LAILAH-DIZHWAR

4.4K 147 10
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*105*

_"Sannu Lailah Allah ya baki lafiya"_
Anty Yusra ta fada tana jijjiga Zuhra dake motsi a bayanta.

Kai kawai ta gyada mata batare da tayi magana ba, tana jikin su Abba kokarin tashi take gaba daya ma ta kwanta jikin Maman, amma Abba ya hana ta.

Sun jima acikin asibitin Sannan Sukayi wa Mama sallama duk suka tafi akan gobe da safe zasu dawo mama kawai aka bari dan tayi jinyar su.

Koda suka fito zaune suka tadda jafar, Sallama sukayi masa suka tafi,har waje ya rakasu suka hau mota suka tafi.

Koda ya dawo shiga ciki yayi, ganinta kwance ta rufe idanta amma ba bacci take ba,jin motsin mutum yasa ta bude ido.

Ganin Jafar yasata sakin murmushi.
Zama yayi tare da yima Mama sannu ta hanyar rissinawa tare da daga mata hannu.

Dadi taji sosai dan tana matukar ganin girman shi da kuma hankalinsa.

_"Sannu ya jikin naki"_
Ya fada yana kallan Lailah.

Shima kai ta daga masa dan bata san yin magana ko ta cire oxygen din dake bakinta dan tana jin dadin numfashi dashi.

_"Kina bukatar wani abunne? "_
  Ya fada yana kallan tah.

Kai ta girgiza alamun babu abunda take bukata.

Sallama yayi musu tare da dauko kudi masu yawa ya ajje ko suna da bukatar siyan wani abun, godiya  Mama tayi masa sannan ya fita.

Dan lokacin 12am har tayi na dare.

________
Yau kwanan Lailah uku a asibitin jikinta yayi sauki sosai an cire mata robar oxygen din dan yanzu tana iya numfashin.

Kullum Dizhwar saiya zo, amma baya jimawa yake tafiya sabo da Jafar kece masa ya tafi be kamata ya dinga zarya haka bah.

Shikuma abun yana masa ciwo duk saiya tsani sarautar sabo da yaga alamun tana san ta hanashi sakewa da matarsa in yana Normal rayuwarsa yafi jin dadi.

Yau ake san sallamar Lailah dan haka su Anty Yusra basu zo ba dan suma su Maman gida zasu dawo.

Bayan an kuma duba lafiyarta aka bata magunguna da zata ci gaba da amfani dasu.

Koda aka gama komai zasu tafi gida, tunawa tayi da Zaliha ta tambayi dakin da take.
cike da zumudi ta karasa, ganinta kwance kafarta a sakale yasa Ta karasa da sauri gurinta tare da fadin,
_"Sannu Zaliha ya jikin naki, ashe karyewa kikayi"_

Murmushi tayi tare da fadin,
_"Kawata da sauki, naga kema kin warke, Allah ya kara lafiya"_

_"Ameen ameen,Nagode sosai da irin taimakon da kika yimin kuma insha Allah zan kubutar dake daga hannun yan sandannan dan nasan har yanzu kina tsare a karkashinsu"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now