💖💝BATUUL 86💖💝

9.7K 518 42
                                    






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



D'akin Ammah ya koma bayan ya fito d'akinshi, bai tadda kowa ba sai Batuul dake Lullub'e cikin comfy bargo tana bacci, d'akin ya shigo ya tura k'ofar ya karasa ya hau gadon ya zauna, bargon nata ya janye yaga gashinta da ya bud'e tun jiya na nan a bud'e, kallonta yakeyi with so much affection da tausayinta a idonshi, hannu yakai ya gyara mata gashinta ya maida shi baya, kallon face d'inta da ya kara haske ya tsaya yi kamar ba ciwo takeyi ba, dukda ta rame amma kyanta na nan, satinta d'aya kenan kwance anan batareda tasan ina kanta yake ba, d'an murmushi yayi tunawa da yayi yau za a gama yi mata magani in Allah ya yadda ta samu sauk'i ya kai hannu ya shafi gefen fuskarta tareda lumshe ido yace "Haya", hannunta ya kamo cikin nashi cikin sanyin murya yace "Fatima you are more than life itself, nasan kina jina ko Fatima, you are worth everything good life can offer, GWS kinji, I need to tell you how much you mean to me, you've become part of me, you know I never thought I could love anyone, I never tot someone could mean this much to me until I met you, The first moment I saw you, I knew there was something great about you, some vibes I can't explain, Mesa tun a da ban dawo gareki ba, I wish I had known you long ago, You have become a part of me, my Haya, I never knew I had life until I met you, in such a small period you have made me understood what love means, I never knew how it felt to b loved, at the beginning inace k'in ki nakeyi sabida effect da kike casting a kaina, but I was wrong, I was growing fond of you, you became an acquaintance, a friend and the very best person I could ever ask for", d'agota yayi ya d'aura kanta kan cinyarshi ya kama fuskanta da duka hannayenshi, idonshi ya rine har ya fara hawaye yaci gaba "Fatima pls get up, get up and don't leave me, I need to tell you how much you mean to me, I promise to keep you Happy all the time, Plssss Fatima, I really need you, just give me a second Chance to show you how much I love you, I really do", bai damu da drip d'in dake hannunta ba, rungumeta yayi Idonshi duk ya kad'a, a haka Ammah ta shigo ta sameshi, tun daga bakin k'ofa take jiyo maganganun da yakeyi, sosai take tausaya mishi itama har idonta ya cicciko, jiki a sanyaye tazo ta zauna daga gefenshi ta dafa kafad'unshi tace "Babana I've told you times without number addu'a zakayi mata, zataji sauki yau d'innan In sha Allah", kallon Ammah yayi da rinannun idanunshi ya kad'a kai yace "Ammah cewa fa yayi in har aka cikata na kwana bakwai ba a samu nasara saidai wadanda sukayi abin nan sun karya da kansu, su waye haka zasuyi mata irin haka, mey tayi musu Ammah?", Ammah ta girgiza kai hawaye taf idonta tace "Abu be optimistic, Da izinin Allah ya fisu, kuma zata samu sauk'i, mu jira har anjiman a gama mata magani sai muga abinda zai faru, kaci gaba da yi mata addu'a", shiru kawai yayi ya kasa cewa komai, tashi Ammah tayi tace "bari inje in sa a shirya shigowan Asheikh d'in sai inzo in shiryata", da haka ta fita daga d'akin zuciyanta duk ba dad'i ga fargaban dake tattare da ita, bayan ta fitane ya gyarawa Batuul d'in gashinta snn ya saka mata hularta




K'arfe bakwai Ajiddeh taji wayarta na ringing, kin dagawa tayi ganin Mum keh kira, duk fargaba ya cikata har wani sanyi sanyi takeji, zata kashe wayar kenan taga text ya shigo, budewa tayi ganin daga Mum ne, ce mata tayi "In baki d'auki wayan nan ba toh wlhy yanzu zaki ganni gidan da kika maida yafi iyayenki", jiki a Sanyaye ta gama karantawa kamin tayi wani abu aka sake Kira, saida ya kusa katsewa ta d'aga da k'yar tasa a kunneta, muryar Mum taji da daki dodon kunnenta tace "Don uwarki har kinyi girman da zan rika kiranki kina kashemin waya ko Ajiddeh, toh gani nan tafe gidan naku sai kin fad'amin dalilin da ya sa duk kika canja, kamin tayi magana taji kiit an kashe wayar, b'ari jikinta ya hau yi jin abinda Mum tace mata, hawayen ma kasa yinshi tayi tsabar tashin hankali, a ina zata samu mafita ita yanzu, tana yiwa Aliyu son da har in ya rabu da ita toh lallai itama zata rabu da tata rayuwar, d'aukar wayar tayi zata kira Mum tace mata zatazo ita gidan basai Mum d'in tazo ba amma har k'iran ya katse Mum bata d'auka ba, sau uku tana k'ira amma har lokacin bata d'aga ba, hannu tasa a ka ta saki wani razananna ihu ta tsuguna a wajen ta saki matsanancin kuka, shawara kawai ta yanke ta fadawa Abu ganin batada wata mafita, wayar ta jawo ta kirashi taji wayar na ringing a cikin d'akin, takaici duk ya isheta, mikewa tayi taje ta sameshi ta fad'a mishi komai, a ganinta hukunci da zai yanke mata ba zai zama mai tsauri ba snn yana sonta zata bashi hakuri tace duk sharrin shaidan ne, hakanan ta fito ko d'ankwali babu daga ita sai y'ar rigar baccinta, gashin da Abu ya tufke duk ta baje shi, Tana fitowa ta kusa cin karo da Ammah, kallonta Ammah tayi ganin duk ta rikice, da k'yar Ajiddeh ta iya had'a kalmomin daga bakinta tace "Ina kwana", Ammah da ta tsaya kallon yanayinta tace "Kin tashi lafiya?", kai kawai ta iya gyad'awa, Ammah ta tab'e baki tayi tafiyarta tana mamakin Abunda ya sami Ajiddeh yasa duk ta rikice da idonta ya kumbura ya rine kamar wacce tasha kuka, ganin Ammah da Ajiddeh tayi ya sake tsoratata, ji tayi jikinta duk yayi sanyi a haka take ganin baza ta iya tunkarar Abu da zancen ba don tun da suka xo gidan har yau bata ga fuskarta da na Farida ba, Sadiq kadai ke kulata gidan, shi kansa Abu ba wani lokacinta garesa ba, komawa d'akin tayi ta zube kan gadon ta rasa inda zata sa ranta taji dad'i


💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now