💖💝BATUUL 87💖💝

9.8K 497 19
                                    

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

      

      Can a asibiti lokacin da Matan nan ta farfad'o, Daddy da nurse na d'akin, nurse d'ince ta taimakawa matar ta gyara kwanciyarta, sai a snn taji duk jikinta ya rirrike ga wani ciwo da takeji a ko ina na jikin nata, k'arewa d'akin kallo ta shigayi har saida taji muryar Dad yana cewa "Sannu baiwar Allah", da sauri ta dubi inda yake snn ta d'ago kai tana k'arewa d'akin kallo, a hankali ta shiga rera kuka, Dad da hankalinshi ya fara tashi ganin tana kuka yasashi tunanin ko kad'eta da sukayi ne ya sata yace "Subhanallahi sannu kinji, Allah ya baki lafiya kiyi hak'uri ki bar kukan haka kar ya k'ara miki da ciwon", yayi ma nurse alama da a kira doctor, har doctor ya shigo bata tsaida kukan da takeyi ba, yana zuwa bayan ya duddubata yayi mata allura, bata jima ba bacci yayi gama da ita, har aka cika kwana uku bata cewa komai, kullum Daddy yakan zo ya dubata safe da yamma, abinci ma sai nurse d'in tayi dagaske take daurewa taci kad'an, a ranan da ta cika kwana uku tun da safe da Dad yazo aka sallameta bayan magunguna da doctor ya bata, gida Dad ya kaita ya sa aka gyara mata snn ya zuba mata masu aiki, washegari bayan ta huta Dad ya shigo ya sameta bayan sun gaisa ya fara tambayarta inane gidansu, kamar jira takeyi ta fashe mishi da kuka, da kyar ya samu tayi shiru snn tace "Ba mu da gida", Dad ya d'an wara ido ya gyara zama yace "ban gane ba ku da gida ba baiwar Allah, akwai wadanda basuda gidane?, kiyi hakuri ki sanar dani mu samu mu maidaki muyi musu bayanin tsautsayin da ya sameki", cikin kuka ta fara "mu biyu iyayenmu suka haifa nida Yayata Sa'adah, ranan da aka haifeni Allah yayiwa mahaifiyarmu cikawa, ban girma nasan dad'in uwa ba saidai rashinta, Babana da Yayata sune suka hanani kewar rashin uwar da nayi, mu yan k'asar Niger ne, ina shekara bakwai lokacin yayata ta auri wani d'an Nigeria da suke kasuwanci tareda Mahaifinmu, bayan an gama biki za a tafi da ita tasa kuka tacewa Babanmu Dan Allah ya bata ni mu tafi tare, da kyar iyayenmu suka yadda akan cewa in nayi kwana biyu a dawo dani, niko da murnata na biyota dan inason Nigeria,  gidane mai girman gaske a garin Kaduna yayata take zaune, part hudu ne a gidan, nashi d'aya, yayata d'aya, uwar gidanshi sai kuma na uwar mijin, tun bayan biki yayata tasa mijinta ya nemamin makarantar kud'i da Islamiyya ta sakani batareda Babanmu ya sani ba, sai bayan wata biyu yace ta dawo dani sbd makaranta tayi magiyar ya bar mata ni, badan yaso ba ya kyaleni a wajenta, har Yayata tayi shekara bata taba koda batan wata ba, daga nan tsangwama ya fara mata a gun dangin miji, numfashi kwakwara bata isa yi ba yanzun zasu fara mata habaici ana zaginta, duk da ina k'arama amma na fahimci bata cikin kwanciyar hankali, maigidanta kullum shike kwantar da hankali kasancewarshi mutumin kirki, Hutu hutu takan shiryani inje gida watarana kuma tare muke zuwa, shekara biyar da aurenta akayi mata waya Babanmu babu lafiya, gaba d'aya hankalinmu ya tashi tunba Yaya Sa'adah ba, mijinta Ishaq ne ya kwantar mana da hankali yayi mana shirin tafiya, washegarin ranar muka isa gida muka tarar Babanmu rai a hannu Allah kwana mukayi yana mana Nasiha kan zaman rayuwaa snn yacewa Yayata ya bata Ni ta riqeni amana, kwananmu uku ya cika, munsha kuka ba kad'an mana, a ranan Ishaq mijin ta yazo bayan bakwai muka koma Nigeria mukaci gaba da rayuwa, duk bayan shekara sai Yaya sa'a tayi b'ari, tun bata damuwa abun ya fara damunta, duk inda taji ana bada magani sai taje nema amma ba a samu sa'a ba, shekara biyar tana yin asarar ciki, a shekara na shida ta samu cikin ya zauna snn nima a shekaran aka min aure da  wani d'an unguwarmu malamin university da mukayi soyayya, bayan wata shida da bikina Yaya ta ta sake samun wani cikin da ya bata wahala, ranan da zata haihu muna tare take ce min duk abinda ta haifa kada in barshi hannun kowa inyi mata alkwarin riqeshi, kamar tasan mutuwa zatayi tana haihuwa ta rasu, abinda ta Haifa ma bayan awa hudu ya bita, tashin hankali babu irin wanda ban gani ba, da kyar na samu na saba da rashinta, haka na koma rayuwa banida dangi, bayan shekara d'aya na haifi Yayana maza yan biyu daga nan ban sake wani ba sai bayan shekara bakwai na haifi mace", tsananta kukanta tayi sosai, Dad da ya tausaya mata ya mik'a mata tissue paper ta ansa ta goge hawayenta taci gana da bashi lbr tace "Safeena na jinjira rannan da rana wata mata ta shigo mana gida wai gidantane, nidai ban kulata ba na tattara yarana muka shiga ciki dan yanayin matar ma abin tsoro ne, da daddare bayan Sulaiman ya dawo ya huta nake sanar dashi abinda ya faru, yaje ya dubo mata ya dawo yace min ai matarsa ce anma tun kamin muyi aure tabar gidanshi ta tafi makkah shine ta dawo yanzu, tunda matan nan tazo mukayi sallama da kwanciyar hankali, masifar yau daban ta gobe daban, bayan watanni da zuwanta rannan muka tashi da safe Sulaiman ya rasu, tashin hankali babu irin wanda bamu gani ba, Yaya Ishaq mijin Yayata babu yadda baiyi in dawo gida ba nace zan zauna tareda Yarana in kula dasu mungode, rannan Hussaini ya shigo min d'aki duk ya rikice nake tambayarsa mey ya faru yace min yaji Larai suna hira itada wasu mazan wai su suka kashe Daddy,  na jawoshi na rungume nace kada in kuma jin haka a bakinshi ba abinda ya jiyo ba kenan, tun daga lokacin na tsorata da lamarinta, na dena barin yarana a ko ina kusa da ita, wata d'aya kenan yanzu da na san rasa komai na rayuwa, nima lokaci nake jira in bar rayuwar, ranar ina kwance na jiyo kamar Hussaini keh ihu daga waje, na tashi na fita, ai kuwa wasu katti na gani riqe da Hussaini zasu kasheshi, da sauri na isa ina tambayarsu abinda ya musu su rabu dashi, wani irin maka da d'ayansu ya kaimin ban kuma sanin ina kaina yake ba, saidai tashi nayi naga d'akinsu Safeena na hayaki alamun ya k'one kurmus, kukan da kanshi ranan nemansa nayi na rasa, lokacin da na farfad'o naji muryar Larai tana wadanne irin banzaye ne ku da baku iya aikinku ba, ba ita nake gani tana motsi ba can, wani k'arfine da bansan da ina dashi  ba na ji yazo min dan naci alwashin d'aukar wa yarana fansa, gudu kawai na shiga yi batareda nasan inda zan jefa k'afa, ina cikin gudun ne na hau titi amma bansan mey ya faru ba bayan nan", Wani irin tausayinta kawai Dad yaji yana ratsa shi, a hankali yace "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", sau uku yana maimaitawa snn yace "Haka kaddararki tazo, kiyi tawakkali ki rungumeta da ikon Allah zaki samu kyakyawan sakamo a wajen Allah, in bazaki damu ba zan tafi dake gidana kiyi zamanki a can, inada mata da yara mata biyu in har bazaki damu ba",

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now