LAILAH-DIZHWAR

1.4K 94 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*127*

Binta yayi da kallo cike da mamaki tare da fadin,
_"Meyasa bakya amfani da kwakwalwar ki, shikenan gayamin menene yasa ta baro gidan nata ta dawo gida? "_
  yana kallanta da sigar Jin amsa.

Shiru tayi kafin tace,
_"Nina saka a daukota sabo da nagaji da abunda yake mata, Dan zaiyi aure saiya dinga Wulakantamin yata aiba cewa akayi masa bata da gata bah"_

_"Humm,yanzu kuma laifina kike gani, lokacin dana hanata auran sa, gudun mu tayi gaba daya, kika daure mata gindi akayi bikin nan batare da izinina bah, kuma yanzu sabo da baki da kunya, kike dinga gayamin magana san ranki,har Namijin daya kasance me taurin zuciya da taurin kai, gaba daya sunbi umarnina, Acikinsu akwai wanda kikaga yana da matsala makamancin yanda ita take dashi,sabo da haka kada ki sake sakani acikin maganar ku, ke kika aura mata shi, kuma dukkan abunda yaje ya dawo laifin kine"_

Bude baki tayi xatayi magana, da sauri ya daga mata hannu dan baya san jin komai.

Sallamar kowacce yayi tare da mikewa ya fice daga falon.

Haka suka mike suka bar cikin dakin suma, Anty Amarya ranta a mutukar bace, dama A tunaninta intazo zai goya mata baya, tunda kuwa yayi mata haka dukkan matakin daya kamata shi xata dauka.

______
Husna kuwa Koda suka dawo jiya ta shige part dinta zama tayi tana tunanin hanyar da zatabi dan ganin ta cimma burinta.

Tasan tabbas bada ban cikin dake jikinta bah, saita yima Lailah mugun duka sabo da ko hotonta bata san gani ballan tana ta ganta, Kuma ta dau alwashin Ita kadai da kuma dan da zata haifa zasu rayu da Dizhwar, ita da yaranta zasu gaji dukiyarsa, saida ta tashi a babun badulahu koda ta samu ciki bazata taba barin shi ba saide in bata raye dan haka yanzu zata ajje su a gefe har zuwa lokacin da xata haihu.

______
*Kano*

Asiya jikinta duk yayi sanyi dan ganin yau duk zasu tafi su barta hakan yasa bata jin dadin gidan gaba daya.

Tun safe Ayman yake bayan Lailah, tana yawo dashi cikin gidan itama cike da kewar Asiyan da zata tafi ta bari.

Humairah ta sanar mata da huri zasu tafi hakan yasa ta mike ta shiga dakin,ganin Asiya xaune kan gado tayi shiru tana kallan wayar dake hannunta.

Da sauri ta karasa tare da fadin,
_"Asiya lafiya?,nifa wallahi kina bani tsoro in naga kinyi shirun nan, sai inga kamar bazamu kara haduwa dake ba, nasan kinayin araba'in zaki zo dan kiga Mami amma duk kin daga hankalinki, toh yanzu da bamu zoba yaya zakiyi, pls kiyi hakuri ki saki jikin ki kinji? "_
Ta fada tana kallan fuskarta.

Kai kawai ta gyada tare da murmushin yake.

Ahankali ta matsa kusa da gadan Ayman din tare da kwantar dashi, tana me masa magana duk da idansa a rufe yake,
_"Ayman yaran kirki, kaga mamanka yau ko Murmushi bata yima Anty lailah, pls yaran kirki ka lallasan mana ita"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now