LAILAH-DIZHWAR

1.4K 88 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*148*


A ranar de yanda Dizhwar yaga rana haka yaga dare sabo da ko kadan ya kasa bacci abun beyi mashi dadi bah.

______
Washe gari da iyayan yaran da akayi masanye a asibiti suka zauna inda suka basu hakuri suka kuma basu kyaututtuka na musamman.

Sunji dadi sosai, maman Jafar har gaban Lailah tazo ta bata hakuri, itama taji dadi sosai kuma xasu dinga zumunci a dinga kawo Jafar din nan gidan suna ganinsa.

Sosai suka ji dadi suka yaba da irin hankalin Lailah da san mutanan ta.

_______
Bayan sati daya da abunda ya faru, kullum kamar yanda aka fada dukkan wanda suke kurkuku suna cikin ukuba da shan wahala, zuwa yanzu Husna babu abunda tafi shaawa kamar ta mutu, gashi babu wanda zai dinga zuwa yana dubasu a yan uwansu har sai ranar da aka fito dasu, wanda suka kasance cikin danginsu masu hankali sunyi Allah wadaran na hali irin nasu, wanda ko basu san abunda sukeyi ba sun tausaya mata har suna zagin Lailah.

Yau kusan kwana uku da dawowar Fareeda gida, babu wanda yake shiga wajan ta sai jakadiya da kuma Nurse da suke duba ta.

Yau Lailah ta nufi dakin nan aka kaita dan duba tah.

Koda taje bakin kofa, ita kadai aka bari ta shiga batare da Kuyanginta bah.

Kwance take kan gado idanta a rufe.

Karasawa Lailah tayi ta zauna kusa da ita kan kujera tana kallanta cikin tausayi.

Ahankali ta bude idanta ta kalli Lailah tare da maidawa ta rufe.

Itama Lailah kallan nata take.
Ganin kamar hannunta yana motsi yasa Lailah saurin kama hannun nata tana fadin,
_"Sannu Fareeda yaya jikin naki"_

Batare da tayi magana ba kawai ido ta lumshe dan ita kadai tasan yanda take ji.

Hannunta Lailah ta hada da nata itama haka, ta jima a haka kafin ta kuma bude idan nata ta juyo ta kalli Lailah cikin sanyin murya ta furta,
_"Lailah"_

Jin ta kira sunan ta yasa ta kara matsawa kusa da ita tana fadin,
_"Naam sannu"_

Bata kuma magana ba kuma har Lailah ta gaji da zama ta tashi dan tafiya.

Ganin taki sakar mata hannu yasa ta koma zata zauna.

Sai kuma taji ta furta,
_"Ina Yaya Dizhwar yake, ki kiraminshi kar in mutu"_

Cikin tsoro ta furta,
_"Insha Allah bazaki mutu bah fareeda kinji, sannu"_

Hawaye kebin fuskarta kawai batare da tace komai bah.

Hakan ya taba Zuciyar Lailah sosai, nan da nan itama kwallah ta cika mata ido dama gata da saurin kuka.

Saita kama kukan ganin yanda take ta faman juya kanta ajikin pillow,

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now