💖💝BATUUL 22💖💝

6.1K 370 2
                                    




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

  
     Shiri suka hau yi bayan sunyi isha da magariba, ďakin Ammah suka zauna suna dudduba kayan, lace ne purple mai ďan ratsi ratsin grey mai kyau, ďinkin ya amshsu soaai, iri ďaya akayi musu, sai da suka gama Ammah ta dubi Batuul "Bitti kunyi kyau, amma babu sark'a da ďan kunnefa, ke Farida ya baki bata ba, sai ki saka keh kaďai", hararan Batuul Farida tayi sannan tacewa Ammah "Ammah kiga jewellery box ďin mafa a gabanta yake, nace ta zab'i wanda zata saka tak'i wai baza ta saka ba", Ammah cewa tayi "A ah Batuul bazai yiwu ba, ina aka tab'a gaye babu ďankunne", mik'ewa tayi ta buďe closet ďinta ta fiddo wani ďan akwati k'arami mai kyau kmar chest box na katako, sai da ta zauna ta buďeshi ta fiddo wasu set ďin y'an kunne da sark'a masu kyau da abun hannu da zobe na azurfa  harda agogonshi ta mik'awa Batuul, "ungo maza saka wannan", a kunyace Batuul ta karb'a ta saka, kamar wasu diamond ta saka haka ya dinga haske sabida tsabar kyan da yayi, sai da ta saka Ammah ta dubeta tace "Masha Allah ko kefa", wasu matane suka shigo dukkansu sunyi shiga ta alfarma cikin kayansu masu kyau, harda Aunty Amna a cikinsu, zuwa tayi kusa da Ammah sannan tace mata "Ammah motocin sunxo sunce a shirya a fito, tace toh sai kije ku fara tafiya, ni Sadiq ne zai kaini ku tafi tukunna", Farida ce ta fara fita, motan farko tabi, Batuul dake ďingisawa kamin taje motocin sun k'are, dawowa tayi tacewa Ammah babu motocin suntafi, a ranta tana murna Allah yasa babu wanda zai dawo, "ba damuwa, bari in Sadiq yazo sai mu tafi tare", tace "toh", ta hau gado ta kwanta, Takwas da kwata Sadiq ya k'ira Ammah uace mata ya iso, yana jiranta, wasu y'an matane sunsha kyau suma zasu wajen dinner suka ce mishi, tafiya zaiyi yace ehh amma Ammah yazo ďauka, suka ce mishi tunda ita kaďai ce bari su shiga dan har yanxu motocin suke jira su dawo, gaba ďaya bayan sunyi occupying saura seat ďin gaba kawai, tare da Batuul Ammah suka sauk'o, rik'e da hannunta a hankali suka taho sabida ciwon da taji, sai da suka zo Ammah taga mota a cike, ce mishi tayi "Sadiq ya akayi haka, ina Batuul ďin zata zauna", "Ammah bansan da Batuul ba shiyasa na ďaukesu", "Shikenan kuje da Batuul ďin , bari in k'ira Alai yazo in ya sauk'e mutanen da ya kai ya dawo ya ďaukeni, Bitti shiga kuje", Batuul dai na tsaye tana ta addu'an Allah yasa ma kar a samu space ďin, cewa Ammah tayi "a ah Amma, ke ki fara tafita ni sai a sa driver ya kaini ko Ahmad ne sai in k'ira ya kaini", bata rufe bakinta ba Ammah ta hango Abutturab yana tahowa, cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufo inda suke yana gyara hulan kanshi, k'amshin turarenshi gaba ďaya ya baza wajen, baima lura dasu a wajen ba, sai da ya k'araso yaji muryan Ammah ya ďago ya dubi inda suke, ce mishi tayi "yawwa Abu ka shiryako", yace "ehh Ammah yanxu zan wuce sunata jirana" ce mishi tayi "toh ga Batuul nan ka tafi da ita, bana son barinta ita kaďai a gida ni zamu tafi tare da sadiq", Batuul da kanta ke sunkuye a k'asa tana wasa da abin hannun da Ammah ta bata ďazu tayi saurin ďagowa ta dubeshi jin abinda Ammah tace, ido huďu sukayi ya daka mata harara tare da ďauke idonshi daga dubanta, marairaicewa yyi yace "Ammah sai fa naje hotel mun haďu dasu Massa da sauran friends ďina tukunna mu biya in ďauka Ajiddeh, tabi Sadiq kawae, ke sai mu tafi tare", Ammah tace "ka ji ka. ina ni ina wannan yawon da ka lissafa, gara dai itan, kuje da ita kawae, kuma ai Ajiddeh ba duka motar zata cinye ba da kake cewa zaka ďauko ta, iyaka ta zauna a gaba, Batuul ďin ta zauna a baya", wani irin b'acin rai yaji gaba ďaya ranshi, wai mesa Ammah ke son haďa shine da yarinyar nan ko da yaushe, a tak'aice yace "muje", snn ya juya ya nufi wajen motarsa, Ammah ta cewa Batuul dake tsaye a wajen ta rasa mey ke mata daďi "Bitti kuje kinji", a hankali ta fara ďingisa k'afarta ta isa wajen motar, wani tsaki yaja ganin yadda take tafiya kamar mai tausayin k'asa, sabuwar lambo ce bak'a k'irin mai tint glass, buďe gidan gaba tayi ta zauna , yadda ya fizgi motan ne ya tsorata ta tayi saurin sa hannunta ďaya a jikin k'ofa ďaya a wajen hand brake tana neman wani abinda zata rik'e, jin hannunta tayi kan nashi, da sauri ta janye nata hannun ta dafa gaban motar, sai da suka fita tukunna Ammah ma ta shiga na Sadiq suka fita


    Gudu yakeyi akan titi kamar shi ya shimfiďa, tsabar tsoro har wani zazzabi ne taji yana son kamata, sanyi takeji sosai, hannu ta saka ta rage Ac dake aiki a motar, ganin ta rage Ac ne ya sashi juyowa ya dubeta yace "hw dare yhu! inamiki wasa ne zaki tab'a min mota, ko dan kin ganki a ciki" wayanshi ne yayi ringing ya duba yaga mai k'iranshi, bai ďauka ba har ya tsinke, haka ya dinga ringing wayan baya ďauka , daga k'arshe ma ya sata a silent, ita dai bata ce mishi komai ba, tunda abunda ke daminta ma ya isheta, ganin ya juyar da kanshi bai k'ara magana ba ta ďan kwantar da seat ďin motar ta ďanyi relaxing tare da lumshe ido dan kanta ya ďan fara ciwo , a hankali ya juyo ya dubeta yaga yadda ta jingina amma a takure, fuskanta ya kalla, idonshi ya sauk'a kan ďan k'aramin bakinta da aka sa mata purple ombre lipstick, kyabe baki yyi tare da ďauke idonshi daga kallonta yaci gaba da tuk'in shi, can ya sake juyowa ya dubeta, lashes ďinta da suka kwanto fuskarta ya kalla this time around, kamar zatayi magana ta ďan motsa bakinta, bin bakin yayi da ido, buďe idonta tayi taga idonshi akanta, da sauri ta mik'e ta gyara zamanta, shi kuma yyi saurin ďauke idonshi yayi ya mayar kan titi tare da jan tsaki, haushin kanshi yaji da ya tsaya kallonta har ta buďe ido ta ganshi, kuma fa ba wae tayi masa kyau bne, gyara zamanta tayi ta janyo kujeran, ta jingina kanta a glass ďin window tana kallon waje, a k'ofan hotel ďin yaja yayi horn aka buďe mishi ya sa kai ciki, motoci dayawa ya tarar na abokanshi suna jiranshi, duk sun shirya sunyi kyau, sauk'e glass ďin motar yayi tareda fitowa waje, inda suke ya isa, Massa ne ya fara tareshi "Kai fa wulak'ancinka dayawa Aliyu, ya zayi kazo ka bar mutane suna ta jiranka, kainefa da kanka kace babu african time 8 dot muna wajen , ana ta k'iran wayanka ma baka ďauka, har matar taka ma baka ďaukan wayanta tana ta damuna, har na rasa k'aryar da zan shirya mata ma ta yadda daga k'arshe", duk maganan nan da yakeyi Abutturab baice mishi komai ba, idon Massa ne ya faďa kan motar da Abutturab yayi parking , ce mishi yayi "Man ba cutie bace a motan can, mey takeyi a motan ka kuma", ba tare da ya kalleshi ba yace satota nayi zanje in saida ta, ya k'arasa wajen sauran abokan yana mik'a musu hannu, sai da suka gama gaisawa yace musu "kuyi hak'uri na b'ata muku lokaci, something came up, muje ko", kowa motarshi yaje ya buďe ya shiga, photographers na ta ďaukansu hotuna da video, bin Abutturab Massa yayi wajen motanshi yace "na tambayeka ya akayi ka taho da cutie kai da zakaje ďauko matarka ku wuce, ina zaka da ita, a hasale Abuturrab yace "bakaji bane, nace maka saidata zanyi" ya k'arasa wajen motansa, massa yace "Man i aint joking, am damn serious", yaje ya tsaya dab da widown da Batuul ke zaune yace "cutie", da hanzari ta ďago ta dubeshi, ce mata yayi "fito in kaiki a motana, tare zamu tafi", juyawa tayi ta kalli Abu, wani mugun harara da ya kada hanjin cikinta ya sakar mata, lkci daya ya dauke kanshi kamar bai san abinda suke faďa ba, da kyar ta iya bude baki tace " yaa Abu Bari in bi Yaa Massa tunda kaima zakaje....." tana k'ok'arin buďe k'ofa, cikin dakewa yace "come on get back, da kinsan da Massan kika tsaya sai da kika biyoni, kai kuma ka bari in na maidata kaje ka ďaukota ka kaita koma ina zaku, just follown Ammah's instruction" yana kai wa nn ya tada motarshi yaja ya bar sa wajen, tsayawa Massa yayi yabi motar da ido, toh mey Abutturab ďinnan ke nufine akan Batuul, haka rannan a wajen wushe wushe ya hanashi sakat, yau kuma ya hanata binshi, yasan kuma ba sonta yake ba, ina! dama ai babu batun so,  kafaďa ya ďaga yayi hanyar motanshi, koma dai menene zaiji bayan bikin, shima convoy ďin motocin da akayi yabi a baya


    Allah Allah ta rik'ayi su isa inda zasu ta rabu dashi, gashi ya wani hade rae wane hadarin kaji, ko kwakkwaran motsi ta kasa a motar, mistakenly idan ta kallesa kuma ya xabga mata harara, gate ďin gidansu Ajiddeh ya shiga dan a buďe yake kasancewar ana biki, wasu motocin sun samu sun shigo, wasu kuma na daga waje, parking yayi, y'an mata ne dayawa duk sunsha kwalliya sunyi kyau, wata ce daga cikinsu ta iso inda motan Abu yake, tace "ango muna ta jira har amarya ta gaji da jira", a takaice yace "Ae gashi nazo ďaukanta, kuyi mata magana, ko kuma bari in k'irata ta fito", harara tabi Batuul da ganinta a gaban Motan Abutturab, sae kuma tayi dariya tace "No bari inje in fito da ita dan nima yanxun daga wajenta nake", ta juya ta tafi, Massa ne ya fito yacewa sauran y'an matan suzo su shiga motocin kamin amaryar ta fito, a hankali take takowa, tun daga nesa ake ganin kyan da tayi, kayanta sai walwali suke saboda hasken dake wajen, tana k'arasowa wajen motan ta tsaya tabi abinda take kallo cikin motan da ido, buďewa yayi ya fito tare da cewa Batuul "get back" a hnkli ta buďe k'ofan motar tayi ta fito, wani irin Kallo Ajiddeh tabi Batuul dashi baki bude, Batuul bata ma san tanayi ba ta buďe gidan baya ta shige, zagayowa yayi ta gabanta yace "wifey" yana kallonta tare da buďe mata k'ofan, wani irin kallo ta sakar mishi tace "Aliyu mey haka?, wane sabon wulak'anci ne kuma wannan, ya zaka zo ďaukana zamu tafi dinner sai kazo da wata, motan nan fa musamman mukayi order saboda in shiga ranan nan shine ka ďauko wata a ciki", shiru yyi yana kallonta sanin gskya ta fada, hannunta ya kamo ya wara mata manyan idonsa yace "c'mon its your happy day, meye dan wata ta shiga, Batuul cefa ba kowa ba, my cousin sis bbu motar da xata shiga ne shi sa Ammah tace in daukota nima ba a son raina ba coz ke naso ki fara shiga motar", a fusace tace "ai nasha faďa maka ni bana son yarinyar nan, wlhy hankalina baya kwanciya duk inda na ganta, kuma ya xaka yrda ta biyoka bayan ga motoci da drivers a gida", Iska ya furzar daga bakinshi a fusace yace mata "get in, in kuma baxa ki shiga ba ki koma gida" yana kai wa nn ya zaga mazauninshi ya zauna, sai da taga dama tana cika tana batsewa sannan ta shige motan, yana fita sauran motocin suka bi bayanshi , a conference hall akayi dinner, suna shiga mutane duk sun hallara, shi da kanshi ya fito ya buďe mata k'ofa ta fito tana ta b'ata rai tana cin magani, Aunty Amna ta fito ta samesu tace k'annen ango ne zasu shigo da amarya, tsayawa Ajiddeh tayi tana jiran taga su waye k'annen Aliyun da zasu shigo da ita, a hankali Batuul ta fara ďingisa k'afarta zata shiga hall ďin, Aunty Amna ce ta tsaida ita, Batuul tsaya ku shiga da amarya, Farida na fitowa, tana gama rufe bakinta Farida ta fito, su suka tsaya a gaban amarya kaďan , Batuul a hannun hagu, Farida daga hannun dama, sai Abutturab daga gefen Farida,  kiďa ne ke tashi a hall ďin kowa yy kyau ssae, sae da suka shigo hall din Batuul tayi tuntub'e don dama ďingisa kafan takeyi, kan ta kai kasa Abutturab yayi maza ya rik'ota, shiru hall ďin yayi kowa idonshi da hankalinshi yayi kansu duk da basu karaso ciki ba gaba daya don da yawa sunyi xaton amaryar ce ya rike, xame jikinta tayi daga rikon da yyi mata ta karashe durkusawa wajen tana runtse ido hade da yarfe hannu, yana gnin hka shi ma ya bita ya durkusa da sauri yana kallon kafar yace "What?" Hawaye cike idonta tace "Na buge ciwona" Anty Amna ce ta taho da sauri don gnin abinda ya faru, Farida ta xaro ido tana kallon ikon Allah, Ajiddeh kam still tayi a wajen xuciyarta na bugawa da karfi.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now