💖💝BATUUL 83💖💝

8.8K 460 21
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





            Bayan Mum ta bar parlour rai b'ace ta fito ta dawo parking lot, da k'arfi ta shiga k'walawa driver k'ira, a guje ya taho yace "Hajiya gani", kallonshi Kawai tayi ya ciro makulli daga Aljihu ya bud'e motar ya fad'a, daga ganin yanayin yayar tata tasan ba lafiya ba, batace komai ba saida ta Shiga ta zauna tace "Yaa Zuwaira mey ya sameki naga kin canza daga shiga ki fito, wani abun ne  ya faru?", Mum taja wani dogon tsaki cike da masifa tace "Dan uwarka kai jahilin ina ne iyye?, ina zaka kaini da ka karyo kwanan nan", Driver da duk ya rikice yace "Hajiya ranki shi dad'e ca nake kasuwa za....", bai gama rufe baki ba a hasale tace "bukkar uwarka zaka kaini ba kasuwa ba, shasha Kuje zamu, jahili", shidai baice komai ba dan inda sabo ya saba indai ran Mum b'ace yake a rana toh sam bai son ya zama shike duty, jiki a sanyaye yace "Ayi min afuwa Hajiya, kuskure aka samu", daga haka ya d'auki hanyar Kuje, Jainaba da ta gama tabbatarwa babban abune ya tab'a Mummy ta tab'a baki tace "Wai Daddy ne ya bata miki rai", Mum tayi k'wafa tace "Abun nayi ne Jainaba, wato ina saka ban sani ba warwara nakeyi, bamuga ta zama ba, wannan karan da zafi zamu shigi kowa, da zafi zafi akan daki k'arfe, bazanyi sanya ba wannan karon, sai naci uban kowama, baza a d'aga min hankali ina zamana ba wlh sai nayiwa abun tufkar hanci", wayarta ta d'auko daga gefenta ta shiga dialling number tasa a kunne, har ya katse ba a d'aga ba, Jainaba taja d'an siririn tsaki tace "Yaa Zuwaira nifa bakice min komai ba har yanzu, mey ya faru kuma banda matsalar Ajiddeh", Mum ta sauk'e wani nannauyan ajiyar zuciya tace "Shifa wannan baban nasu ne ya sani gaba da surutunshi na banza da wofi, akan mene zai dameni nida rayuwata, kinji wai wa'azi ya zauna zai min wai ina abubuwan da basu dace ba", Jainaba tayi dariya tace "baki mik'a mishi microphone ba dan kifi jin wa'azin da kyau", Mum tace "birki na taka mishi, inji da abinda shashashar yarinyar ta Sani ko kuma in biye mishi ya dad'a bata min rai,  kuma fa duk sai nayi maganinsu, in banda taurin kanshi ma na jaraba duk  abinda akayi kwana biyu yake barin jikinshi amma dai wannan karon alwashi naci sai na samu komai yadda nakeso", Jainaba tace "Yaya wai ina laifin wannan karan ayimana yadda Daddy kullum komai nashi zai koma naki, a badda hankalinshi da tunani ya zama komai a hannunki", Mum tayi k'wafa tace "Dan ubanki wace makarantar nayi da zan iya riqe wadannan abubuwan, ai sai yanxu nake takaicin kin zuwa makarantar da nayi ina Karama, da yanzu komai nashi nasan takansu", Jainaba tace "Ai ba sai Lallai ke din ba, dama su Zee ne zasuyi ai", "kinga fa dad'a tunzurani kikeyi kina b'atan rai, wadanne yaran marasa wayo ne zasuyi min abin kirki, kiga kayan takaicin da Ajiddeh ke k'unsa min, itakuma Zainab in banda yawo kamar wata hadari a cikin gari babu abinda takeyi, kedai bari duk na kusa kawo k'arshen komai", Jainaba tace "Toh Allah yasa", Mum taci gaba da k'iran wayan Zee da har lokacin taqi d'auka, Driver dake gaba yana jin komai  Addu'a ya riqa Allah ya rabashi da masu irin halin Mum, kamar kullum yauma tafiya mai nisa sukayi kamin su isa gurin bokan nasu, da zuwansu Mum ta gama zayyane mishi duk abinda ke tafe dasu, k'asar dake gabanshi ya buga yace "itafa wannan yarinyar abinda muka tura Mata yana nan jikinta har yanzu kuma yana kan aiki saidai bansan mey ya hana aikin ci ta mutu ba, dan yaci ace ta mutu tun bayan kwana biyu", Mum tace "gaskiya ne yana aiki  dan y'ar tawa da nayi maka bayani tanason kawo mana matsala tace min mutuwa zatayi, in da yadda za ayi ranka shi dad'e ta mutu a huta, kaga in ta mutun, ta wajen nawa zata dawo hankalinta sai musan nayi akanta itama", haka dai Mum ta dinga Zayyanowa boka abinda za ayi tun daga kan Daddy, Ammah, Abu da kuma Batuul, boka yace indai jaka a bud'e take zasuga aiki da cikawa, nan ya duk'ufa ya fara da na Batuul, Suna zaune a wajen wayar Jainaba ta shiga ringing, saida aka kira wajen sau shida snn ta d'aga, shiru tayi tana sauraren mai magana a wayan, sai da yayi shiru tace "Toh naji", ta katse wayar, boka ya gama masu tsubbe tsubbensu yace "kuje, kamin ku k'arasa gida zaku ci karo da lbrn mutuwarta" da murna fal ransu suka zube mishi kudi suka tashi akan zasu dawo in da wata matsalar, sai da suka fita zasu gun mota Mum tace "Wane d'an iskan ne yake damunki a waya, yaga baki d'au na farko ba ai sai ya rabu dake koma wani jarababben ne", Ajiyar Zuciya Jainaba ta sauk'e ta tab'e baki tace "Idrees ne", Mum taja tsaki tace "Shifa wannan k'aramin mara kunya ne, ko ba d'azun nan ya k'iraki ba", Jainaba tace "Shine ya k'irani, wai tuna min zai sakeyi indai ban dawo gobe lallai lallai ba toh inyi zamana a inda nake ba sai na dawo ba", Mum taja tsaki tace "Karamin mara kunya, sai yazo ya kinkimeki ya maidaki", da haka har suka isa mota Driver ya tada sukayi gaba suna ci gaba da hiran abinda zai faru



      Aunty Amna dake tsaye tana magana ta hango Abu rik'e da Batuul suna sauk'owa downstairs, juyawa tayi ta dubi Ammah snn ta juya tayi stairs d'in, tana zuwa ta rungumo Batuul jikinta tace "Ayyyyy Batuul Habibty, bakiji dad'i ba ashe, Allahumma yashfiki, Allah yasa Kaffara ne Allah ya k'ara miki lafiya, baiwar Allah kina zamanki mutane na binki da sharri, kiyita Addu'a kinji, In sha Allahu duk wani mugun nufinsu akanki bazai tabbata ba da izini Allah", murmushi Batuul tayi tana tunanin maganganun da Aunty Amna ta gama fad'a mata yanzu, ita bata gane ma zancen mey takeyi ba", lumshe ido tayi ta bud'e snn tace "Namafa ji sauki Alhamdulillah Anty", Aunty Amna tace "Zaki warke kinji, Allah ya rabaki da sharrin masharranta", daidai nan Ajiddeh ta fito d'akin Abu zata sauk'o down stairs itama, jin maganan da Aunty Amna keyi yasa ta kasa d'aga k'afarta kuma, ta tsaya tana kallonsu, Aunty Amna ta dubi Abutturab da ya had'e rai tace "kai kuma yarinya batada lafiya kaje ka ajiyeta baka fadawa mutane ba", hannun Batuul ya janye ya dawo da ita gabanshi yace "Bata fa jin dad'i, she is weak", wara ido Aunty Amna tayi tace "Iyye, kaji mara kunya, da kasan she is weak ka barta tana shan wuya a can, kai a dole mai mata ko, ai sai ka kinkimeta tunda she is weak" sunkuyar da kai Batuul tayi dan kunya, kamar jira yakeyi ko sai gani sukayi yasa hannayenshi duka biyu zai d'auketa, wara ido Batuul tayi tareda matsawa baya tana girgiza mishi kai alamun kar ya mata haka, kamar bai gane mey take nufi ba ya sa hannu ya kamota zai d'agata taji kamar ana kulle mata ciki ta fasa wani razanannen k'ara da yafi na ko yaushe had'e ta rike cikin tana kiran Anty da kyar, lkci daya ta sulale yayi maza ya bita ya kamata a rikice yace "Ya salam, Not again baby, you will get well soon", Aunty Amna da ta tsaya kallon tsiyar Abutturab a tsorace da jin karan ta tsuguna itama ta kamo Batuul duk ta rud'e tace "Abu ciwon nata ne", kasa bata amsa yayi sai d'aukarta da yayi cak yayi k'asa da ita yana k'iran sunan Ammah, Ajiddeh da ke tsaye har lokacin tana kallonsu idonta ciccike da hawaye ta kasa d'aga k'afarta, ta rasa me ke mata dadi a duniylar, ganin yayi k'asa da Batuul ta fashe da kuka ta koma d'akin da take da sauri, a rikice Ammah ta fito tana tambayan mey ya faru, Farida da Sadiq dake side d'in Abui tare suka fito suna tambayan mey ya faru, Aunty Amna ma na tambayarshi ko ciwon nata amma ya kasa ce mata komai sai sunan Ammah da yake k'ira yana girgiza Batuul d'in ta tashi, Gaba daya duk sun rud'e kowa ya rasa abinda zaiyi ganin jikin Batuul d'in duk ya saki, Farida na kuka tace "Ammah ni kam nace ku kaita wajen Dr Zakaa zai  dubata ya fad'a mana abinda ke damunta," hawayen dake idonta ta goge tace "Sadiq Abui na Guest room tareda bak'onshi, kace ciwon nata ya dawo", a rud'e Sadiq d'in ya amsa ya fita amsa aiken da Ammah ta mishi, da k'yar Ammah tayi k'arfin hali ta kamo Abun dake riqe da Batuul ya kasa cewa komai tace "Babana kawota ka kwantar da ita, zataji sauk'i In sha Allah, yanzu za ayi mata magani", ta fad'a tana k'ok'arin karb'an Batuul daga hannunshi, girgiza kanshi yakeyi hawaye na gangarowa idonshi, zama yayi kan kujerar Batuul na  rungume jikinshi, gefenshi Ammah ta dawo ta zauna zatayi magana kenan Abui yayi sallama shida Ashiekh da Sadiq, Abui yace "Subhanallahi, jikin nata ne kenan", Abu bai iya cewa komai va don shi kadai yasan mey yakeji cikin ranshi, bayason kowa ya tab'ata sbd fargaban abinda za a ce mishi ya biyo baya, bayajin ko d'aya daga cikin nerves da pulses d'in jikinta na aiki, Ammah ce ta kawo hannunta ta rik'o na Batuul d'in, gabanta ne ya rik'a fad'i ganin hannun Batuul d'in ya saki, d'agowa tayi tana kallom Abu da idanunshi suka kad'a, lumshe ido yayi snn ya bud'e yace "Ammah babu abinda ya sameta ko?, I know she will be alright, nasani Fatima zakiji sauk'i i know you won't leave me just like that isn't it Batuul, you have to get up", Aunty Amna Abui ya kalla yayi mata alamun taja Farida da Ammah da ta matsa baya tana girgiza Kai, hakan ko tayi ta kama hannun Ammah tace "Ammah zataji sauk'i fa, ba dama haka yakeyi mata ba, yanzun nan zata farfad'o, muje muyi mata addu'an samun sauk'i", Itama Aunty Amna k'arfin hali kawai takeyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai hawaye da takeyi, Farida ce ta karb'e hannunta daga rik'on da Aunty Amna tayi mata ta dawo gaban Abu ta tsuguna dab fuskar Batuul d'in tana kallonsa hawaye na sakko mata tace "Yaaa Abu saida nace maka a kaita asibiti fa, don Allah mu tafi", ta kalli Abui dake tsaye ta mike ta isa kusa da shi cikin kuka tace "Abui don Allah nace mu kaita asibiti da yanzu ta warke, ka ganta yanxu kwance ko motsi batayi, Dan Allah muje a kaita", Hannu Abui ya d'aura kanta ya shafa snn yace "Babu abinda ya sameta kinji, zataji sauki" yacewa Sadiq " *Sadiq tai sha samiro Leno*, Sadiq kamata ka kaita sama", tana girgiza kai tana kuka haka Sadiq ya jata yayi sama da ita ya rage daga Abui sai Abu dake riqe da Batuul snn Asheikh, Asheik ya dubi Abui yace "Alanguro akwai Zamzam a kusa?" Abui yace "Ehh bari a d'auko",

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now