LAILAH-DIZHWAR

1.8K 110 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*109*



_"Ya kike fadin irin hakane Husna, sai yaushe zakiyi hankali yaushe zaki dena abunda kike, zuciyarki bata da aiki sai raya miki abunda be dace ba, Cikin nan ciki nane, kuma gudan jini nane, tayaya kike tunanin zan qishi, pls ki dinga yima kanki fada mana"_

cikin masifa da tsiwa ta mike tsaye tare da fadin,
_"Bazanyi ba,ba zanyi ba, inka gaji danine kake kokarin hulakantani ka sakeni mana, auranka dole ne, wallahi dada hali da saina zubar da cikin nan sabo da koda an haifeshi bana tunanin zaka soshi"_

Wani wawan mari ya sakar mata, dan yagaji da lallabata, yanzu kam ta kaishi makura.

_"Wallahi kika kuma furta kalmar zubar da cikin nan sai kin gane kuskuranki, ke mahaukaciyar inace, toh bara kiji in gaya miki wannan ciki ko cikin shege ne in har nina yishi baki isa ki zubar dashi ba ballan tana dan sunna ne, sakarai mahaukaciya"_

Yana gama fadar haka ya wuce daga dakin.

Kallan fuskarta da kanta tayi a mudubi, wai Dizhwar ita ya mara.

Wani saban kukan ta saki tana me Tsanar kanta.

_____
Shikuwa ranshi a bace ya nufi part din Lailah, koda ya shiga dakin da suka kwana be ganta ba, dakin kusa dashi ya shiga dan yana zuwa falon duk wanda yake ciki ya fita.

Ahankali ya tura kofar hangota yayi kwance kan gadon ta turo kafafunta waje daga cikin rumfar gadan.

Ahankali ya karasa yana kallanta gadan shima ya burgeshi.

Jin mutum ya shigo yasa ta mike zaune tare da fitowa daga ciki.

Kallanshi tayi ta rage tsawanta tare da fadin,
_"Ina kwana"_

Dadi yaji har cikin ransa dan koba komai yau matarshi ta gaida shi abunda Husna batayi koda wasa.

Be amsa mata ba saida ya rungumetah tare da cire hijab din ya ajje a gefe,
_"Lafiya qlau ya helo(My beautiful) "_

_"Kinci abinci kuwa"_
Ya fada tare da zira hannunsa cikin rigarta.

Abun mamaki yaji zafi jikinta daya taba fatar ta.

Da sauri ya kalleta tare da fadin,
_"Baki da lafiya ne naji jikinki zafi"_

Shiru itade tayi dan itama bata san ko bata da lafiya ba,dan gani take duk wahalar datasha jiyane bata jin dadin jikinta.

_"Bara in kira Dr. Ta duba min ke"_

Da sauri ta furta,
_"Aa nide kawai ka barshi, me kakesan nace musu ya janyo rashin lafiyar, zan warke ma ansan duk gajiya ne"_
Ta fada ahankali tana mejin kunya.

_"Menene abun jin kunya kuma aciki, kowa yasan in anyi aure abunda akeyi kenan, kuma sai ki cutu sabo da kunya "_

_"Dan Allah nide ka bari,nide bana so in kai bakajin kunyar ni inaji, wallahi bazaka kira wani dr. ya dubani ba"_
Ta karasa maganar murya na rawa kamar me shirin yin kuka.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now