💖💝BATUUL 14💖💝

6K 378 2
                                    

         


        Dedicated to KHALEESAT HAYDAR


  

             Shiru hall d'in yayi ana sauraron speech d'in da VP keyi, da ta gama ne sauran members d'in high table suma suka karb'i mic suna yiwa graduants d'in Nasiha da tunatarwa rayuwansu da kuma wanda zasu fara a gaba (university), sai da aka gama speech aka fara k'iran graduants d'in d'aya bayan d'aya su karb'i Certificate da Testimonials d'insu, Batuul ce number Twelve cikin wad'anda ake k'ira, Hall d'in ne ya cika da ihu bayan Batuul ta mik'e, Juniors d'inta sai hailing d'inta suke, malamanta da sauran mutane na tafa mata, she have been their most outstanding student, kind, generous, neat and obedient, Ihun da aka sane yasa Abutturab mamaki, surnames d'in da yaji an ambata are familiar, not even familiar ya san sunan sosai, tab'e baki yaci gaba da abinda yakeyi, a hankali ta sauk'a daga kan kujeranta ta k'arasa a nutse inda vice president yake, da hannunshi ya mik'o mata certificate d'inta, a hankali tace mishi "Thank you", tare da d'an duk'awa sannan ta ansa akayi musu hotuna dashi tukunna ta koma inda sauran ke tsaye itama tabi layinsu ta tsaya, har saida aka k'ira 67 students sannan akayi musu standing ovation tareda tafa musu, a kan stage ďin kowannensu ya cire graduation cap ďinshi suka sa ihu sannan suka watsa su tare da faďin " Mommah we made it", a hankali Batuul tace "Alhamdulillah", hawaye murna taf idonta, kowa kujeranshi ya koma bayan ovation ďin da akayi musu, lokacin ne aka fara presenting prizes, Best in further Physics goes to Affan Abba gana, tafi aka sa mishi, bai dawo ya zauna ba ya sakeji ance shine best in TD, haka ya sake karb'an building and construction sai chemistry, Farida Ahmad Kyari aka k'ira best in Mathematics da Further Maths, sai Hamra Imam Imam best in biology, Maryam Ibrahim Tsoho best in Agric, Abdul Azeez Abidemi ne best in Accounting and commerce, Sai da aka gama k'iran sunayensu aka ce best in Economics goes to Fatima Kashim Goni, tashi tayi taje ta karb'a da smile a fuskanta, bata k'arasa wajen zamanta ba aka sake cewa itace best in IRS, Government,Geography, English sai Arabic , marketing da Food and Nutrition, tasowa akayi ana tayata kwasan prizes d'in dan baza ta iya ďauka ba duka sunyi yawa, haka aka ci gaba da bata prizes har na neatest, punctual da most obedient, Dj ne ya kunna mata wakan stand up for the champion dan tafi k'owa karb'an prizes a wajen, Abutturab na daga zaune tunani ya fara wacece Fatiman nan, koma wacece Masha Allah tayi k'ok'ari, sai da ya sake ambaton sunan ne ya tuna da Kashim Goni ai Minister ne, lokacin ya tuna da ai Batuul ce, kwata kwata bai ganeta ba dan wani kyau tayi da tsawo saboda heel ďin dake k'afanta, Sadiq dake zaune gefenshine ya tab'a shi yace "Yaa Abu yarinyar nan is a Genius, ga wani kyau da tayi bari mu fita sai na tambayeta yadda akayi tayi tsawo" ya faďa yana dariya, Abutturab bai kulashi ba illa wayarshi da ya ci gaba da dannawa, haka aka ci gaba da occasion d'in daga k'arshe aka rufe da addu'a, tun suna ciki suka fara selfie har suka fito waje, Kowa wajen family members ďinshi ya wuce, Baba Batuul ta fara rungumewa shi kuma yace mata "Mamana Allah yasa Albarka, Allah ya taimaka yasa kufi haka", daďi ya sata cewa Amin da sauri, wajen Aunty ta koma, da murmushin murna a fuskanta ta shafa kan Batuul tace "Sannu Batuul, Allah yayi miki albarka, Allah yasa afi haka", Hotuna sukayi tayi dama sunxo da photographers ďinsu , duk y'an gidan sai da tabisu sukayi hotuna ďaya bayan ďaya sannan sukayi na Family, Affan ma sai da yazo dasu Maa sukayi hotuna, Farida ce tazo a guje tana k'iran sunan Batuul, ganin su Aunty yasa ta gaishesu, sukayi congratulating ďinta, cewa Batuul tayi "kixo Ammah nata jiranki tun ďazu muyi pictures, taqi ayi wai sai kinxo, a jiraki wait", murmushi Batuul tayi tace "toh muje nima yanxu nake tunanin zuwa" , tacewa Aunty zataje ta dawo, Aunty ce tace suma gasu nan zuwa wajen su Ammah ďin bari su gama gaisawa da mutane, suna juyawa zasu tafi ta rik'e hannun Farida da k'arfi, kallonta Farida tayi tace "lafiya?",  "I dont know y, but these days i use to feel restless kuma heart beat ďina na increasing", Farida da damuwa a fuskanta tace "Dont worry kiyi addu'a, we will talk about it later, let's move now", k'arasawa wajen su Ammah sukayi, y'an gidansu Farida ne a wajen duk tasansu sai wata farar yarinya daga gefen Abu, sai wani da bata sani ba, bata kalli gefen da Abu yake ba ta je wajen Ammah ta rungemta,janyeta Ammah tayi tareda da d'ago kanta ta dubeta tace "useki Bitti, Masha Allah, Allah bariki", murmushi tayi ta tace "Amin Ammah", juya wajen Abui tayi shima ya shafa kanta yayi mata addu'a, Juyawa tayi ta dubi Sadiq da Massa da suke a tare tace Yaa Sadiq "ina wuni", smirking yayi yace "Batuul wannan tsayi da kika k'ara ai har nima kin fini, ban ma ganeki ba, ni kai har yanxu banma yadda ke bace", da murmushinta mai kyau tace "Yaa Sadiq u are just too much, kome na saka ai bazan fika tsayi ba", yace mata "gashinan kin kamo hanya", dariya tasa sannan yace mata "congrats Batuul, we are proud of you, keep it up", murmushi tasa sannan tace "Thank you Yaa Sadiq", mutumin dake tsaye da Sadiq tacewa "ina wuni", da murmushi yace "Lafiya kalau, congratulations, kinyi k'ok'ari sosai, Allah ya bada sa'a", duk da bata san ko waye shima amma addu'an da yayi mata yasa ya burgeta, da murmushi tace "Nagode In sha Allah", Abutturab na daga gefe shida Ajiddeh sai zuba take mishi, Ammah ce tace bakayi congratulating Batuul ba, Idonshi ya sauk'e k'asa yace "ai mun haďu nayi congratulating ďinta" dan shi har yanxu ya kasa yadda Batuul ce, da mamaki Batuul ta ďago ta dubeshi duk da yadda zuciyanta ke bugawa dan tasan bai yi congratulating ďinta ba amma yacewa Ammah wai yayi, tana ďaga kanta suka haďa ido, sauri tayi ta ďauke nata dan brown hazel eyes ďinshi na sata taji wani iri, matar dake gefenshi fara siririya tacewa "ina wuni", kamar baza ta amsa ba har saida suka haďa ido da Ammah ne tace "lafiya" a dak'ile, duk da bata san Batuul ba, bata tab'a ganinta ba amma sai da taji bata sonta, Ammah ce tace "toh tunda kun gaisa sai ayi pictures", photo grapher ne yazo ya fara arranging yadda zasu tsaya, da Batuul na daga gefen Abui ita da Farida, cewa Batuul yayi ta dawo gefen Abutturab, Ajiddeh kuma ta koma daga gefen su Sadiq, ba dan taso akayi wannan canjin ba haka ta koma daga gefen su Sadiq, itako Batuul kamar bata ji shiba ta tsaya a inda take har sai da ya sake cewa "young madam ki dawo nan", ya nuna mata gefen Abutturab, a hankali take tafiya har tazo inda yake nuna mata ďin , rigarta ta kama daga k'asa tana cikwikuyewa, tsayawa tayi amma gaba ďayanta ji take kamar a kan k'aya take tsaye, tsayawan da tayi gefenshi ne ya sashi jin wani iri, so yake a gama hoton nan gaba ďaya ya bar wajen dan gaba ďayanshi wani iri yakeji, sai da mai hoto yayi clicking wajen talatin sannan ya tsaya, Ammah ce tace Abutturab ya tsaya suyi daga shi sai Batuul, ďago kanta tayi ta dubeshi taga shima ita yake kallo, maza tayi ta ďauke kanta ta k'ara damke riganta da k'arfi har hannunta na gumi, hawaye ne ke shirin fitowa daga idonta dan gaba ďaya a tsorace take, tsayuwa sukayi dukkansu biyun dan babu yadda suka iya, mai hoton ne yace Abutturab ya ďan matsa kusa da Batuul, matsawa yayi dan so yake a gama wannan photo session ďin da Ammah ta sasu yi, tana ganin ya matso itama ta mata da baya, tsayawa yayi ranshi a b'ace yana kallonta, hannunta ya kama ya jawota har saida ta kusa faďawa jikinshi, ido ta wara ta bishi dashi taga bama ya kallonta, su Ammah ta juya ta gani taga hankalinsu ma baya kansu, wannan farar matar ce kawai taga ta k'ura musu ido tana kallonsu, da Batuul ta kalleta ne ta bita da harara, kanta ta ďauke daga duban matar ta tsaya har pg ya gama snapping ďinsu, yana gamawa su Aunty da Maa suka iso, bayan sun gaggaisa aka sake sabon photo session, Ajiddeh kam k'in shiga tayi wai flash ďin na reflecting idonta yana sa mata ciwon kai, suna gamawa Batuul da Farida sukace zasuje suyi pictures da friends ďinsu, Affan suka fara haďuwa da a garden ďin school ďin yana ganinsu ya cewa Batuul "Best friend i will miss, i dont know how i will start over without you, you have been there for me through good and bad times all these six years..." bai k'arasa maganan ba kukan da take ta mak'alewa tun safe ya fito, da gudu taje tayi mishi bear hug tace "Affan i will miss you more, how you always make me laugh, how you make me waffles every week end night, kuma har yanxu ban koya ba, Affan muje Uk tare kaji sai kaci gaba da koyamin,i will miss everything about you", tana buďe idonta dake rufe zata janye daga rik'on da yayi mata taga Abutturab a tsaye daga gefe ya zubo mata hazel like eyes ďinshi yana hararanta, kamar ma waya yakeyi amma ya kasa ci gaba da wayan sai tsayawa da yayi yana kallon inda suke, idonta ta ďauke taci gaba da magananta tace "zan faďawa Maa ma kar a kaika cyprus a bari muje Uk tare" Farida da ta tsaya daga gefe tana share hawaye dan sun bata tausayi duk da itama tana tausayin kanta na rabuwa da masoyinta amma tasan shak'uwan Affan da Batuul daban ne, ce musu tayi "you guyz there, kun tsaya kuna ta kuka and you are making me an emotional fool here, wont anyone give me a hug", hannayensu suka buďe mata taje itama ta rungumesu, Affan ne yayi k'arfin hali dan shima sun kusa sashi kukan yace musu "its okay, am always the man, just give a call and i will be there right away", murmushi sukayi a tare suka ce mishi "The man", haka sukaci gaba da hiransu sannan suka gyara fuskokinsu suka je inda sauran abokanensu suke sukayi hotuna,
K'arfe 1:30 kowa yayi shirin watsewa, Farida ce tacewa Batuul "muje gidanmu sai daga nan mu tafi prom ďin daga nan it will be easier ko", Shiru Batuul tayi sannan tace " okay muje mu faďawa su Aunty sai su turomin kayana gidanku", wajen Aunty Batuul taje ta faďa mata komai sannan tace "okay kuje sai Baa Liman yazo miki da kayanki", mota su Aunty suka shiga suka tafi , wajen dasu Ammah suke suka k'arasa taga su Ammah ma basa nan daga Abutturab sai wannan farar matar ta zauna daga gaban mota tana ta kumbure kumbure, hango su yayi yabi Farida da harara yace "ina kika tsaya inata k'iran wayanki bakya recieving", ce mishi tayi "Yaa Abu a silent wayan yake, banji bane" Batuul ce a ranta addu'a take Allah yasa ba dashi zasu tafi ba, da ta sani da kawai su Aunty tabi in yaso daga baya a kawota, da taga Farida ta buďe k'ofan baya ta shiga ne yasa itama ta buďe ta shiga, tana zama ďaga kan da zatayi suka haďa ido da Abutturab, harara ya sakar mata tayi saurin ďauke kanta sannan yaja mota suka fita daga wajen

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now