LAILAH-DIZHWAR

1.3K 88 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*133*

________
Koda Dizhwar ya isa fada, cike ya sameta da jama'a, sabo da haka zama yayi, nan aka shiga mika gaisuwa Jama'a daya bayan daya ana
masa gaisuwa, yaji dadi sosai koba komai sun kula da dan uwan nasa, sunyi masa addu'a sosai wanda hakan har kuka ya sakashi dan farin ciki batare da sanin kowa bah.

________
Be shigo gida ba saida dare yayi bayan sallar ishsha'i, daki ya nufa tare da zama yaci abinci ya dauki wayarsa ya kira Asiya.

Bayan sun gama gaisawa ya kwantar mata da hankali sosai tare da mata fada akan yawan tunani kuma ta dinga cin abinci.
Taji dadi kuma tayi masa alkawarin zata kiyaye insha Allah

Sun dan jima yana mata hira, duk dan ya debe mata kewa ya hanata shiga damuwa dan yasan koda yaushe tana cikinta kamar shima yanda yake.

Ya tambayi Ayman yafi sau a kirga, har saida ta dinga masa dariya.

Saida ya tabbata ya sata cikin farin ciki, yayi mata sallama tare da sanar mata ta gaida su Mami.

Tambayar Lailah yayi ta sanar masa sunyi bacci ita da Ayman din nata.

Tunda ya fara wayar Husna ta shigo dakin ta zauna kusa dashi, har ta fara kaguwa ganin ko ta kanta bebi ba kamar ma besan tana wajan ba, sai bayan ya gama tukun ya ajje wayar yana shirin kwanciya.

_"Wai dan Allah menayi maka, ni bana san abunda kake min, da ka dinga yimin irin wa yan na abubuwan ai gwara kawai ayi me yiwuwa dan bana san Ranin hankali.

Shiru yayi mata ya juya dan yana san yayi bacci.

Ganin haka yasa ta kara tunzura tana fadin,
_"Wallahi gwara ka sakeni, tun dazu nake maka magana amma kayi banxa dani, koni na kashe Jafar din da zaka dinga tsanata kana ma nuna kana gaba dani tunda kaki ka kula"_

Shiru babu magana bacci ma ya fara daukarsa.

Hakan yasa ta fashe da kuka me cin rai, haka taci gaba da rairai kukanta, yaukam ya danne zuciyarsa iya danni dan saida ya daina jin kukan alamun bacci ya daukeshi.

Ita kuwa ganin duk sanda ya bata mata in tayi kuka yana kulata yasa ta dage tana yimai kukan daya tsana

Amma ga mamakinta har ta fara gajiya amma be zo ya lallasheta bah ganin har tayi shiru be zoba tasan Lallai ba karamin Laifi tayi ba hakan yasa ta mike ta shiga toilet ta wanke fuskarta,ruwa ta fito tasha me sanyi dan makogaranta ya fara ciwo sabo da kukan data dinga yi na banza.

Bayanshi ta kwanta tare da kudindine jikinsa.

Koda ya tashi lokacin daya saba, alwala yayi ya fice daga dakin dan zuwa masallaci, bashi ya dawo ba sai Wajan 8am, batare da yayi wanka ba ya koma ya kwanta dan kwana biyu be samu yayi isashshan bacci bah, hakan yasa duk yake jinsa kamar anyi masa duka.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz