LAILAH-DIZHWAR

1.7K 93 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*111*



Sanye ta fito da Hijab dinta mekyau kalar kayanta, Takalmi ta saka Flat a kafarta.
Humaira ce ta rike mata hannu da kanta suka fita da jakadiya da kuma kuyangi guda biyu.

Can bangaran Baban nasu suka nufa dan shi zasu fara gaidawa.
Da sallama suka shiga yayin da yana zaune a babban Falonsa shida Abban amininsa kuma wazirinsa.

Ganin haka yasa ya fita, nan cikin kunya da Girmamawa Lailah ta durkusa har kasa tana gaidashi.
  Shima cikin jin dadin hakan ya amsa yana me kalla Humaira tare da fadin,
_"Mamana ashe kin shigo gidan namu yau"_

_"Eh Baba, ya gidan ya karfin jikin naka"_

_"Alhamdulillah, ina me gidan naki da yaran, dazu Asiya ta kirani ashe ta samu karuwa "_

_"Eh Baba"_

_"Toh Allah ya raya ubangiji ya albarkace ku ya bamu yara masu Albarka "_

_"Ameen"_
dukkansu suka Amsa, sannan ya koma kan Lailah.

_"Allah yayi muku albarka kinji yata, ya baku zaman lafiya da mujinku, kuyi masa biyayyah ki kula dashi, Dizhwar yana kaunarki yana sanki, ki dinga masa addu'a"_

Dadi Lailah taji, yanda yake mata maganar.

Sun jima wajansa sannan suka tafi part din Hajiya Babba.
Koda suka shiga Babban falon bata nan, dan haka zama sukayi suna jiranta.

Koda ta fito zama tayi cikin fara'ar ta suka gaisa tana me yima Lailah addu'ar zaman kafiya kamar ba ita ba.

_"Humaira yaushe rabanki da gida? "_

Murmushi kawai tayi, dan  harta manta kam.

_"Zakiyyah ma yanzu ta tafi, tace kunyi waya zaku tafi kanon Ranar talata ko? "_

_"eh ranar zamu tafi dukkan mu harsu lailah insha Allah"_

_"Toh, Allah ya kaimu,Allah kuma ya raya abunda aka samu yayi albarka"_
Hajiyar ta amsa.

Basu jima nan ba ma suka nufi part din Anty Amarya, Humairah kuma duk tana yin hakanne sabo da Mami ce ta saka tah.

Koda suka shiga suma basuga kowa cikin falon ba, sai daya daga cikin kuyangin da suka zo da ita suka tura ciki danta kira tah.

Cikin tsoro da fargaba ta nufi dakin da take tunanin nan take zama.

Ahankali ta shiga knocking, cikin tsawa aka bata iznin shiga.

Jikinta yana rawa ta zube kasa tana gaisuwa tare da fadin,
  _"Ranki ya dade, Gimbiya Humairah da Maryar Sarki ne suka zo gaida ke? "_

Kallan juna sukayi ita da Fareeda dake zaune.

_"Lailah"_
Fareeda ta fada tana kallan Mommyn tatah.

Amsa ta bata da _"eh"_

Aikuwa cikin zafin nama kanta ko dankwali babu ta fita dan ganin wata tsinanniyarce Lailah.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now