LAILAH-DIZHWAR

1.6K 105 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*114*

Kai tsaye dakin Mama Aminar ta shiga cikin farin ciki ta sanar mata yanda sukayi da Abban, itama ba karamin dadi taji ba ta kuma tausayawa Zahra.

Koda suka gama shirinsu suka fito kusan duk rabin yan gidan suna san zuwa ganin yayan nasu.

Abinci aka hado kula kula masu rai da lafiya da drinks, mota biyu sukayi amma banda Alhajin nashi.

Kai tsaye suka nufi inda aka datse shi, cikin jagorancin Uncle din nasu.

Koda suka karasa kasan cewar ya sanar ma da ma'aikatan zuwan nasu, basu sha wani wahala ba, bayan an gama bin cika motar da suka zo dasu suka shiga ciki.

Zama sukayi inda aka tanada dan zaman masu ziyara, sunyi tsuru tsuru suna jiran suga yayan nasu.

Koda ya fito cikin rausayawa da masu kuka suka shiga kallansa.

Da gudu Zahra ta mike cikin tsananin kaunarsa da kuma tausayinsa ta fada jikinsa tana kuka.

Hakan yasa ya karya masa zuciya shima ya fara hawayan.

Duk aka rasa me lalashin wani cikinsu, Uncle da yake kallan su yana tsaye gefe daya shine ya bude baki tare da fadin,
_"Kukan ya isa haka,Faisal zauna ka samu abinci kaci tukun"_

Zahra neman kunya tayi ta rasa, tana jikin yayan nata harya zauna, kamar ta maida shi ciki haka suke ji, abinci aka bashi yaci yasha ruwa, nan ya roki yafiya wajan Mamanshi, wanda ta kasance mace me mutunci da Amana, taji dadin yanda yaran nata ya canza, tasan kuma insha Allah sanadiyar shiriyarsa kenan, cikin kulawa ta kalleshi tare da fadin,
_"Faisal yau wajan kwanan ka nawa nan amma baka neman matarka ko tasan halin da kake ciki, kaga hakan zai sa ta shiga damuwa wanda kasan tana da hakki akanka"_

Shiru yayi dan baya tunanin Fareeda bata san halin da yake ciki bah,
_"Ummi nima ina san nayi mata magana amma tunda aka tsareni, basa bari nayi waya ko wani ya ganni, yanzuma saida Uncle ya rokesu sabo da Dizhwar ya hana yace har sai Lailah ta yafe min tukun za'a sakeni daga wajan nan, Kaduna suka ce zasu maidani"_

Fashewa Zahra tayi da kuka tana kallan uncle din, wanda duk haka family din suke kiransa hakan yasa yaransa ma da haka suke kiransa.

_"Uncle dan Allah ka basu hakuri kada susaka akai yaya wani waje, ka ce su rabu dasu dan Allah"_
Zahra ta fada tana kallan uncle din da yake jin tausayinta da kuma mamakinta yanda lokaci daya soyayyar yayan nata ta haukata tah.

Shikuwa Faisal wanda yanzu ya kuma saukowa yana me jin tausayi da kuma kaunar matar tashi.

_"Mezai hana muje Zamfara dan mu roke alfarma wajan ita yarinyar"_
  Mama amina ta fada tana kallan Uncle din.

Gyaran murya yayi tare da fadin,
_"Wallahi sam Yaya ya hana, nima saida nayi kokarin hakan, nima yanzu nayi mamakin daya bari har kuka zo nan"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now