💖💝BATUUL 7💖💝

6.5K 405 0
                                    







Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



A hankali take tafiya sabida yadda bugun zuciyanta ke k'aruwa, tana zuwa bakin k'ofa ta juyo ta kalli Farida da pleading eyes ko zata rakata amma sai taga tana d'aga mata hannu da wide smile a fuskanta, Ammah ta sake juyawa ta duba taga ko tana wajen, itama hannu ta d'aga mata tare da mata murmushi, horn dinshi ta sake ji da k'arfi , murda kofan tayi ta fita daga palon har ta k'arasa wajen da motocin gidan ke pake, rasa wanne motan yake ciki tayi sai da taga ya dallo hasken motan daidai inda take tsaye tukunna ta k'arasa amma bata bud'e ba, tsayawa ta sakeyi tana contemplating gaba zata shiga ko baya ? Tsayarwa da tayi tana b'ata mishi lokaci bata shiga ba ya b'ata mishi ya sake danno mata horn din da k'arfi, kofan dake gaba na gefen driver ta bud'e ta zauna ba tare da tace mishi uffan ba, tada motar yayi sai da sukaje gaban gate kamin mai gadi ya bud'e mishi gate bayan yayi mishi horn ne ya jeho mata tambaya ba tare da ya dubi inda take ba yace "wane anguwane", a hankali cikin sanyin magana tace mishi "Lagos street", tambayanta ya sakeyi "Which side of Lagos street?" , cikin muryar sanyi tace "In munje area din zan nuna maka" Baisan Lokacin da ya juyo ya watso mata wani irin kallo ba, a ranshi fadi yake "Is she kidding me? muje zata nunamin, bata san ma hanyan gidansu ba kenan" bai ce mata komai ba ya fita daga gate din gidan ya d'au hanyan anguwan da ta fada mishi, tafiya sukeyi babu wanda ke cewa kowa komai sai k'ira'ar Juhanny dake karanta suratul Qasas da k'arar air conditioner, gaba daya hankalinshi na kan tukin da yake , Batuul kam skirt din jikinta ta riqe da k'arfi har hannunta na yin gumi saboda kwata kwata she is not comfortable, Allah Allah take su k'arasa gida, wani hanyan Lagos street din yabi wanda bata tab'a bi ba har suka isa, suna zuwa ya sake tambayanta "Ta ina gidan yake" juyawa tayi tabi window motar da kallo taga bata san wajen ba, a hankali tace mishi "ba nan bane fa" , wani kallon ya sake watso mata wanda yasa ta saurin sata kai k'asa , tare da gangarawa gefen titi ya tsaida motan, dago kanta tayi taga ita yake kallo yana jira ta k'ara yi mishi bayanin ina ne idan ba nan ba, ce mishi tayi "Ni ban taba ganin nan ba a anguwanmu ba, mu koma gidanku sai in nuna maka daga farko inda hanyan gidanmu yake ko kuma in qira Ahmad sai ya d'aukeni a can" sai da ya bari ta gama magana bai ce mata komai ba sannan ya tada motan yaci gaba da tafiya, tsaki yayi tare da duba agogo yaga k'arfe takwas 8 daidai, Sun kusa minti talatin suna yawon neman hanyan gidan basu samu ba, ita dai babu abinda takeyi sai addu'a gashi tana ta k'iran number Ahmda baya d'auka, sai da ya gaji da yawon neman tukunna ya sake tambayanta "For God's sake tell me where your house is" cikin kakkausar murya yayi mata maganan, take jikinta ya fara b'ari, hawayen dake mak'ale ya k'arasa gangarowa, shiru tayi ta kasa ce mishi komai, magana ya sake yi "Are you this dumb naji Sadiq na cewa kina da ilimi", tsaki ya sake ja yace mata "okay tell me right now cuz you have wasted my time alot", ce mishi tayi "Nifa ban gane hanyan nan da ka bi ba, ba ta hanyan nan muke bi ba mu in zamu.....", bai bari ta karasa maganan da ta keyi ba yace mata "GET OUT" da k'arfi, kai ta d'ago ta kalleshi dan ta k'ara tabbatarwa da gaske yake, ce mata ya sake yi "I SAID GET OUT", kasa yin komai tayi a lokacin saida ya mik'a hannunshi ya bud'e mata k'ofan sannan ya k'ara ce mata "OUT" ko ledan da Ammah ta bata bata tsaya dauka ba ta bud'e motan ta fita, tana fita ya fizgi motan kaman wanda zai tashi sama


A wajen Batuul ta tsaya ba tare da tasan abun yi ba, ga tsoro da ya cika ta, tsoro ma takeji tayi motsi dan gani take wani abun zai kama ta, kuka ta saka a hankali tana k'iran Baba, wayanta ta ciro ko xata ga missed call din Ahmad amma taga bbu, takaici yasa ta ki kiransa ta kuma mayar da wayar cikin jaka, tsugunawa tayi a wajen ta kifa kanta a cinya ta ci gaba da kuka dan ita bata ma san inane nan ya kawota ba, gashi anguwan babu commercial vehicles bare tace zata hau d'aya ya kaita gida, shirun da anguwan yayi ne yasa ta d'ago kanta ta sake dubawa ko zata samu mafita, da taga babu yadda zatayi ne ta yanke shawaran kawai ta tashi tayi ta tafiya ko zata samu yadda zatayi,


Tunda ya bar wajen hankalinshi yake kanta, tuk'i yake cike da damuwa, "yama za ayi mutum yace baisan hanyan gidansu ba idan ba rainin wayo ba?" Tambayar da ya yiwa kanshi kenan tare da jan tsaki, Tunawa da yayi da fuskanta da yadda hawayen ke gangarowa daga idonta ne yasashi saurin taka brake da k'arfi, mutane ne ke ta yi mishi horn amma bai kulasu ba, parkin gefen titi yyi, idanunta da ke Tara hawaye kawai yake gani,d'an siririn tsaki yaja, wayanshi ya d'auko ya lalubo number Farida ya k'ira, tana d'auka yace "ke inane anguwansu k'awarki", ce mishi tayi "lah Yaa Abu har yanxu baku k'arasaba" a tsawace yace "Tell me what i asked you and dont question me" ce mishi tayi "Lagos street ne behind Leventis, Yaa Abu wani abune ya faru" bai jira ta k'ara magana ba ya katse wayan, yana ajiye wayan ya juya motan hanyan da ya bar Batuul a wajen, yana isa inda ya bar ta ya duba yaga bata nan sai d'an kwalinta da bata san ya fad'i ba a kasa gun, fitowa yyi ya dauka ya jefa bayan motanshi, a hankali ya dinga bin hanyan, daga can ya hango ta tana tafiya tana share hawayen dake zubowa a idonta, karasawa yayi inda take yayi mata horn, bata juyo ba sai ci gaba da tayi da tafiya da sauri, wani horn din ya sake mata amma bata juyo ba sai ma sauri da ta k'ara sabida tsoro, gabanta yaje ya tsaya da motan, bude mata k'ofa yayi yace mata "GET IN", ko kallonshi bata yi ba taci gaba da tafiya, fitowa shima yayi daga motan yabi bayanta dan ranshi ya soma b'aci, yana isa wajenta ya kama hannunta ya jawota har wajen da yake, fixge hannunta tayi da karfi batasan lokacin da tace "dole ne sae na shiga motar ka malam" bata ankara ba sae ji tayi ya ka ta cikin motar, yyi banging kofar snn ya zaga ya shiga ya tada motan ya bar wajen, kuka ta dinga yi a motar uwa wata karamar yarinya, kara gudunsa yyi had'e da dukan steering wheel din motan yace "Damn it" sae kace warce ya sato, a ranshi fadi yake "Duk su Ammah ne suka jawo masa yana xaman xaman sa" gnin har lkcn bata fasa kukan da take ba yasa ya bude pidgin din motar ya dauko handkerchief ya miko mata, kin karb'a tayi, wani haushi ya kuma kama sa ya mayar da handki din, wani gida suka kusa wucewa tayi sauri tace mishi ga gidanmu nan, brake ya taka yayi horn a gate din yana jira a bud'e, bata jira an bud'e ba ta fita da sauri ta shige gidansu, bin ta da kallo yyi cike da bacin rae, yafi minti goma a k'ofar gidan ba tare da ya tafi ba, idonshi ya fad'a kan ledan dake ajiye, d'auka yayi ya fito yayi sallama da mai gadin ya mik'a mishi yace mishi na Batuul da ta shiga yanzu ne, k'iran sunanta da yayi ne ya sashi jin wani iri ya juya ya koma mota ya tada ya tafi.

💖💝BATUUL💖💝Where stories live. Discover now