💖💝BATUUL 51💖💝

8.1K 416 1
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



       A dinning d'in ta ganshi zaune yayi serving kanshi breakfast din da ta yi yana ci, Ajiddeh na daga gefenshi tana ta kumbure kumbure, tana ganin Batuul ta watso mata wani mugun harara, ko kallonta Batuul batayi ba ta karaso cikin falon ba tare da tace musu komai ba ta wuce, har ta kai bakin kofa idon shi na akanta, sai da yaga fitanta snn ya maido da hankalinshi kan Ajiddeh da ta zuba mishi ido rai a b'ace tana kallon yadda yake kallon Batuul,  yasan driver bazai tafi ba sai ya jirashi ya fito dan yana son bata wayanshi in ta tashi a k'ira a d'auketa kuma ya bata kud'i, yi yayi kamar bai San kallon da take mishi ba yace "so you ain't eating har yanzu,  kilan zaki dafa ne ko kuma sai na tafi zaki faraci ta shigo ta ganki kinaci kije kina amai koh", ya karashe maganan yana murmushi, sake hade rai tayi tace "kaga nifa wulakancinka ne banaso Aliyu, koh jiya a gabanta ka dinga min dariya, ko ta rainani ai kai ka jamin, bare ma bata isa tayi hkn a gidana ba", bai ce mata komai ba yaci gaba da cin abincinsa yana murmushi, sai had'iyar miyau take tana kallon yadda yake cin abincin, duk yadda akayi abincin nada dadi ganin yadda yake ci sannan ga k'anshi duk ya gama bad'e ta a gun, kallonshi tayi rai a b'ace tace "magana fa nayi maka amma kaqi kulani sai tunkud'a abinci kakeyi kamar wanda bai tab'a ci ba", kallonta yayi da idanunwanshi dake piercing zuciyarta yace "ko kin taba dafa irin wannan ne a gidannan da kike cewa inaci kamar ban tab'a ba", baki ta turo tace "nifa duk ba wannan ba, ai abinci ga ka gashi, baby ni abinda na tambaya tun jiya, I urgently need it, gashi har ka shirya bakace komai ba fa", cike da shagwaba ta kare maganar, shi kam har ta gama maganan bai ce mata komai ba, da alama santin chips d'in Batuul yasashi kasa magana, ran Ajiddeh ne ya fara b'aci, tashi tayi a fusace zata tafi ya riko hannunta da sauri, ya dawo da ita ya zaunar kan dinning chair din, kallonta yayi da murmushi a fuskanshi yace "keh bakisan in mutum na cin abinci bai son damuwa ba, da kinci abincin kema nasan all your worries will b cleared away" wani irin kallo ta mishi yace mata "tunda bakici je d'auko min cheque d'ina a sama", da murna ta mike ta haura sama, bata jima ba ta sauko rike da cheque book dinshi a hannunta, har saida ya gama cin abincin tukunna ya janyo ya rubuta mata amount din da take bukata, murna ta dinga yi kamar mey, har bakin kofa ta rakoshi tareda yi mishi peck a kumatu sannan yayi mata sallama ya tafi.



        Inda Batuul taga driver na tsaye nan ta nufa, da kanshi yazo ya bud'e mata k'ofa tareda ce mata "Morning Ma'am" kai ta gyad'a mishi ta shiga ta zauna ba tareda ta iya ce mishi komai ba, ganin bai tada motar ba yasa tace mishi "am getting late, let's get going" babu musu ya tada ya d'au hanya, har suka isa school ranta b'ace yake, tasan ta riga da tayi missing first lecture, har gaban department dinsu ya kaita, kamin ya fito ya bude mata kofa ta bude ta fito, wucewa tayi lecture hall ta tadda ana lecture , shiga tayi ta zauna ba tareda ta cewa Kowa komai ba, Aisha dake gaba sai kallonta takeyi haka ma Samantha, sai da ta zauna tukunna suka juyo suka ci gaba da sauraren lecturer, batafi 45mins da shiga ba lecturer ya gama ya fita, a tare Samantha da Aisha suka yo wajenta, Aisha ce ta fara ce mata "don't tell me har kin fara latti daga farawa", kamin tayi magana Samantha ta karb'e da cewa "Hey love you were late today, and you missed almost two lectures today, you okay?" , hawayen da take ta kokarin maidawa ne ya shiga zubomata, a tsorace su Samantha ke kallonta ganin yadda take hawaye, janyota Aisha tayi ta rungume, Samantha ce tayi mata alama da ta jata suyi waje, sai da sukaje inda babu mutane tukunna suka zaunar da ita, kuka sosai ta shiga, babu abunda sukeyi sai rarrashinta, har suka gaji suka rabu da ita, sai da tayi mai isarta tukunna tayi shiru dan kanta, hawayenta tashiga gogewa da hannu sannan ta dubesu tace "what were we thought, I mean d topic", Aisha dan haushi ko kallonta batayi ba, Samantha ce tana kallonta tace "It seems you are hungry, let's go and get something to eat, am also famished" kallon Aisha tayi taga ta had'e rai, jiki a sanyaye tace "Aisha cikina ke ciwo", cikin sanyi Aisha tace "toh Fatima koh baki d'aukemu komai ba ai kinsan bazamu cutar dake ba, ciwon ciki dai ko clinic ai sai muje a baki magani, amma kinzo late we were worried sannan kuma kiyita kuka kiki bamu ansa", Samantha dai baki ta bud'e tana kallonsu, sai da taji sunyi shiru sannan ta dubi Aisha tace "She said what, what's d problem?", a takaice Aisha tace "stomach ache", ido Samantha ta xaro tace "then?, we should be in the clinic, let's rush her", kai Batuul dake zaune ta girgiza tana kallon yadda Samantha ta rud'e tace "I will b fine dear, you shouldn't worry, it usually does, I will take my medication when am back home", da rashin gamsuwan abinda ta fad'a musu Aisha ta girgiza kai tace "Fatima bafa cutar dake zamuyi ba, nanfa kika zauna kina kuka amma kice wani wai you are okay, how does that even makes sense", ta k'arashe maganan ranta b'ace, a hankali Batuul ta kamo hannunta ta zaunar gefenta tace "dagaske nake ya daina, kinga Kuma inada magani na a gida, ba lallai school clinic suyi min prescribing irinshi ba" sai yanxu Aisha ta yadda ta fad'awa Samantha yadda sukayi, littafin dake hannun Samantha Batuul ta ansa tana Kallo tace "Did I miss so much", Kai Samantha ta girgiza tace "you got no worry, I will explain everything", giranta d'aya Batuul ta d'aga, Samantha na kallonta ta fashe da dariya tace "yeah you gat my back" tanayi tana kad'a kai, dariya su dukan suka sa, Samantha tace " SHIT!,But girl you scared me, you shouldn't cry again when am there, I have this terrible phobia of tear, it doesn't even have a name", dariya ta basu, Batuul tace, "not in my weirdest dream, its not happening again I promise" ta k'arashe maganan tareda mik'ewa dan taga duk jikinsu yayi sanyi, sai da ta mik'e ta fara tafiya tukunna ta juyo ta dubesu tace "who is joining me for a cup of frapuccino", a tare suka mik'e suka biyota, suna isa wajen taji cikinta ya k'ulle, a hankali ta fara d'aga k'afarta ba tare da ta bari sun gane, har suka samu waje  suka zauna cikin bai barta ba, k'aryan da tayiwa su Aisha ne ya dawo mata, dama ance babu kyau k'aryan ciwo, d'an k'aramin tsaki taja dan tasan period d'inta can come anytime tunda har cikinta ya fara ciwo, waiter dake aiki a wajen ne ya iso wajensu, ya tambayasu abunda xa a kawo musu, Samantha tace "Serve me caramel", juyawa yayi ya kalli Aisha yace "Ma'am what would you like to have?" , kallonshi tayi tace "Hazel nut sugar free and and chicken lasagne", daga haka ya juya yana kallon Batuul da taketa tunani hankalinta ma baya wajen, sai da Aisha ta d'an tab'ota tukunna ta d'ago tana kallonsu, tambayanta yayi itama me take so, tunda har cikinta ya fara ciwo in tasha abu mai zak'i wahala ne zai k'aru mata gashi batada magani, ita pad d'inma bata dashi, tunanin hakan yasa ta hawaye da tayi k'ok'arin maidawa, jiki a sanyaye tace mishi "peppermint sugar free", da haka ya tafi yaje kawo musu, baifi minti biyar da tafia ba ya dawo riqe da tray, ajiyewa kowa abinda yayi ordering yayi sannan ya bar wajen, sai da suka kusa gamawa kanta a k'asa taji anyi musu sallama, bata d'ago ta Kali mai sallaman ba amma tasan namiji from his voice, kujeran dake gefenta taga yaja ya zauna, ji tayi yana cewa "This isn't fair, you girls enjoying without an invitation?", Samantha ce tace "Hey lemme order one for you, ta juya zata k'ira waiter, hannu ya d'aga mata alamar surrender yace "Hey No Thank you, am okay", kallonshi Aisha tayi da mamaki ganin baya tab'a kula matan dake binshi ma amma yanzu shi da kanshi yake zuwa inda suke, a hankali Aisha tace "You sure?", kai ya gyad'a mata tareda da yi mata murmushin shi mai kyau, kallon Batuul yayi yace "Sai dai in wannan da bata magana xata bani nata, I will gladly take it", Batuul batasan ma sunayi ba dan hankalinta ma baya kansu, kud'in frapuccino da zata biya ma bata dashi a yanzu haka da take zaune, tunaninta sam bai kawo bata da kud'i ba har sai da ta tuna ba da jakan jiya ta fito ba kuma yau bai bata kud'i ba, d'an tab'a table d'in yayi yace "y'ar uwa tunanin mey kikeyi, you are too young for that", sai a lokacin ta d'ago ta kalleshi da murmushinshi mai kyau a fuskanshi, ajiyar zuciya tayi tace "Ba tunani nakeyi ba", tsareta yayi da ido yace "okay tell me what we just said", shiru tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi yace "you see you can't say, ki dena its not good for you at such a tender age", batace mishi komai ba itadai, dan tama manta da sunanshi ko jiya da ya fad'a musu, alama yayiwa waiter yaxo, ce mishi yayi ya bashi bill d'insu, shi ya biya musu duka kud'in abunda sukaci, duk da suna ya bari bai sauraresu ba, Samantha ce ta mik'e tace "okay Mr Shaheed, we got class now, hope to see you ltr, and thank you for all" murmushi yayi mata kawai yana kallon Batuul dake Zaune, ciwon cikinta na dad'a k'aruwa, a hankali ta mik'e tana kallonshi taga shima ita yake kallo suka had'a ido, maza tayi ta d'auke idonta tace mishi "mun gode" murmushin sa na nan fuskanshi har lkcn yace "its okay", daga haka suka mishi Sallama suka wuce, bayansu yabi da kallo har sai da ya dena kallonsu ya juya tareda murmushi, suna tafiya Samantha tace "He is such a gentle man, am already crushing babes", Aisha kawai ta biye mata Batuul kam shiru tayi tana jin abinda ke damunta har suka isa class



    
       Abuturrab na fitowa ya shiga  Duddubawa ko zai ga motar driver amma wayam, da mamaki ya ciro waya ya k'irashi, yana d'agawa yace "I didn't say you should leave, where are you guys", a daburce driver yace "Sir Ma'am insisted we should leave, and am by d office now, av already dropped her", rai a b'ace ya katse k'iran ba tare da ya jira driver ya k'arasa magana ba, he wanted giving her money, kuma inma ta gama lecture ya za ayi tasan anzo d'aukanta, d'an tsaki yaja ya fad'a motarsa, awa biyu sukayi suka fito daga class d'in, gumi sosai takeyi tsabar azaban ciwo amma ta daure dan bataso su Aisha su sani, Aisha ce ta fara yi musu sallama ta wuce yau da yayarta zasu tafi, bayan minti kamar Sha biyar Samantha ma ta wuce, sai lokacin tayi tunanin bata fad'awa driver ya dawo lokacin ya d'auketa ba ya fad'o mata, waje ta nema ta zauna ta kifa kanta kan gwiwa ta fashe da kuka, sunan Aunty kawai take k'ira, ita Yanzu ya zatayi ga ciwon ciki da zai hanata takawa ta tafi da k'afa tunda ba nisa sosai, gashi bata da kud'i bare tayi karambanin hawa Bus ko Taxi tunda ba lallai ma ta gane ba, kuma batada number Yaa Abu bare ta k'irashi tace ta gama lectures azo a d'auketa, to in ma tana da shi iya kiransa xata yi, kuka sosai takeyi kamar wacce ake zanewa, tafi awa d'aya zaune a wajen, kamar daga sama taga mota yaja ya tsaya gabanta, a hankali ta d'ago rinannun idanuwanta dai dai lokacin da ya fito daga motan, tsayawa yyi ya hade rae yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mike a hnkli tana jan kafa ta xaga xuwa seat din gaba, tana shiga motar shi ma ya shiga ya rufe, ya juya yana kallonta fuskarsa daure sae dae fa har da borin kunyan daxu da safe yace "How dare yhu xan ba driver na order ki sa ya ketare? Kin yi employing driver ne garin nn?" D'ago kai tayi tana kallonsa, sae a snn ya lura da idonta da yyi ja, kana ganinta kasan kuka tayi, d'an kyabe baki yyi ya tada motar ya ja ya nufi gida, jinginar da kanta tayi jikin kujeran motar ta lumshe ido tana jin ynda ciwon cikinta ke karuwa ba kadan ba, yana gama parking a garage ya bude motar ya fita ba tare da ya bi ta kanta ba, da kyar ta bude motar ta fito, bata jira ya kulle motar ba ta nufi cikin gida, bin ta yyi da kallo yana mamakin halinta, komai kuka kmr wata 'yar goye, tsaki yyi ya rufe motar ya nufi cikin gidan shi ma. Bbu kowa falon Batuul ta haura sama da sauri ta shige dakinta ta sa key ta fada kan gado ta cusa kanta cikin pillow ta dinga rusa kuka kamar ranta zae fita, juye juye ta shiga yi ta sauko k'asa ganin kwanciyar ma ya gagareta, kan kace me duk ta fita hayyacinta.   Abuturrab kam bedroom dinsa ya shiga, ya nufi toilet yyi wanka, xaune ya samu Ajiddeh dakin da ya fito, ta mike tace "Babe wllh na mance ban gaya maka ba, lotions dina sun kare, gashi akwae wani turare don nake son siya, xan kuma sake kayan make up" wani kallo ya shiga mata yace "Wae ke wace irin mace ce Ajiddeh, how on earth mijin ki xae dawo daga aiki bbu sannu da xuwa, baki bari ya huta ba, baki kawo masa ko ruwa ba ki xo kina masa lissafe lissafen banxa, to bani da kudin siyan komae ynxu" sakin baki Ajiddeh tayi tana kallonsa, sae kuma ta ja tsaki tana hararansa cike da fitina tace "Toh idan ban maka lissafe lissafe ba Aliyu wa xan ma, ko ina da su xan xo ince maka bbu, ubana xan kira ince yyi min bayan kana da halin min" kayansa ya sa ya fice daga dakin ya bar ta nan tsaye, downstairs ya sauka ya kwanta dogon kujera ya lumshe ido, to ita kuma wancan kukan me take a sch, tsaki yyi ya mike xaune ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam kawae wahala aka hadasa da, mikewa yyi ya koma sama ya nufi dakin Batuul, kwance ya sameta kasan dakin tana juye juye tana kuka, tsayawa kallonta yyi da mamaki, shi dae ya shiga uku, karasawa dakin yyi ya durkusa gabanta ya dagota yana kallonta yace "Wae ke kina da hankali kuwa?" Kuka take tana yarfe hannu tana neman kwace kanta daga rikon da yyi mata, jawota yyi jikinsa don xuwa ynxu ta d'aga masa hankali yace "Wae wats wrong with yhu, me ya faru ki gaya min? Talk to me plss, What happen" rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka, ya dago kanta yana kallonta yace "Fateema!" Da kyar tace "Cikina ke man ciwo" yace "Ciki kuma? What did yhu eat at sch" girgixa masa kai tayi ta runtse ido tace "Nothing!" Sae kuma ta fashe da kuka, duk ta rikitasa yace "Wait yana maki haka a gida ne, wani irin magani ake siya maki?" Boye fuskarta tayi jikinsa taki cewa komae sae kuka don ita kadae tasan axaban da take ji, murda kofar dakin aka yi, ae da sauri ya turata ya mike ya koma baya, Ajiddeh ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskar nan nata daure tana kallonsu, kame kame ya shiga yi yace "Kinga babe wae cikinta ke ciwo kuma taki fadin cause din, nd nd... Wat are we going to do to her then, ko mu tafi clinic?" Ajiddeh ta yatsine fuska tace "Cikinta ke ciwo ko kuma tana Al'ada?" Kallon Ajiddeh ya tsaya yi kafin ya juya ya kalli Batuul da tayi k'asa da kai tana hawaye, Ajiddeh ta watsa mata harara tace "Ko ba jini bane?" Ae Batuul k'asa dagowa tayi, Ajiddeh ta ja tsaki ta fice daga dakin, kallonta Abuturrab ya tsaya yi, ta ki bari su hada ido.


💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now