LAILAH-DIZHWAR

1.3K 102 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*132*

______
Yau Dizhwar ya dawo gida cike da kewar dan uwan nasa, yayi wani iri duk yabi ya rame sosai ya kara haske, haka yaso ya taho da Lailah ko dan ta dan debe masa kewa amma sam taki, saita yi bakwai itama haka Mami ta daure mata gindi taki biyoshi, dole badan yaso ba ya hakura.

Koda ya shigo gidan kai tsaye dakinsa ya nufa ya watsa ruwa ya shirya dan fita fada dan da mutane da yawa da suke san kara masa gaisuwa.

Koda ya fito yana shirywa, cikin mamaki Husna ta shigo da katan cikinta dan yanzu kam ya girma sosai ta kusan haihuwa ya shigo wata na 7.

Da sauri ta fada jikinsa tare da fadin,
_"Sannu da zuwa masoyina,yanzu Sarkin gida yake sanar da zuwanka shine naji nazo inji yaya mijina ya dawo, shine kaje har tsawan kwana hudu ka barni cike da kewar kah, gaskiya banji dadi ba, kodan kaga da Lailah acan shiyasa kaje kayi zaman ka"_

Duk wannan magana da take tana jikinsa.

Kasancewar cikin da take dashi ya hana yayi ball da ita ahankali ya janyeta batare daya kula taba ya karasa shirinsa ya fita.

Binsa tayi da kallo tare da tabe baki dan ita hakan be dameta bah, dan bataje gaisuwa ba yake wani faman sha mata kamshi, gaisuwarce bazata bah, dan bataga abunda zai kuma sawa taje gidan nan bah.

Fita tayi ta nufi part dinta.

Koda ta shiga falonta mamakin ganin Anty Salma tayi, wanda rabanta da ita tun randa suka samu matsala da Lailah harta mareta sai yau.

Cikin murna ta karasa tana fadin,
_"Oyoyo Antyna ta kaina"_
Ta fada tare da zama kusa da ita.

Kallanta tayi a yatsine tare da fadin,
_"Yana ganki haka duk kina kamar cikin damuwa"_

_"humm, wallahi Dizhwar ne yake san bata min rai, wai dan dan gidan Yayar Babansa ya mutu banje gaisuwa kano ba shine yake wani shareni"_
Ta fada tana kallan Anty Salma da itama tunda ta fara maganar take kallanta baki a tabe.

_"Ke dallah rabu dashi, nadan lokacine, keda kike da cikinsa abunda kuma yake so, ai fishin da zaiyi dake nadan lokacine, ni bama wanan bah, kinsan abu ya matso kuma baki cika kudin bah, shiyasa nazo inji yaya abun yake"_

Ajjiyar zuciya tayi tare da kallanta,
_"Karki samu damuwa, satin daya huce ya tura mana kudi cikin account din mu, kuma dama nayi masa magana akan ya bada kudi zakije Dubai ki siyo mana kayan Baby, tunda shine yayi min alkawari, sabo da haka, yanzu zan turo miki cikon 1million din, kuma nayi miki alkawarin dama in har abun nan yayi batare da wata matsala ta faru ba, zan Baki kudi masu yawa dan nasan inna kama dana a hannu kudin dazan samu daga wajansan da kuma iyayansa da abokansa ba kanana bane"_

Cikin jin dadi Anty Salma ta washe baki tare da fadin,
_"Haka nakesan ji ta wajena ai kima daina maganar samun matsala, mun gama magana da dr. Jiran lokaci kawai nake ki kama yaranki a hannu"_

Cikin jin dadi ta furta, _"Allah ya nunamin wannan rana, Anty ai shiyasa nake abunda naga dama, dan ko memartaba yana san ganin jikansa na wajan Dizhwar din"_

Shiru ta danyi cikin damuwa kafin ta kalli Anty Salman ta furta,
_"Anty akwai abunda yake damuna wallahi"_

Cike da mamakin jin maganar yasa ta fadin
_"Menene shi Husna?"_

Ajjiyar zuciya ta kumayi tare da fadin,
_"Wallahi Anty in kinga yanda Dizhwar yake san Lailah da kuma irin rawar kafar da yakeyi akanta sai kinyi mamaki shine hankalina yake tashi, dan nasan wallahi ta samu ciki ta haihu, saiyafi san danta akan nawa, shine abunda yake damuna fiye da tunaninki"_

Dariya Anty Salma tayi me isarta kafin tace,
_"Husna kenan har yanzu labarina kikeji, duk zaman damuke bakisan halina bah, toh bara kiji in gaya miki wani abu in baki sani bah"_

Zama ta gyara sosai yanda zasu fuskanci juna da Husnar sosai, cikin iyayi da kisisina ta kalli Husnar tare da fadin,
_"Nasan bazaki manta abunda Lailah tayi min ba agabanki agaban jakadiya, sabo da haka na gaya miki  na dauki alwashin saina rama kuma saina nuna mata ita karamar yar iskace, tunda na koma gida na rasa wani irin abu zanyi mata in bakanta mata rai, Tsawan kwanaki, sai yanzu na gano dukkan wanda yake gidan sarauta ko gidan attajirin me kudi babu abunda yake bukata sama da samun zuri'a,badan komai ba saidan samun dukiya da kuma gadan wannan miji nasu bayan ransa, sabo da haka, jiya naje wajan bokana, abun mamaki kinsan wani abu? "_
ta fada tana kuma matsowa tana kallan Husnar.

_"Na gaya masa abunda nake san ayi mata, inasan a mata ajjiya cikin mahaifarta yanda zatayita fama da cuta da rashin lafiya, kuma ciki ya ki zama har abada babu ita babu haihuwa,amma sai kash!, aka samu matsala domin kuwa bokana ya sanar mun tana da ciki na tsawan sati biyu da kwanki,dan haka saide inta haihu wannan aiki zai yiyu"_

Cikin tashin hankali ta zaro ido Husna ta furta,
_"Ciki, ciki fa kika ce Anty Salma"_

Cikin tabbatarwa ta kalle ta tare da fadin,
_"Kawai kuwa ciki, dan bokana baya min karya, kinsan jiya satin ta biyu da kwana daya, yau kuma da kwana biyu, sabo da haka kinji dai abunda nazo miki dashi, amma na canza shawara, yanzu su kansu basu san tana dashi ba, sabo da haka da zarar an gane tana da ciki, abun fa zai sauya, za'ai ta mata bara zana kala kala har sai cikin nan ya zube, yana zubewa kuwa aljannu zasuyi maza su saka ajjiyarsu aciki, aiki ya fara, sabo da haka yanzu ki kwantar da hankalinki, ya zama Gidan nan daga ke sai ya'ya'nki.

Cikin murna da farin ciki Husna ta mike tare da rungumar Antyn nata tana godiya.

Dariya Anty Salma tayi tare da fadin,
_"godiyar me zakimin, ai wannan aikin nawane, ni nake yima kaina bake ba, fansa ce na dauka dan abunda tamun babu wani mahaluki daya taba yimin irinsa, sabo da haka zata gane kuranta, Wallahi, tunda ta taba lafiyar fuskata saita gommace bata zo duniyar nan bah gaba daya"_

_"Kutmar uba, gaskiya Anty ke bala'i ce, kice in baza bura'ubata acikin gidan nan, inci karena babu babbaka, wallahi wannan maganar da kika gayamin sainaji babu wani sauran damuwa cikin raina, wallahi naji dadi kuma insha Allah, sai wannan abun ya yiwu"_

_"ai kibar tantama, boka ya tabbatar min da yiwuwar hakan, ko kin manta asiri gaskiya ne, aini in har na kaima bokan nan kukana, wallahi sai bukata ta ta biya ko me za'ai kuwa"_
*_(Wa'iyazubillah, Allah ya tsaremu da shirka,Ameen)_*

Haka sukayita hira cikin farin ciki  har lokacin tafiyar yayi tayi sallama ta tafi.



*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now