LAILAH-DIZHWAR

1.4K 82 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*147*


Ganin Sarki yazo duk sai suka nutsu, suna nan tsaye har ya shige cikin gida, inda lailah ta sanar da dogarawan nasu kar subar kowa ya shiga ciki, itama ta shige part dinta tare da mutanen tah.

_____
Part din Mami  ya shiga shida nasa jama'ar tare da Memartaba, zama sukayi bayan duk mutanen sun ragu Mami  ta shigo Babbna falon nata.
  Kana ganinta kasan tana cikin damuwa.
Zama tayi tana kallansu kafin tace,
_"Sannunku da zuwa, yaya me jikin? "_

_"Jiki da sauki, tunda sunyi nasarar ceto Rayuwarta, gobe nake san a maido ta gida ma"_
Memartaba ya fada yana gyara zamansa.

Kallanta ta maida ga Dizhwar din da yayi shiru bai yi magana bah.

_"Sarkin Sarakuna yadai, naga kayi shiru"_
Mami ta fada tana kallansa.

Murmushi ya danyi tare da fadin,
_"Ba komai inasan in shiga ciki"_
Batare da tayi musu ba,ya mike ya fice da masu tsaransa zuwa part din Lailah.

Mami Kallanta ta maida ga Memartaba tare da fadin,
_"Akwai babbar matsala da take faruwa ciki gidan nan ranka ya dade"_

Cike da mamakin maganarta ya furta,
_"Matsala kuma? "_

Tana kuka da bakin cikin abinda ya faru ta sanar ma da Memartaba dukkan abunda yake faruwa.

Abun shima ba karamin daure masa kai yayi bah, cike da tausayin kansu da kuma Dizhwar din, ga kuma gefe daya zuciyarsa da take faman tafasa ya furta,
_"Amma yarinyar nan tayi babban kuskure"_

_"Wallahi kuwa, nima abun ya bani mamaki, ban taba tunanin Asma'u xata aikata abu makamancin haka bah"_

_"Zata iya,zata iya abunda yafi haka ma, yarinyar da bata da mutunci, Lailah ta fita hankali ai, wallahi tun tuni nake cike da nadamar hada auranta da yaran nan sabo da ko kadan bata da tarbiya, amma insha Allah komai yazo karshe"_

Yana fadin haka shima ya wuce nasa bangaran cike da tunanin irin babban abunda ta aikata.

________
Dizhwar jikinsa duk babu dadi ya shiga part din Lailah.

Dakinta ya nufa amma bata nan kwanciya yayi yana hutawa, kuma sai yaji yana san zuwa yaga jaririn nasa dan kmar akansa yake jin babu dadi.

Yana kokarin mikewa ta shigo da sallama, ganinsa yasa tayi saurin karasawa wajansa tare da rungumeshi tana me jin tsananin tausayinsa da halin da zai shiga idan yaji abunda ya faru.

Zama yayi yana me kara matseta jikinsa.

_"Rouhi ya jikin Fareeda?"_

_"Da sauki"_
Ya fada cikin wata irin murya.

Jin muryar da yayi magana, yasa tayi saurin dagowa tare da kallansa.

Cikin damuwa ta shiga shafa fuskarsa tana fadin,
_"Rouhi menene yake damunka haka naji muryarka ya canza? "_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now