LAILAH-DIZHWAR

1.7K 87 32
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*145*


_______
Fareeda Asibiti aka kaita dan yi mata taimakon gaggawa kasancewar har lokacin akwai sauran tah.

Nan suka yi mata aiki tunda gubar bata mata illah sosai bah.

Koda abu yayi kyau ya daidaita aka yima me martaba waya aka sanar dashi, sai lokacin hankalin yan gidan ya kwanta.

_______
Yaune ya kama suna, inda yaro yaci sunan Jafar kamar yanda mahaifinsa ya masa hudubah.

Nan da nan gida ya dauka da sunan da aka sakama yaro, Husna kuwa tayi tsalle ta dire babu wanda ya isa ya kira danta da suna jafar, inda wasu daga cikin yan uwanta da kwayanta suka goyi bayanta tana ta faman fada da masifa.

Lailah ta hada kayan jarirai masu kyau da tsada aka kai amma kin amsa tayi, haka aka maido mata kayanta  bata damu ba tunda tasan ba uwar dan bace, hakan yasa bata damu data shiga gidan sunan bah ma tunda mijinta ya bata dama fitarta zatayi.

Jakadiya ta samu wanda da ita aka je asibitin da Husna ta haihu.

A mota ta dauke ta da kuyangi biyu da kuma motar dogarawa suka nufi asibitin.

Bayan ta isa aka yi mata magana da Babban me asibitin anyi Sa'a yana nan har cikin office dinsa suka kaita shida matar sa suka amsheta hannu bibbiyu sunyi mamakin ganin itace Amaryar sarkin yar karama da ita ga dan cikinta daya fito.

Cikin nuna izzah da mulki ta zauna danyin magana dasu babu alamun wasa ko kuma Raini a fuskar tah.

Bayan sun gaisa da me asibitin tayi masa magana kamar haka.

_"Ina san a kiramin likitocin da suke da duty on 15th, da kuma record na matan da suka haihu a ranar misalin 3pm zuwa 6pm"_

Tana kallan mutumin, babu musu ya umarci Matarsa da hakan.

Cikin dan kan kanin lokaci kuwa aka kawo mata komai sannan aka kira mata likitan da kuma nurse din,  dukkansu basu san abunda yake faruwa bah.

Dan haka zama sukayi,Lailah ta dubesu daya bayan daya kafin tace,
_"Mata ukune kawai suka haihu a wannan lokacin?"_
Lailah ta fada tana kallan likitan.

_"Eh ranki ya dade, gaba daya ranar ma mata ukune suka haihu, daya anyi mata Cs biyu kuma sun haihu da kansu"_
  Ya fada cikin girmamawa.

Juyowa tayi tare da kallan me asibitin kafin tace,
_"Dukkansu ma'aikatan kane? "_

_"Eh"_
Ya fada yana kallansu.

kallanta ta maida zuwa likitan daya yi aikin sannan ta ce,
_"Akwai jaririn daya mutu ko kuma ya samu matsala a ranar?"_

Jin haka yasa likitan kallan mutanan dakin kafin ya kalli Lailah yace,
_"Eh akwai wata mata da danta ya mutu "_

Tunda ya fara magana take kallansa harya gama bata dauke idan ta akanshi ba, sai kuma ta kalli Nurse din nan guda biyu tare da fadin,
_"Dan gidan waye kuka bawa gimbiya Asma'u"_
da sauri kowa ya kalleta cike da mamakin abunda ta fada.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now