LAILAH-DIZHWAR

1.8K 94 16
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com



*150*

Cikin muryar kuka ta furta,
_"Nagode ranka ya dade, Allah ubangiji ya saka da alkhairi, kuma ina neman wata alfarama  a wajanka"_

_"Inajinki"_
ya fada yana kallanta.

_"Dama inasan inje in duba inda babana yake ne, ingani ko yana raye ko kuma ya mutu, inasan ya tuba yabar abunda yakeyi kafin ya koma ga ubangiji "_

_"Gaskiyane kuma babu damuwa, insha Allah saiki shirya gobe sai a hadaki da dogari kuje ku duba inda yake din"_

Jakadiya yasa aka kira masa, inda aka tambayeta ko zata gane wanda ta gani da Anty Amarya, tsaf ta furta zata gane shi.
Amma koda
akaje dubashi, sai aka ce yabar aikin ya jima da tafiya, hakan yasa aka saka duk inda yake sai an nemoshi a ranar basai an kwana ba.

______
Washe gari tunda safe Fareeda ta shirya ita da dogari suka nufi inda Bokan yake dan tabbas zata gane wajan da  kauyan dan wajan ba buya yake bah.

Nan suka dauki hanya, sam bata jin dadin yanda zataje taga bokan Mahaifin nata, amma tana son zuwane kawai danta nuna masa hanyar shiriya karya mutu cikin shirka.

______
Asiya da er ta bar Lailah ta tafi part dinsu, sunsha hira sosai dan Lailah ta jima bata kai musu ziyara bah.

Tunda safe ta nufo part  dinsu dan ji take kamar ta janyo safiya dan tana san lailah sosai.

A falo ta zauna tana yima Ayman wasa.

Dizhwar ne ya fara fitowa koda ya ganta yaji dadi sosai karasawa yayi inda suke zaune tare da amsar yaran yana masa wasa.

Cike da sha'awa take kallansu kafin tace,
_"Yayana ka shirya inde Ayman ya isa yaye zan kawo muku shi, na bar muku shi duniya da lahira "_

Kallanta yayi cike da murmushi tare da mika mata hannu..

Kusa dashi tazo ta zauna tare da fadin,
_"Yayana ina kewar Yaya Jafar sosai, musamman in naga Ayman"_

Cikin sigar lallashi ya kalleta tare da fadin,
_"Ki dena saka damuwa acikin ranki,karki samu matsala"_

Murmushi tayi tare da fadin,
_"Insha Allah Yayana"_

Rungumeta yayi ta gefe ita da yaran nata.

Lailah ce ta fito cikin shiri daga daki tana fadin,
_"Abun sha'awa yaya da kanwarsa"_
Dariya tayi tana kallan Lailah tare da fadin,
_"Yayana gaskiya zan nemo maka yar yarinya ka aura, naga Anty lailah ta fara tsufa"_

Dariya Lailah tayi tana kallan Dizhwar din da shima kallanta yayi yana murmushi.

_"Allah yayi nifa ban taba ganin sarkin daya zauna da mace daya ba gaskiya, sai kace turawa, kamata yayi harda kwarori kana dashi Gaskiya"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endKde žijí příběhy. Začni objevovat