💖💝BATUUL 35💖💝

6.2K 313 0
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



      Aunty na fita ya jawo kujera ya zauna kusa da gadon yana kallonta, ita kam kanta a k'asa yake, dan ji tayi kamar ta bita su tafi, har ji take ďakin na suffocating ďinta, tabe baki yyi ya mik'e ya isa wajen da ya ajiye ledan da ya shigo da ya ďau wani bowl da Batuul ta wanke a hannu ciki da zata ci abinci ya zuba apple, grapes sai pomegranate a ciki ya bude table water dake wajen ya juye ciki ya nufi toilet, tana zaune ya fito ya zuba fruits din kan plate ya dawo ya zauna kan kujerar da ya tashi  ya fara b'are pomegranate yana shan abin shi, Batuul kam kin ďagowa tayi ta kalleshi bare tasan abinda yake, cikin nutsuwa ya shiga maimaita mata maganan ďazu ya kara da cewa "yhu beta pretend yhu are nt recovering, ki kuma gaya ma likita auren dole xa a maki, I bet he will find a solution" ko kadan Batuul bata san mey yake cewa ba dan ji tayi abincin da taci yana son dawo mata tsabar tashin xuciya, ranshi ne yayi mugun b'aci ganin ynda tayi banxa da shi tak'i cewa komai, a fusace ya tashi ranshi a haďe, cikin tsawa yace mata "keh kurma ce ina miki magana kin wani min shiru kina jina, are yhu stupid", ko ďagowa batayi ba bare ta nuna mishi tasan abinda yake faďi, ranshi ne ya daďa b'aci yace "Kehh!" k'ala bata ce mishi ba, jin amae na shirin taho mata yasa ta tuge drip ďin hannun ta ta yunk'ura xata sauka daga gadon yyi saurin rik'eta yana mata mugun kallo yace "ina zaki?", hawaye ne ya shiga zuba daga idonta tana girgiza mishi kai alaman ya saketa amma yaqi, sai ma daďa rik'eta da yayi da k'arfi don mamaki reaction din nata ya bashi to ko dae ba ita kadae take ba, bai ankara ba kawai yaji ta kwararo mishi amai a jiki.




     Aunty na komawa gida tasa aka kawo mata Aabid dake wajen Fa'izah ta bashi abinci, dan rabonta dashi tun jiya da Batuul ta zama unconscious, tana gama bashi ta mik'ashi ta shiga yin wanka, fitowanta kenan daga toilet taga Baba zaune akan gado, har ta ďan tsorata, ganin shine ta k'arasa fitowa daga toilet ďin, dubanshi tayi taga ita yake bi da ido, ce mishi kawai tayi "Uncle sannu da zuwa", snn tayi gaban mirror, kwaso mayukan da zata shafa tayi ta dawo bakin gadon itama ta zauna, Kallonta yayi yadda takeyin abu kamar bata san yana ďakin ba, hannunta ya rik'o tare da cewa "Maryam", bata ďago ta kalleshi ba tace "Na'am", yace "ya jikin Batuul ďin, waye a wajenta", k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata tayi a hankali tace "Abu na wajenta, wanka nazo inyi in kai mata kayan da zata canja itama", matsowa yayi kusa da Aunty ya jawota jikinshi, hawayen da take ta k'ok'arin maidawa ne ya shiga zubowa, kuka sosai ta shiga yi mishi, patting bayanta ya shiga yi , bai hanata ba har sai da ta ďan tsagaita dan kanta tukunna ya ďago tareda da k'iran sunanta, ajiyar zuciya tayi tace "ina jinka", yace "Maryam yanxu akan nace zanyi wa Batuul aure shine kika bi kika ďagawa kanki hankali?"  yayi tambayar yana kallonta, ganin tak'i magana sai hawayen dake zuba daga idanunta yasa yace "auren nan da zatayi kamata yayi kifi kowa murna, wannan yaron ďanki ne, kinfi kowa sanin waye shi, ke da kanki kinsan babu wanda Batuul zata aura hankalinmu ya kwanta da yafi Aliyu, da bakin ki kin yabi nutsuwarshi, toh sai yanxu dan zai auri y'arki shine kike qi, wani hali garesa da har baki son ba shi 'yar ki? Naga dae auren nan ko ba yanxu ba dole ta yishi, toh meye amfanin a barshi nan gaban bayan yin hakan shine gatan da zamu iya yi mata, kuma shine rufin asirinta da namu baki ďaya, inma karatunta kikeji, da kaina zan sa a nemo mata admission a can inda zatayi auren, babu abinda zai tauye mata karatun ta, kiyi hak'uri kiyi mata addu'a Allah ya bata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda zata tsinci kanta", jikinta ne yayi sanyi har yanxu hawayen na ci gaba da zubowa ta shiga gogewa cikin sheshek'a tace "Uncle Batuul k'arama ce fa, batasan meye aure ba bare abinda ke cikinshi, kuma fa mai mata zaku aura mata, abin ai zai yi mata yawa, kai da kanka kasan yadda Batuul ke da rauni, haka zataje a cutar da ita tunda ita ba wani wayo gareta ba", murmushi yayi tareda ďagota yace "yanxu naji dalilinki na k'in auren, bakiso y'arki ta auri mai mata saboda kema ke kaďaice gidanki ko, nima ďin ai zan k'ara", da sauri ta ďago tana kallonshi ya sake jawota jikinshi yana murmushi yace " Be optimistic Maryam, in kika nuna tsoron kishiya y'ar taki kuma tayi yaya, addu'a zakiyi musu Allah ya haďa kansu ya basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya bashi ikon rik'esu da amana, sannan Batuul fa University take, tana second year ďinta, kinga ba yarinya bace, she is matured enough, she can decide what is wrong and right, tasan abinda zai cutar da ita da wanda zai amfaneta, mubita da Addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi", ya faďa yana goge mata hawayenta, da haka Baba ya rarrashi Aunty har ta hak'ura da zancen auren, tace Allah sa hkn shine mafi alkhairi.



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now