LAILAH-DIZHWAR

1.6K 96 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*124*

Sun dan taba hira kadan kafin yayi musu sallama ya fito ya nufi dakin da Husnar take ciki.

________
Dama tun da ta shiga cikin dakin Kuka take na kishi da bakin ciki, ita bata san meyasa bah ta tsani Lailah ko ganinta bata san yi ballan tana tare da mijinta.

Tura kofar dakin yayi, kan gado ya hangota zaune, jin tana kuka yasa ya karasa wajanta.

Husna tana bashi mamaki, ko kadan bata ganewa bata da kwakwalwa, ita kawai abunda takeso in bata samu ba bazata taba yin tawakkali bah.

Ahankali ya karasa tare da zama a bayanta.

_"Husna"_
Ya kira sunanta yana dafa kafatunta.

Bata jiyo ba kuma bata masa bah,

_"Husna bansan da wani yaran kike san nayi miki bayani, duk yanda naso ki fahimci menene aure, ya ake zaman aure, ya ake zama tare da kishiya,amma sam kin kasa fahimta Husna, Ya kike so nayi, so kike na rabu da Lailah kome? "_

Juyowa tayi da idanunta da sukayi jajir cikin kuka ta furta,
_"Koma menene ai kaine kaja, Tunda ka aureta ka daina sona, baka damuwa da damuwata,  bayan kasan ina san kulawarka musamman a wannan Lokacin da nake ciki, amma koda yaushe kana tare da ita, itace farin cikinka, itace kake gayama suna me dadi nikuma da sunana ma kake kirana sabo da baka sona yanzu"_

_"Ya Allah, Meyasa zaki fadi haka yanzu ki fadi menene bani miki, na auri Lailah, an raba girki, kowacce in girkinta yazo ina kokarin sakata farin ciki, Wata irin kulawa kikesan in dinga baki, goyaki zanyi in dinga yawo dake ne, Dukkan abunda kikeso ina miki shi, nasan kishi dole ne, amma meyasa bakya kishin daya kasance me tsafta, bakiga yanda Lailah  take ba, wallahi kome zanyi anan dukka jimawar da zanyi anan, wallahi ban taba zuwa wajan Lailah tayi korafi akan hakan bah, jiya muna waya da ita kin kwace kin hana, amma inda itace tayi miki haka bazakiji dadi ba, bayan kinsan bata nan kuma danna kirata naji yaya take ba laifi bane"_

_"Ai dama haka zaka fada, ita akan me zata damu bayan tasan itace star awajanka"_

Ajjiyar zuciya ya kumayi tare da fuskantarta,
_"Bana san in dinga ganinki cikin damuwa, ki gayamin me kikesan ayi yanzu, ki gayamin me zanyi ki daina dukkan wannan koke koken da kikeyi?"_

Kallansa tayi ido cikin ido tare da fadin,
_"ka rabu da ita, ka saki Lailah muci gaba da rayuwarmu kamar yanda muke da"_

Batare da yayi mata magana bah, ya mike, pecking goshinta yayi tare da fita yana fadin saida safe.

Dan tabbas yasan bata da kwakwalwar mutane, bata da fahimta dan haka yaji tayi ta kukan tana abunda taga dama, Dan taga yana lallabata, yanzu babu wanda ya isa yasa ya rabu da lailah inba Allah  bah.

Tana ganin haka yasa ta kuma fashewa da kukan bakin ciki, yanzu yama daina santa kenan, dole tadau mataki, dole tasan me zatayi, sabo da Lailah mayyah ta lashe mata kurwar mijinta gaba daya.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now