💖💝BATUUL 10💖💝

7.8K 400 0
                                    



Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

        Sweat pant blue ke Jikinshi da riga bak'a yana dadanna Macbook dinshi, tea ne a flask daga gefenshi idan yayi aikin sai ya ďan sha kaďan, wayanshi ne yayi k'ara ya ďauka yaga Amma keh k'iranshi, rusuna yayi yace "Hello Ammah", daga ďaya bangaren Ammah ce ta amsa da " ina falon sama, kazo ina jiranka", tunani ya fara yi akan dalilin wannan k'ira da take mishi dan tun daga muryanta ya san something is up, maganan Ammah ya sakeji tana cewa "banji ka amsa ba", da sauri yace "Ammah ina zuwa yanzu" ya katse wayar, matsar da Macbook ďin yayi gefe ya tashi ya fita daga ďakin, hanyar falon sama yabi har ya isa, yana zuwa yaga Abui da Ammah a zaune tare a kujera ďaya, k'arasawa yayi ya nemi waje ya zauna akan tattausan rug ďin dake shimfiďe , a kusa da Abui dab ya zauna daga k'asa, kanshi dake duk'e ya ďago ya gaida su a tare, Abui ne ya fara amsa mishi sannan Ammah, bayan y'an seconds Abui yayi gyaran murya tare da k'iran sunan shi, "Abutturab magana zamuyi dakai kamar kullum akan dai maganan kayi aure ne, mun gaji da zaman ka haka, you are not  getting  any younger, girma kakeyi", Ammah ce tayi sauri ta karashe maganan da cewa "bazan yadda da tafiyanka wajen nan babu mata ba, wane aiki ne zakaje ka k'ara banda wanda kayi musu ba, yanxu Abui ke cemin gobe zaka tafi ,kuma kana gama aikin ne zasu tura ka waje, toh ni bazan yadda ba, kayi aurenka in yaso kaje kayi shekara goma a can banida damuwa", Abui ne ya tareta da cewa "a ah ba shekara goma ba dai, abi komai a hankali, yanxu kai Abutturab kamin ka gama contract dinnan dasu har su turaku wajen muna so ka fiddo da mata ayi muku  aure, mutuncinka ma zaifi k'aruwa a idon mutane, within two weeks kayi mana introducing wacce kake so aje a samu magabatan ta, inma babu wacce kuka daidaita zamu samo maka a family, ga cousins ďinka ko a cikinsu ka duba, in akwai wacce tayi maka kuka daidaita fine, in kuma babu sai ka nemo da kanka", Ammah ce tace "ai ni Nafison ma mu nemo mishin dan da alamun bashida niyya", Abui yace "Aure is a life time commitment, he should chose for himself, Allah yayi maka albarka", baice komai ba har saida su Ammah suka gama maganan da zasuyi sannan ya ďago kanshi yace musu "In sha Allah zainyi Ammah, but inaso a ďan k'aramin lokaci, two weeks ďinnan yayi min kaďan, a k'aramin ko da one month ne, in sha Allah by then i will be done with duk abunda zanyi, sai ayi introduction ďin" Ammah ce ta sake ce mishi "Aliyu ban yadda ba, two weeks ďinnan da na faďa shi kenan, tukunna ma y'ar gidan waye kake cewa za ayi introduction ďin da ita", sunanshi da yaji ta k'ira ne yasashi saurin ďago kanshi, don ya daďe baiji ta k'irashi ko da Abutturab ba amma yau gaba ďaya Aliyu ta ambata, a hankali yace "y'ar gidan perm sect ce Engr Abba Muhammad Jidda", Abui ne yace "Masha Allah, ai Engr abokina ne, mutumin kirki ne sosai, ba komai kaje in mun koma Abuja sai kuyi magana da yarinyar akan zaka turo, tashi kaje Allah ya maka albarka" Amin yace sannan yayi musu godiya ya tafi, Ammah dai bata so haďin nan da ďanta ya samo ba, dukda tana y'ar Tchad amma bata so ďanta ya auri yar gidan nan ba, amma haka dai ta hak'ura ba dan tana so ba, gara yayi auren da ya zauna babu mata, Allah  ya had'a kansu ya tabbatar da alheri. Bayan yayi musu sallama ya fita suka ci gaba da hiran Abutturab ďin da sauran y'ay'ansu bayan ya tafi

       Suna isa gida bayan sun shiga ciki dukkansu suka zube a palon, Baba ne da ya shigo daga k'arshe yace kowa ya shiga ya kwanta gobe flight ďinsu sha ďaya ne dan haka kowa ya shirya da wuri, mik'ewa kowa yayi ya tafi makwancinshi ya shirya yin bacci, Batuul na shiga ďaki ta cire kayan dake jikinta ta ďaura towel zata shiga toilet, fridge ďinta ta buďe zata sha Fanta taga ya k'are, wayanta dake ajiye gaban mirror ta ďauka ta nufi kan gado ta zauna sannan tayi dialing number Janet, tana ďauka tace "Janet ki kawo min fanta ďakina , na fridge ďina ya k'are, "Janet ta amsa da to anti za a kawo miki wani abu dinne bayan Fanta", Batuul tace "No i dont need anything else, am okay" sannan ta katse wayan ta ajiye ta shiga toilet, warm shower  tayi ta fito daga toilet ďin, tana fitowa akayi knocking k'ofar ďakinta karasawa tayi ta buďe, Janet ce ta shigo da square serving tray na ceramic ďauke da Fanta akai, da kuma carton a dayan hannun. Akan table ďin ďakin ta ajiye na tray din sauran na carton kuma ta bude fridge tana jera su. Ta juya zata fita Batuul ta k'ira sunanta "Janet ku shirya da wuri gobe zamu koma,ki faďawa Fa'iza da Aunty Tabawa, karku sake delaying ďinmu kamar lokacin da zamu zo", "Toh anti zan fada musu", "kuma ba sai kunyi breakfast dayawa ba,amma kije wajen Aunty ta faďa miki abinda za a dafa goben", da toh ta amsa sannan ta fita, tana fita Baatul ta shirya cikin kayan baccinta na Lulu kitty purple, ta haďe gashinta cikin hula dark purple ta gama shafe shafenta ta hau kan gado, Laptop dinta na Apple ta ďauko ta ďanyi danne dannenta sannan ta kashe ta mayar kan side drawer, wayanta ta ciro a caji, kamar dama jira ake ta ďauki wayan ya fara ringing, ganin mai k'iran ya sa wani wide smile shimfiďuwa a fuskanta, dimple ďinta sai da suka lob'a deeply, wayan ta saka a kunnenta tare da tsuke fuska kamar ba ita ke murmushi ba yanxu ta Kuma   yi shiru taqi magana, daga ďaya bangaren aka ce "shikenan since you wont talk, i will end d call, da sauri tace "Affaaannn" da k'arfi ta k'ira sunan har tana jiyo dariyanshi daga ďaya b'angaren, "woh lady so kike ki min bursting ear drums ko ko ya", sake k'iran shi tayi da Affanu, "ta yaya ma akayi kika zama friend ďita ya faďa yana dariya", "I know you love me" Batuul ta faďa mishi, ce mata yayi "waya faďa miki i love you, ai d moment you left for airport na manta da momeries and friendship ďinmu", face ďinta tayi kalan tausayi dashi ta zumb'uro baki kamar yana ganinta tace mishi "ka manta dani, nayi fushi ma tunda ka manta ni" murya ta fara yi kamar zatayi kuka, da sauri ya fara ce mata "No no no Lulu, kar kiyi kuka mana, wa ya isa ya saka Batulan Baba kuka, kema ai kinsan you are my potential treasure, ai nima sai ki sani kukan" ya faďa muryanshi na rawa, kyalkyalewa ta kuma yi da dariya, ce mata yayi "dariya ma na baki ko, am offended shikenan ma goodnight", da sauri ta tare shi, "wait wait pls, dagaske dariya ka bani how you reacted, so you care, interesting", dukkansu biyu a tare suka sa dariya, ce mata ya sakeyi "I misssed you bestfriend", a hankali itama tace mishi "I missed you too", "so when y'all coming back", Affan ya tambaya, "Gobe ina Abuja by now", da sauri Affan ya tambayeta "Dagske Lulu gobe zaku dawo, baby na fa", dariya Batuul tasa sannan tace "masu baby, toh ba gobe zata dawo ba sai nextweek, hope kana kula min da ita da kyau, jiya ma i was with her", ce mata Affan yayi  "i got to call her now in roqeta su dawo before next week dan i cant wait that long, I want to see her", Da dariya Batuul tace mishi "Aii best friend, good night", da haka suka katse k'iran, suna gamawa tayi adduan bacci ta shafe jikinta dashi, taje ta shafe duka k'annenta har way'anda ke kwana a ďakin Aunty, sannan ta tofe duka angles ďin gidan , ta kashe bedside Lamp ďinta ta kwanta

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now