💖💝BATUUL 45💖💝

7.1K 356 0
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



         K'arasawa yayi bakin gadon yasa hannu zai yaye bargon yaga small figure ďinta na bacci peacefully a ďan takure, kitson da aka yi mata ya rufe rabin fuskanta, d'an tabe baki yyi ya bugi gefen gadon da nufin t'ada ta amma ko motsi bata yi ba, cire bargon yyi lkci daya ta mike xaune da sauri ta shiga komawa baya ganinsa, tsaki yyi yace "Kin ma yi breakfast din kusa?" Kai ta gyada ba tare da ta kallesa ba, yace "Gud, sae ki tashi kiyi sllh ki kara komawa kitchen ki sama ma kanki lunch, don matata bata girki!" Jin bata ce komae ba ya duka kusa da ita har tana iya jiyo numfashin sa da kamshin turarensa da ya cika ta, cikin kaushin murya yace "Hope am clear?" Kai ta gyada masa tana kkrin mayar da hawayen idonta, ya juya ya fice daga dakin.



      
       Kwance ya tadda Ajiddeh parlour, kwalin pizza duka uku a buďe an ďan tab'a kowanne, sai apple a hannunta yana kallon Tv, daga gefenta ya zauna ya kamo hannunta yana kallonta yace "shine kika gudo kika barni koh babe", ba tareda ta kalleshi ba don ita kam Batuul ta tsaya mata a rai tace "ai bacci ka keyi shi yasa na dawo nn" murmushi yyi ganin ynda ta basa amsan  ya mik'e yace "tashi kiyi sallah toh", dauke kai tayi kawae, kwalin da tayi littering yabi da ido ya kaďa kai ya koma sama, yana idar da sallah ya koma gaban desktop ďin dake ďakinshi, buďewa yayi yana dudduba sak'onnin da aka turo mishi, yawanci daga office ne sai na k'arshen ne ya gani daga Sadiq, sai da ya gama buďe na office ďin tukunna ya buďe wanda Sadiq ďin ya turo mishi, tsayawa yayi ya gama karanta abinda yake ciki tukunna yayiwa sauran reply sannan ya kashe ya ďauki wayanshi ya shiga neman layin Sadiq, Sadiq na ďauka yace "Yo bro, kun isa lafiya", Abu yace "Sallama kenan", kai Sadiq ya sosa kamar yana gabanshi yayi sallama, Abu ya amsa yace "Yeah naga ka turomin abu ta email, Sadiq yace "Ehh Abui ne yace in turo maka, acceptance letter Batuul into London University of Economics ba?", Abu yace "tun yaushe aka nema mata admission ďin, like everything is so fast kuma tana da wannan k'ok'arin ne na karatu a can ne ma?", dariya Sadiq yasa yace "Yaa Abu dont estimate Batuul, yarinyar nada kok'ari sosai, ai sai da akayi issuing transcript ďinta suka bata admission toh kaga they are satisfied with her perfomance", yace "Fine naji, sai anjima ka gaida gida", Sadiq yace "Okay bro, a gaidamin Batuul da sis Ajiddeh", yace "zasuji", daga nan ya katse k'iran, duk da yana son jin muryar Ammah bae kirata ba don bae son ta d'aga masa hankali da xancen Batuul.




     Kan abin sallah ta zauna tayi jigum bayan ta idar da sallah, akwatinta da wayarta ke ciki ta hango daga gefe, bata san ma ko yaushe aka shigo dashi ba, da murna ta tashi ta isa ta buďe akwatin, wayarta dake ciki ta ciro ta kunna, ganin layin dake ciki yasa jikinta yin sanyi ta koma bakin gadon ta zauna, yanxu sai ta sayi sabon layi kenan, ďan tsaki tayi ta jefa wayan kan gado, tana missing gida, tana son tayi magana da Aunty da kowa ma, hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta, tunanin roaming ne ya faďo mata, da hanzari ta mik'e tana dariya ta ďauko wayar daga kan gado, babu b'ata lokaci tayi roaming, da murmushi a fuskanta ta shiga dialing Aunty, kamar jira akeyi aka ďauki wayan, da murna tace "Hello Aunty ina kwana", ajiyar zuciya Aunty ta sauk'e daga ďaya b'angaren har Batuul na jiyowa tace "Lafiya Batuul, halan yanxu kika tashi daga bacci naji kina kwana", dariya Batuul tayi tana goge hawayen idonta tace "A ah Aunty, garin ne kamar safiya shiyasa nace kwana, yanxu nayi azahar ma", Aunty tace, "yayi kyau Batuul, tun ďazu ma muke trying number ki baya shiga, Su Mahir sai damuna suke a k'ira musu ke", kukan dake shirin fitowa ta maida jin abinda Aunty ta faďa mata tace "Allah sarki Aunty suna ina, a basu mu gaisa", Aunty tace "sunyi bacci Batuul tun ďazu, sai dai gobe in basu ku gaisa", kai ta kaďa kamar Aunty na ganinta, Aunty tace mata "Batuul kun isa lafiya babu matsala ko, ina y'ar uwar taki", wani iri taji maganan Aunty, wai har itama cewa take Ajiddeh y'ar uwartace, dan batasan mey ya gama faruwa bane bama yau da safe, sai da Aunty ta sake maimaita tambayan jin tayi shiru, a hankali tace "Aunty tana lafiya, ai tana ďakinta", Aunty tace "yayi kyau Batuul, in kin huta zamuyi waya kinji, inason muyi magana", Batuul tace "Toh Aunty, Baba fa, yana gida?", Aunty tace gashi nan Batuul, tayi rau rau da ido tace "Aunty shine baice zaiyi magana dani ba", Aunty tayi dariya tace "ai gashi nan faďa mishi da kanki", kamar zatayi kuka bayan Aunty ta mik'awa Baba wayan tace "HellO Baa, nda dubdo", da murmushin shi na manya yace "Mamana nda dubdo, ya sabon waje", a hankali tace "Baa Alhamdulillah", yace "Masha Allah Batuul, Allah yayi miki albarka, ki kula da ibadunki, ki girmama na gaba dake kinji, babu ruwanki da tsokana ko tadawa mijinki hankali, ki zama mai biyayya kuma kiyi ta hkuri kinji, Allah ya taimaka", tana kuka da k'yar ta iya buďe baki tace "In sha Allah Baa, nagode", da haka suka katse k'iran, kuka sosai ta sa bayan sun gama wayan, shikenan rayuwanta ya canja kenan, ta dde xaune ganin yunwa ya dameta don har uku na rana yyi yasa ta mike a hnkli da Hijab jikinta ta tura kofan dakin ta fito, downstairs ta nufa a xuciyarta tana addu'an Allah yasa Ajiddeh bata nn, xaune ta sameta falon tana kallo tana cin sauran pizzan ta, duk irin faduwar da gabanta yyi hkn bae sa ta koma ba, cikin natsuwa ta tako har cikin falon ta kalleta a hnkli tana ci gaba da tafiya tace "Ina yini Anty?" Wani matsiyacin kallo Ajiddeh ta bi ta da shi har ta shiga kitchen din, snn ta mike, sae da ta fara kallon stairs snn ta bi ta cikin kitchen dib, Batuul na tsaye tsoro ya cikata don xuciyarta ya bata sae ta biyota, lallai tayi gangancin sakkowa Ajiddeh na falo, daga bakin kofa ta tsaya tana kallonta tana murmushin rainin hankali tace "Ke a tunanin ki kin samu gun xama a gidana koh? To yhu are mistaken yarinya, don sae kin gwammace da baki shigo gidana da sunan xama kiyi karatu ba, banda kinibibi, gulma, da munafurci irin na iyayen ki sun san basu da halin kama maki hostel me xae kai su karambanin turo ki UK karatu, shine xa a wani xo a daura ma miji na nauyi da wahala to wllh kun yi kadan, duk uban da ma ya kawo wnn shawarar zae saketa ne, don sae sai kin gwammace da titi kike kwana kan gidana, makwadaita kawae" Ae Batuul bata san lkcn da ta fashe da kuka jin xagi da cin fuskar da Ajiddeh ke ma iyayenta, ita din ba mai son fada bace bare ta mayar mata da martani, durkushewa gurin tayi ta dinga kukan takaici da tausayin rayuwarta, ran Ajiddeh yyi fari don har da murmushinta, ta cigaba daga inda ta tsaya.



💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now