💖💝BATUUL 100💖💝

18.5K 695 155
                                    

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

"Daaaddddyyyyy, she let you take them?", yarinya k'arama y'ar shekara hud'u da ke zaune kan comfy bed ta baza colouring books d'inta kan bed d'in ta fad'a tareda mik'ewa tana wara ido, da ganinta kasan cike take da murna, dariya yayi ya zauna kan gadon shima yana zube mata chocolate packs da bottle of nutella d'in dake hannunshi, with excitement ta yarda crayon d'in dake hannuta ta hawo kan jikinshi ta zagaye duka hannayenta biyu wuyanshi biyu tace "Dad how did you get em?", ta fad'a tana kai hannu zata karb'i packet d'Raffaello packet d'aya, bud'ewa yayi ya mik'a mata, saida tayi pecking duka cheeks d'inshi biyu kamin ta jefa size bite d'in bakinta tana lumshe ido, kamin ta gama shanyewa ya bud'e mata nutella jar d'in tareda soka mata craft stick ciki, ido ta sake warawa tana lashe bakinta ta karb'i jar d'in daga hannunshi tace "Daaaaddddyyy", kallonta kawai yakeyi yana murmushi ya amsa da "Yesss Twwiinnkkllee", tayi dippping stick d'in ciki takai bakinta, saida ta lashe tace "Daddy life is always better with nutella jar", kai ya kad'a mata yana dariya dan yasanta da son zak'i yace "Really?", kai ta kad'a mishi tace "Yessss, and do you know what makes life the best?", kai ya kad'a mata alamar a'a tace "having the best Dadddyy like mine, you make life the best Daddyy", ta fad'a tana kawo mishi craft stick d'in bakinshi tareda d'age mishi girarta d'aya kamar yanda yakeyi shima, ido ya lumshe yana jin k'aunar yarinyar har numfashinshi, ko kad'an bai damu da har yanzu bata samu kannai ba dan son da yake mata na sashi ya manta da wasu damuwanshi, baki ya bud'e ya lashe nutellar, daidai nan Batuul ta shigo rik'e da glass cup cikeda fresh milk, kallonsu kawai ta tsaya yi da mamaki da kuma chocolates d'in da suka baza kan gadon, ita sam bata ma san da yana d'akin ba, sake shigewa jikinshi twinkle tayi ta kanainayeshi tana sadda kai k'asa, zama tayi bakin gadon bayan ta k'araso cikin d'akin batareda ta kallesu ba ta ajiye cup d'in kan drawer tace "zimme gone yay"("sauk'o ki d'auka ki sha"), a hankali ta janye jikinta daga na Abu, da ganinta kasan batada gaskiya, har ta mik'a hannu zata d'auki cup d'in ta fasa ta d'ago idanunta masu haske ta sauk'esu kan Batuul da ta zauna babu wasa fuskanta, kamar zatayi kuka har idonta ya cicciko tace "Mommah am sorry pls, imma not gonna take chocolates again", batareda Batuul ta kalleta ba tace "nyiro gone yay na woko",("Nace ki d'auka ki shanye ko?"), jiki a sanyaye ta mik'a hannu ta d'au cup d'in tareda kaiwa bakinta tana yatsina fuska ta fara shan madaran da aka tafasa da spices(cinnamon da cardamom), kurb'a ta dinga yi kamar baza ta shanye ba, saida ta shanye fiyeda rabi snn ta kalli Abu dake zaune yana kallonta ta langab'ar mishi da kai tanason ya taimakata ta bar shan madaran nan haka, tsaresu da Batuul tayi da ido yasa shi shima langab'ar mata da kai tareda lumshe mata ido, alamun tayi hak'uri kawai ta shanye tunda Batuul ta kasa ta tsare, maida cup d'in tayi bakinta ta shanye sauran da ya rage hawaye na sauk'o mata, Sai da ta gama shanyewa tass snn ta karb'i tumbler daga hannunta ta mik'e zata fita daga d'akin batareda tace musu komai ba, raurau twinkle tayi da ido tana kallon Daddynta dake zaune, hannu yasa ya rik'o Batuul, bata juyo ba snn bata ci gaba da tafiyan ba, cikin sanyi taji muryar twinkle na cewa "Mommah kanadi tay plsss, I promise not to take chocolates again, don't be angry plss Mommah, Daddy tell her I promise not to", "( Mommah kiyi hak'uri, nayi alk'awarin bazan sake shan chocolates ba, kar kiyi fushi dani kinji Mommah, Daddy ka fad'a mata nace bazan sake ba plsss", muryan Abu taji shima ya kwaikwayi yadda twinkle d'in ke magana yace "Mommah kanadi tay, gadero diyen ba plssss", ("Mommah kiyi hak'uri baza mu sakeyi ba"), juyowa tayi tareda dubansu d'aya bayan d'aya har suna jin dad'in ta huce fushin da takeyi duk faces d'insu yayi lighting da smiles, "Dinner is ready", ta fad'a tareda juyawa ta bar musu d'akin, raurau twinkle tayi da ido tana kallon Daddyn nata, ido ya lumshe tareda mik'a mata hannunshi, pan d'in grilled salmon d'in dake hannunta ta ajiye kan dinning table d'in, ta juya zata koma kitchen d'in ta hangosu suna sauk'owa kan stairs, shigewa tayi ta fito riqe da bowl d'in ta ajiye kan dinning d'in shima, har sun zauna a lokacin, kujera taja ta zauna, saida ta fara serving Twinkle kamin tayi serving Abutturab da kanta, A nutse suka fara cin abincinsu bayan sunyi addu'a, Kallon plate d'in kawai twinkle keyi riqe da fork a hannunta, kallon Abutturab Batuul tayi snn ta sake kallon Twinkle da ta k'urawa Plate d'in abimcin nata ido kamar mai son ganin wani abu jikin marinated olives d'in dake cikin abincin, da ganinta kasan abu na damunta, kujerarta ta matsar kusa da ta twinkle tana k'arb'an fork d'in dake hannunta ta gutsoro salmon fillet d'in tareda kaiwa bakin twinkle d'in, "Mommah jirero waltike dikkin ba fan3ma?, wande g3ran3mi, plsss", ("Mommah nayi alk'awarin bazan sakeyi ba dagaske kinj?, kar kiyi fishi plsss"), tayi maganar hawaye na gangarowa fuskarta, har cikin ranta takejin rashin dad'in ganin hawayen twinkle, da saauri ta d'auketa ta d'aura ta cinyarta tareda rungumeta tana rocking d'insu tace "Its okay baby, g3rang3i dei Twinkle, wande yir3mi, baby nyiro g3ranyin ba, bei b3rim", ("its okay baby, banyi fushi ba Twinkle, karkiyi kuka baby, bazan iya fushi da baby na ba, kici abincinki"), ta fad'a tana kai mata fork d'in bakinta, wani irin murmushi ne yayi escaping lips d'in Twinkle jin Mommah d'inta bata fishi da ita, a hankali ta bud'e bakinta ta saka mata abincin ciki, tana taunawa tana share hawayen dake kan fuskarta, saida ta gama taunawa snn ta kalli Daddynta dake kallonsu tace "Dadddy g3raz3i wono, am happy", ("Dadddy tace batayi fishi dani ba, naji dad'i"), murmushi yayi mata tareda mik'o mata hannunshi yana cewa "High five", tana dariya ta mik'a mishi suka tafa, suna tafawa tace "Goals yeah?", kai ya kad'a mata yana mata Thumb up, daga haka ta maida hankalinta kan abincin da Batuul ke bata, tab'are fuska Abu yayi yace "Wannan son kan naku dayawa, you guys are eating and no one is concerned about Daddy?, am hurt Twinkle, I will also go to my Ammah to feed me", ya fad'a yana langab'ar da Kai, dariya Twinkle tasa tace "Daddy you look an old smurf", dariya yayi yace mata "Tell your Mommah I want to b fed by her", kallon Batuul da tayi kamar bataji abinda yake cewa ba tayi tace "Mommah my Daddy wants you to feed him too", hararar wasa tayi mata tace "Sannunki mai Daddy", kujerarshi ya matso dab da ta Batuul yace "Glitter yanzu kin dena caring about me ko, kullum komai sai Twinkle, babu komai nima zan nemo wacce zata rik'a caring about me nima", ido Batuul ta zaro tace "Amor rigima dai kace kake jin yi, ko breakfast we had it together, we fed each other fa, yanzun ma its because ina feeding Twinkle ne, bara in gama da ita sai in baka, kasan I can't take it ka samo wata mai kula min da Kai, nida  ita ma mun isa haka, plss kaji?", tafad'a tana langab'ar mishi da kai tareda zumb'uro d'an bakinta, kamar jira takeyi ya matso da kujerarsa kusa da nata tareda sunkuyowa yayi brushing lips d'inshi kan nata, ido ta wara tana janyewa tareda yi mishi alama da Twinkle fa na nan zaune, murmushi yayi yace "nima d'in bazan iya kallon wata ba bare har ta kular miki dani, Inajin dad'ine in kikayi feeding d'ina, and then those lips, kinsan bana iya resisting d'insu ko, I love everything about it, ke kuma kullum sai ki rik'a pouting d'insu, they tempt me to", ya k'arasa maganan yana kallonta yana son ta d'ago su had'a ido, murmushi kawai tayi tana ci gaba da bawa Twinkle abinci, saida ta tabbata ta k'oshi snn ta juyo ga Abu ta fara bashi dan taga bashi da niyyan ci, tare suka ciyar da junansu abinci cikeda kwanciyar hankali, Daidai suna gamawa aka k'ira sallah Isha, Twinkle da Abu tare suka tafi masallaci Batuul tayi a gida, tana idarwa ta shiga had'a musu kayansu da zasu yi tafiya gobe dashi, suma  bayan sun idar da Sallah sukaje gidan Ajiddeh, tayi kyau abunta duk ramar nan ta b'ace, cikeda Murna Twinkle ta hau jikinta, tunda sukazo take ta surutu, Ajiddeh ma ta dinga biyeta, bata sauk'a daga jikinta ba saida zasu tafi, saida ta rakosu bakin mota ta rad'awa Twinkle magana a kunne, a mota Abu ke tambayan Twinkle mey Ajiddeh ta fad'a mata, sam taqi fad'a mishi tace "Mummy said I should tell Mommah first", haka ya hak'ura, Batuul kam tunda taga har an idar da sallah basu shigo gida ba tasan mayb ya kai Twinkle yawo ne dan sun saba hakan, suna komawa gida ta tafi da gudu jikin Batuul tana mik'a mata ledan dake hannunta da Ajiddeh ta bata, karb'a tayi ta duba mey ke ciki, tana gani tasan inda sukaje d'in dan duk lokacin da taje ire iren abubuwan da take batan kenan, da murna ta zauna kan cinyar Batuul ta zagaye duka hannayenta biyu jikinta ta sunkuyo dai dai kunnenta snn tace "Mommah, Mummy ye nyiro gulnge wa Disney world California wo sadin wono" (Mommah, Mummy tace in fad'a miki zaki zata kaini Disney world Carlifornia tunda muna summer ne yanzu", Babanta ta nuna mata tace "Daddy ro gulle, shima deciding sidin", ("ki fad'awa Daddy, shi zaiyi deciding", ba musu ta sauk'o ta fad'a mishi yadda sukayi da Ajiddeh, ya jawo hannunta yana d'aura ta kan cinyarshi yace "Twinkle I don't like America you know?", jiki a sanyaye ta kad'a mishi Kai, yayi murmushi dan yasan tsoro taji zai hana zuwan, yayi murmushi yana kamo cheeks d'inta duka biyu yaje "But we will be going to Paris", ihu ta saka tana rungumeshi tace "I will see small Mommah there", yace " Yeah But after coming back from Nigeria, then we  go to Paris", pecking duka kumatun nashi tayi tace "I love you Daddy", shima pecking d'inta yayi yana cewa "I love you more Twinkle", "Daddy can I tell Mummy we will b going to Paris not California?", yace "You will tell her tomorrow, its late now, okay?", kai ta kad'a mishi tana k'ok'arin sauk'a daga jikinshi, Batuul dai na zaune tana jinsu batace komai ba, saida suka gama hirarsu wajen 8:15 tacewa "Twinkle ta tashi taje tayi mata wanka ta kwanta dan gobe zasuyi tafiya, a nan toilet d'in d'akin tayi mata wanka ta nad'ota cikin towel, lokacin Abu shima ya tafi yin nashi wankan a d'akinshi, saida ta gama shiryata tsaf snn sukayi addu'an bacci a tare, daga gefenta ta kwanta tana karanto mata stories of the Sahabas daga wayarta, dan har sun gama na prophets, jin ta dena tambaye tambaye hakan ya tabbatar mata da tayi bacci, ta gyara mata kwanciya tareda pecking d'inta snn ta sake tofe duka d'akin da addu'a, k'asa ta sauk'o ta samu Inna Halima(Mai kula da Twinkle da Ammah ta samar musu) a kitchen tana y'an goge goge, sanar mata tayi da ta kwantar da Twinkle, ta bar aikin haka ya isa taje su kwanta, saida ta kashe komai ta tabbata everywhere is safe ta koma sama itama, d'akinta ta koma dan yin wanka, tana k'ok'arin cire kaya ta mirror ta hango mutum kwance kan gadonta, k'ara ta saki zatayi waje yayi maza ya kamota, sam bata lura dashi ba lokacin da ta shigo, rungumeta yayi yana mata magana k'asa k'asa a kunne, yasanta da saurin tsorata amma bai tsamman yanzu ma zataji tsoro ba tunda d'akin duk haske ne, a kunne ya rad'a mata "Shhhhh Glitter, sorry kinji?, banso na tsorataki ba", har lokacin jikinta na b'ari, bata d'ago daga jikjnshi ba tace "I tot kana d'akinka fa", ya kamata suka zauna kan gado yace "its been long nayi wanka da kaina, keh nake jira kizo muyi tare", lafewa ta sake yi jikinshi tana turo baki  tace "shine ka tsoratani ko?", murmushi yayi yace "Sorry Fatima, ki rage tsoron nan kinji banaso babu kyau, beside ba ke kad'ai bace, Lil champ d'ina is there, kar tsoronki yayi affecting d'inshi", ya fad'a yana k'ok'arin rage mata kayan dake jikinta, tace "Amorrr, watanshi fa d'aya duka duka amma shine har an fara zumud'inshi, haka akayi tamin a cikin Lil Farida ma", ya shafa cikin nata yace "I wish duk wata zaki bani sabon Baby ba, da nafi kowa murna, inason yara Fatima, kamar 12 or more, inason in ganshi kamar wani mini nursery, duk motsi inji yara kusa dani, i know i can't pay you but bakina bazai gaji da yi miki addu'a ba, Allah yayi miki albarka", tausayi ya bata, tasan yana da son yara, gashi ita kuma Allah bai sake bata wani cikin ba sai bayan shekara hud'u, Ajiddeh kuma har yau shiru ko b'arin wata batayi ba, har yau suna zaryan zuwa asibiti, rungume shi tayi tace "Amorrr, In sha Allah the best will happen kaji, Alkahairi da Albarka muke nema ba yawansu ba, in mukayi addu'a komai daidai zai tafiyar mana", muemushi yayi yana sake matseta a jikinshi, tare sukayi wanka sukayi shirin kwanciya bayan sunyi addu'o'insu, Washegari suka tashi da shirin tafiya Nigeria su dukkansu, suna isa Abuja suka sake boarding wani plane d'in to Maiduguri, banda Ajiddeh dan tace ita su barta a gidansu, in yan gidan nasu sun tashi zuwa zata biyosu su taho Maidugurin tare, da farko yaqi amma sbd magiyar da ta riqa mishi ya hak'ura, a gidanshi na can dake Old GRA suka sauk'a, daga gidan Ammah da gidan Aunty aka turo musu abinci dan su sunyi kwana biyu da zuwa,  suna idar da Sallah Magrib suka shirya suka tafi gidan Aunty sbd zumud'in da Batuul keyi na son ganin yan gidansu, a parlour suka tarar da kowa, duk sun k'ara girma baki d'ayansu, da gudu Twinkle ta haye jikin Baba dake parlour dan tanason tsohon sosai, lokaci lokaci take sawa Abu ko Batuul su k'ira mata shi suyita waya, sama ya d'agata yana cewa "Ashe amaryar tawa na hanya shiyasa nake ta jin k'anshi ko ta ina", dariya tayi tana ajiye mishi jakan turaren da tayi ta rigiman ita zata d'auka tace "Handsome granny, this is for you", dariyan sunan da ta k'irashi yayi yace "Na manta ashe Baturiya ce, How was your journey?" kamin tayi magana Aunty ta d'agata ta baya tana cewa "Abinda ya kawoki kenan dama, ki gama kalle Handsome granny ko, toh ina nan babu mai kallar min shi,  harta fara rigiman a sauk'ta ganin chocolate pack a hannunta yasa tayi shiru tana murmushi, Dariya suka sa su dukkan Aunty tace "Sarkin kwad'ayi, wato kinga chocolate shine kikayi shiru ko, ungo karb'i ya daifi ki sha ki barmin Handsome granny d'in", Nan su Abu suka zauna sukayita hira, sosai Aunty da Baba sukayi murnan ganinsu da result d'in da Batuul ta nuna musu na kammala makaranta, ta gama degree d'inta da first class honour, tho su Ahmad da Sa'eed sunje graduation d'inta da yake a UK suke karatu suma amma ba gari d'aya ba , sai albarka suke saka musu, anan Batuul ta Bawa kowa tsarabar da sukayo musu , har d'an kwalla Batuul tayi ganinta cikin y'an uwanta after years, kasa hakuri tayi gobe tazo ta gansu saida tazo a yau, har d'an kwalla ta share tana tuna rayuwarsu ta baya, da a dane da yanzu itace gefen Baba , But life has to move on, yau itace da tata y'ar tana raino, a ranta ta dinga furta "Alhamdulillah", k'arfe tara sukayi haramar tafiya gidan Ammah, Abu a Twinkle ne suka fara shigowa, turus ya tsaya ganin Farida zaune parlour da titsetsen ciki( shekararta d'aya da aure itada Affan d'inta) zaune ta tasa fruits gaba tana ci kanta ko d'an kwali babu, da gudu Twinkle ta je ta rungumeta tana fad'in "Small Mommah, Daddy didn't tell me you are here", rungumeta tayi tana jin dad'in ganinsu dan dama zuwansu take ta jira tun d'azu taqi tabi Aunty Sadiq kuma taqi baccu, da murnarta tace "Lil me, kin girma, Mommah na kula dake sosai", tayi dariya tace "Mommah are you too getting me a new lil smurf, Daddy said Mommah too is getting me a new Lil smurf?", ta fad'a tana tab'a cikin Faridan, muryan Abu ne ya katsesu yace "Yanzu shi  Usman(Affan) dinne ya barki kina yawo tsakanin Nigeria da Paris a condition d'innan naki, marairaicewa tayi tace "Yaa Abu I was missing you all shine da naji zakuzo ya had'ani dasu Aunty Amna muka taho a tare, kuma I will be coming for Yaa Sadiqs wedding, inaso ayi duk shirye shiryen tare dani shiyasa nazo tun yanzu, shima next week zaizo", d'an tsaki yaja yace "Ai zanyi magana dashi inji inma ke kika matsa mishi da sai kin taho d'in", ya fad'a yana k'arasa shiga ciki, cikin d'aga murya tace "Dagaske nifa ban matsa ba Yaa Abu, ko ka tambayeshi he will tell you same", ko juyowa baiyi ba ya k'arasa ciki, A bakin kitchen ya had'u da Ammah tana fitowa, take murnarshi ta fad'ad'a ya rungumeta yace "Barka da gida Ammah", Ammah tana dariya tace "Da girmanka kana shirin tarb'o second child d'inka baka bar rungumata ba", ya marairaice fuska yace "Bazan tab'a canjawa daga Abutturab d'inki ba, kema you will always be my Ammah komai yawan yaran da zan haifa", ya fad'a yana pecking goshinta, tayi murmushi tana shafa kanshi tace "Inasu Bittin?", yace "suna parlour", k'arasawa sukayi parlour suka tarar da su duk sun zazzauna sai hira sukeyi gwanin sha'awa, Abu ya dubi Ammah yace "Ammah dubi yarinyar nan at this her condition aka barta take yawo haka", marairaice fuska Farida tayi tana duban Ammah with pleading eyes, Ammah tace "Toh ai ko ba yanzu ba zata dawo gida yin jego, shine dasu Amna zasu dawo Usman d'in yace ta biyosu", harara ya sakarwa Farida  yace "Samun guri dai, dan zaka haihu sai kayi ta yawo", daga haka ya mik'e yayi side d'in Abui, Farida kam ko d'agowa batayi ba tasan intayi magana sabon fad'ane kuma,  Batuul kam dariya ta dinga mata k'asa k'asa, ba a jima ba Sadiq ya shigo gidan shima, nan sukaci gaba da hirarrakinsu, Batuul kam sai tsokananshi takeyi ya kusa zama ango, Gashin nan da yake tarawa duk ya ragesu ya k'ara girma into a responsible mutum sosai amma duk da haka saida ya biyesu dan shima d'in gwanin tsokanan ne, Twinkle kam sam taqi zuwa wajen Ammah, tana b'oye jikin Farida duk maganar da take mata na tazo taqi, tana ganin an kawo kwab'ab'b'en jan lalle tayi maza ta mik'e daga jikin Farida tace "Will you do it for me Granny? I want to look beautiful", Ammah ta dubi Abu dake shan fruit Salad tace "badai har yanzu turancin nan kake mata ba Abu, haba inata magana yarinya tak'i zuwa", Batuul ce tayi maza tace "Tana fa jin Kanurin Ammah, haline dai da take dashi", Ammah tayi maza tace "Hali irin na Babanta ba, shima haka yake ai da yana k'arami ayi ta mishi magana yana jin mutane yaqi kulasu, amma dai keh ba turan cin nan kikeyi mata ba ko, dan wannan ai asara ne yaro ya taso baijin  yarenshi", Batuul tayi murmushi tace "Da kanuri nake mata magana", Ammah tace "Kin ko kyauta, hakan yafi ai, Turanci da larabci ai ko a makaranta ka koyesu amma yarenka in bakayishi tun a gida ba babu kuma Inda zaka samu ka iyashi", ta dubi Twinkle tace "ja'ira da da nake ta miki magana kina jina kika k'i kulani shine saida kika ga lalle ko kike cemin a miki, you want to look beautiful, toh ko me zakiyi baza ki fini kyau ba bare ki samu k'wace min miji, zo zauna ayi miki, tsohon mijin naki ya biyani", duk wannan maganan da kanuri tayi mata shi, kallon Batuul tayi tana son tace mata taje d'in, kai ta gyad'a mata alama taje snn tace "wande nan fuun Nasaran(English)nduro mananimi, fanema naaa?"(Kada ki sake yiwa kowa magana da turanci nan gaba kinji?"), kai ta gyad'a mata tace "Yo Mommah", ta nad'e mata hannun riganta da yake dogo son ta tafi kusa da Ammah ta zauna, saida aka fara mata a hannu kamin a fara yiwa Ammah, taso ayi mata na k'afa amma a al'adar kanuri yara ko y'an mata basa yin lallen k'afa sai dai matan aure, sam Batuul tak'i yadda da ayi mata shi, sai wajen sha d'aya sukayi musu sallama akan gobe zasu dawo suci gaba da ziyara har gidansu Shehuri, har parking lot suka rakosu, Twinkle kamar a barta ta kwana dan ta sake da Ammah kuma ta bata chocolates masu dad'i, ana fitowa Twinkle ta hango wata mota tace itakam Sam a ciki zasu tafi gida, babu yadda suka iya haka Sadiq ya koma ya d'auko musu key d'in motar, Batuul kam na ganin motar  saida gabanta ya fad'i, shekara biyar yanzu amma tana iya tuna komai about motar, Sadiq na kawo key d'in suka shiga, sai tsokanan Twinkle yakeyi da turanci, ta had'e rai tace "My Mommah said I should not speak Nasara again", Sadiq ya kwashe da dariya yace "And you just did", tayi maza ta riqe baki tace "Sorry Mommah", Batuul kam shiru tayi tana ta tunane tunane zaune cikin motar, har suka d'au hanya bata ce komai ba sai Twinkle da Abu ke hiransu, Pidgin motar Twinkle ta bud'e tana saka hannu ciki, wani d'an kwali ta ciro a ninke cikin pidgin d'in sai k'anshi yakeyi, Abu tana nunawa tace "Daddy see what I found", Hannu ya mik'o daga baya ya amshi d'ankwalin yana kallo da ido, ido Batuul ta wara ganin d'an kwalin, takan manta da kayanta koda bata rabu dasu ba, in har ba ganinshi tayi ba mancewa takeyi dasu, Ammah wannan tana ganinshi ta tuna komai da ya faru da ita a ranan da ta sakashi, ranan da ta fara had'uwa da Abutturab, ranan ta fara shiga motarsa, ranan komai na rayuwarta ya canja, a hankali taji bugun da zuciyarta keyi ya fara daidaita, hannun Abu masu d'umi taji cikin nata, ajiyar zuciya ta sauk'e tana   jin wani abu na ratsa duka sassan jikinta, ido ta lumshe ta bud'e snn ta kalleshi tace "You still remember?", murmushi yayi yana kawo hannun nata daidai bakinshi yayi kissing snn yace "Ban tab'a mantawa ba Fatima, Ban tab'a mantawa da rana d'aya da nayi spending tare dake ba, they are my most treasured  moments and memories I always keep to reminisce, ranan da kika saka kayan nan ranan na fara had'uwa dake, ranan da sonki ya zama a part of my breathing,ranan na fara d'aukanki a motata, ranan nasan komai nawa ya canja, hankalina bai sake kwanciya ba saida na mallakeki a matsayin matata, son da nake miki is something da ban san ya akayi na fara shi ba kuma bansan ya zan gama shi ba, abu d'aya nasan ina fata yanzu, to be with you till my last breath Fatima, I can't imagine life without you yanzu because inasonki dayawa, I love you a lot", murmushi tayi idonta na cika da kwalla ta kwanto ta jikinshi tace "I love you more Yaa Abu, I will be with you In sha Allah", "In sha Allah" shima yace yana sake kissing hannun nata, Twinkle dake wasa da iPad can baya bata san ma mey ake ciki ba, kamin su k'arasa gida har tayi bacci.

💖💝BATUUL💖💝Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ