi kici abinci", had'e rai tayi ta zumb'uro mishi baki tace "Ina Farida nace?", tana magana tana dad'a sulalewa jikinshi, ganin baza ta tashi ba yace "Farida anyi delaying flight d'insu sabida bad weather baza su iso yau ba sai gobe da safe", daga haka ya d'agata ta zauna, hannu yasa ya janyo pack d'in abincin yace "C'mon zo kici abinci", ya bud'e pack d'in, da sauri ta matsa baya tace "mey wannan d'in?, ni banaso", da mamaki yake kallonta yace "ba kya so kuma, duk yau baki ci komae ba fa, c'mon have it, ya d'ebo daga cikin spoon d'in ya kawo mata baki, da sauri ta toshe bakinta da d'ayan hannunta d'ayan kuma ta ture hannunshi da ya mik'o mata gabanta tace "Nace banaso, banason k'anshin abinci bazan ci ba, ka fita dashi", kallon mamaki kawai yake mata, rai b'ace cike da masifa tace "ka matsar mana, nace fa bazanci ba", abincin ya matsar gefe kamar yanda tace ya rik'ota da damuwa yace "toh mey zakici",  kamar jira takeyi da sauri tace "Ni ice cream zansha", baki ya bude yace "kina ma da hankali kuwa, ina tambayanki mey zakici kina ce min ice cream, I will slap you right away in baki bar wannan shirmen naki kin fad'amin abinda zakici ba, duk yau mey kikaci da zakice min wani ice cream zakisha, you were sleeping all day kamar wata jaririya", tutturashi ta shiga yi daga jikinta tana murgud'a baki tace "Ni dama bance dole sai ka samomin ba ai, kuma ma ni da kaina zan iya zuwa inyi, bana ma so na fasa, ko ka kawoma bazan sha ba, ka tafi min daga d'akina ni", ta d'an ja tsaki tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya kai minti biyu zaune yana kallonta da mamaki, can dai ya mik'e daga karshe ya nufi kofar d'akin, jin motsin kofa ta juyo da sauri tace "ice cream d'in zakaje kawo min?", wani irin kallo ya watsa mata, bata damu da kallon da yakeyi mata ba tace "Ni kar kaje Cold stone fa, ko na lick ko scoop, ba na can nakeso ba, na gelatorino nakeso, sai flavour Kuma pistachio, strawberry, Madagascan vanilla, kuma banason na corn, su min scooping a cup, yawwa with a couple of some more exotic options kamar su coconut lemon grass, pepper mi.....", bai jira ta gama surutun nata ba ya kad'a kai ya fice ya rufo k'ofan, baya ya jefa key d'in aljihunsa, gaba d'aya ya kasa gane what came over this girl, mota ya shiga sannan ya kunna map navigator yayi searching wajen da ta fad'a mishin, dan shi baisan ma inda gun yake ba, tafiyan 15mins ya isa wajen, duk abubuwan da ta lissafo mishi sai da ya siya harda k'ari, da snacks, bai jima ya dawo gidan, har lokacin bai ga Ajiddeh ba, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye da ledojin hannunshi, tana jin motsinshi ta mik'e da sauri, daga bakin gado ya zauna ya mik'o mata ledan hannunshi, da sauri ta anshe, na snacks d'in ta fara ansa, rai b'ace ganin abinda ke ciki tace "nifa ba abinda nace inaso ba kenan", ta tura mishi gabanshi, jin d'ayan ledan da sanyi yasa tayi hanzarin jawoshi ta shiga bubbud'ewa, ba tareda b'ata lokaci ba ta shiga shan ice cream d'in, kallonta kawai yakeyi ganin yanda takesha d'agowa tayi suka had'a ido, murmushi ta mishi tace "Thank you, you can have some", tayi mishi nuni da ledan dake ajiye, kai kawai ya iya girgiza mata, tab'e baki tayi taci gaba da shan abinta, ko rabin na cup d'in batasha ba ta ajiye tace "Alhamdulillah, am full", ta ajiye zata juya ta kwanta yayi maza ya rik'ota yace "meye hakan?, wai kina nufin har kin gama sha? kai ta gyad'a mishi tareda d'age mishi girarta d'aya tace "Ehh", yace "abincin kuma fa?", d'an had'e rai tayi jin ya ambaci abinci tace "Nifa bana jin yunwa, am okay", ya d'an yu shiru sannan yace "toh brush d'in kuma fa da kike k'ok'arin kwanciya, and baki yi sallah ba, tace "nifa bacci nakeji, xan yi anjima wllh", "Bacci?", ya tambayeta dan yau wuni yaga tayi tana bacci kuma its just 8:08 yanxu, bata bashi amsa ba ta kwanta abinta, tana kwanciya kuwa bacci ya d'auketa, ya dad'e zaune yana kallonta daga baya ya tashi ya ciro mata kayan baccinta cikin closet ya cire mata na jikinta ya saka mata wanda ya ciro?, mamakin irin baccin nata kawai ya dinga yi dan har ya canja mata kayan bata tashi ba ita da bata da nauyin bacci,  addu'ar bacci ya tofa daga baya ya kashe mata wutan ya tafi d'akin da ya kwana jiya, wanka yayi sannan ya d'auro alwala yayi sllhn Isha ya koma gado, kamar jiya yau ma a waya ya dudduba ayyukan office da baiyi ba snn ya kwanta, sai wajen sha biyu snn Ajiddeh ta shigo  d'akin, yana jinta sai wani shige mishi jiki takeyi, ganin yayi bacci ta k'yaleshi  itama ta kwanta.



Washe gari da asuba bayan yayi Sallah direct airport ya wuce d'aukan Farida, arrivals ya wuce kai tsaye bayan ya gama parking, dai dai lokacin da Farida ta fito daga terminal janye da akwatinta, ita ta fara hangoshi, da gudu ta k'araso ta rungumeshi, shima d'in rungumeta yayi, cike da farin cikin ganinsa tace "Yaa Abu ina kwana, thought tare xa ku xo da Anty Batuul" da xolaya ta kare maganan da wide smile d'inta mai kyau shimfid'e fuskarta, murmushin shima yayi yace "Lafiya Alhamdulillah, Ya hanya?", zumb'uro mishi baki tayi jin yace ya hanya tace "hmmmm ai ni shiyasa bana son bin wani flight inba B.A ba ko Emirates, kasan transit kawai muka tsaya amma suka fake da wani wai bad weather, baza mu taso ba sai bayan nan da 14hrs , ni ai da so nayi in koma Nigeria, amma sabida ina son ganin my other half", ta wani lumshe ido tana d'aura duka hannayenta biyu a k'irji tace "Allah dan ita kad'ai na yadda na k'araso, kuma kasan wani abu......", bai barta ta k'arasa ba yace "Let's get going, d'an wannan surutun naki zamu kwana nan baki gama ba", suna tafiya yake tambayanta Yasu Ammah da kowa a gida, kamar jira takeyi ta dinga mishi zuba, wasu abubuwanma ba ji yakeyi ba har suka isa inda yayi parking mota, butt ya bud'e mata ta saka jakarta a ciki, sannan ta xagayo ta zauna, sai da ya tada motar suna tafiya sannan ya juyo ya dubeta yace "kina jina?", gaba d'aya hankalinta ta tattaro ta kalleshi jin yana mata magana, yaci gaba da cewa "Babu ruwanki da duk wani abu da zaki gani in mun je, Ajiddeh isn't aware Batuul is my wife", a firgice ta kalleshi tace "What?", kallonta yayi ya wani hade rai yace "Yeah you heard me right, dan haka babu ruwanki da duk abinda ke faruwa cikin gidan, am repeating it, don't try anything stupid like you did last time, babu ruwanki da Ajiddeh", tabe baki tayi ta kauda kai, yace " Baki da hankali ina mako magana kina dauke min kai" xumburo baki tayi ta gyad'a mishi kai alamar ta ji, ya hade rai sosai yace "bakida bakine?", ta dan murguda baki tace "Toh naji mana", kwafa yayi ya ci gaba da driving dinsa, ta d'auke kai ta juya tana kallon window, ranta ne taji ya baci ba k'adan ba wai Ajiddeh batasan Batuul matarsa bace, toh does that mean they weren't intimate ko me, shine har Ammah ta fara lissafin jikoki, "Chabdi" ta fad'a a ranta ba tare da tasan ya fito fili ba, juyowa yayi yana kallonta yace "kikace meye?", maza tayi ta kad'a mishi kai tace "No ni bance komai ba", ya harareta ya maida hankalinsa kan driving din da yake,farida taci gaba da sak'e sak'enta, a ranta tace masifaffe wai wani I shouldn't try anything stupid, tabdi ai kuwa wlhy sai dai in wannan matar tasa mai kama da bishiyar gwanda sai tsawo babu shape tayi hankali itama, dan indai ta tab'ani ba yadda za ayi in k'yaleta wlhy sai na rama, kuma sai nasan ynda nayi tasan wacece Batuul, "kutt, ai wlhy bama zai yiwu ba", batasan a fili  tayi maganar ba saida taga yayi parking yana mata wani irin kallo yace "meye d'in ne bazai yiwu ba?", da sauri ta shiga girgiza mishi kai a rikice tace "I wasn't talking to you fa", ya jima yana kallonta fuskarsa daure kafin yayi k'wafa ya ci gaba da driving, bata kuma gigin wani tunanin ba bare har ya fito fili, kamin su isa har gari ya washe, bayan yayi parking kamin ta fito in a serious tone yace mata "hope you heard all I said clear?", kai kawai take girgiza mishi dan ita ta matsu taga Batuul, yana bud'ewa ta fita guje ta shige gidan, tun daga bakin k'ofa ta fara ihun "His beloved, His First Lady, kina ina na iso", A guje Batuul dake kitchen ta d'an samu karfi tana gyare gyaren kitchen din ta fito jin muryar Farida, Ajiddeh da Aunty dake d'aki ma fitowa sukayi lokaci d'aya ganin wake ihun, Abu kam mamakin Farida ne ya cikashi jin abinda take fad'i, ya k'asa karasawa parlorn, ita ko ta tafi da gudu suka rungume juna da Batuul cike da murnan ganin juna, farida ta tura Batuul daga jikinta tana kare mata kallo ta wara ido har da d'an tsallanta tace "Waoww waow, yayana ya iya kiwo wllh, kinga yanda kika yi wani fresh kika yi kyau kuwa love, OMG" wani tsawa da ya rikita ta daga ita har Batuul din Abuturrab ya daka mata.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now