LAILAH-DIZHWAR

1.7K 60 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*119*

Kallan Zahra tayi da idanta yanzu ya cika da ruwa tana kokarin gogewa.

Cikin tsananin jin tausayinta ta kuma kallan Mami da itama ita take kallo sunnan ta maida kallanta ga Jafar da shima de kallan nata yake yana jiran ta fadi abunda zata fada.

Shiru tayi tare da rufe idanta, nan take abubuwan da suka faru da ita suka dawo mata sababbi, kukata fashe dashi, wanda hakan yasa Mami saurin tasowa daga inda take zuwa wajan ta.

Kukan da takene yasa zuciyar Zahra karaya dan itama akwai saurin kuka, nan da nan tsiro ya darsu cikin zuciyarta dan tana ganin kamar Lailah bazata yafema Faisal din nata bah.

Hakanne yasa ta mike daga inda take, cikin fuskarta me abun tausayi ta jaraso inda Lailah take zaune, durkusawa tayi tare da rike kafafuwanta, cikin rawar murya ta furta,
_"Dan Allah Anty Lailah kiyi hakuri ki yafema Yayana, yana cikin wani hali, basa bashi abinci, gashi kullum suna dukansa, bashi da lafiya, shima yana kuka yana kuma nadamar abunda ya aikata, ki taimaka kiyi masa afuwa dan Allah Anty, badaban halinsa bah"_
  Ta karasa maganar tana me zubar da hawaye yayin data hade hannunwata tana kallan Lailah da itam atake kukan.

Ganin har lokacin Lailah batayi magana bah, yasa Zahra kallan Mama amina tare da fadin,
_"Mama kice wani abu, zasu tafi da Yaya sunce, dan Allah karsu rabani dashi, ina sanshi bana so ya mutu in zama bazawara, Mama kinsan dukkan wanda yayi kidnapping kisane hukuncinsa dan Allah Anty karki bari a kashemin Yayana bazanji dadi bazan taba farin ciki a rayuwa tabah, dan Allah Yaya kaima ka bata hakuri kinji Anty"_
Ta karasa maganar tana me kara hade hannunta nan da nan ta fita daga hayyacinta.

Ita kuwa Lailah tausayin halin da Zahra take cikene yasa ta kasa magana, tana tausayinta soyayyah, taga yanda take mutukar son Faisal din, ga kuma tausayin Faisal din ahima gefe daya cikin ranta, kofa komai dan tsananin soyayyar da yake mata ta yafe masa.

Da sauri ta sakko daga kan kujerar tare da rungumeta batare da tace mata komai ba.

Hakan yasa kukan nata ya lafa, ta tsinci kanta da rungume Lailah itama, kowacce da abunda yake cikin zuciyarta.

Dagowa tayi tana kallan Zahra, hannu tasa ta goge mata fuskarta tare da fadin,
_"Na yafema Faisal dukkan abunda yayi kin duniya da lahira, kuma inde yardata ake bukata dan a sakeshi na yarda dari bisa dari, Yaya na yarda a saki Faisal dan Allah kaji?"_
Ta fada tana kallan Jafar da yake a zaune.

Ajjiyar zuciya duk sukayi da hamdala, cikin farin ciki ya gyada kansa jin abunda Lailah ta fada.

_"Naji dadi Lailah ina me alfahari dake, dukkan wanda ya sameki a matsayin abokiyar rayuwarsa dole yayi alfahari dake, sabo da haka gobe insha Allah in Dizhwar ya iso garin nan zamuje tare kusa hannu ajanye dukkan dokar da aka saka akansa naji dadi"_

Murna sosai Mama da Zahra suka shiga yai, yayin da Mami ta shiga cikin farin ciki itama, godiya da kuma albarka suka shiga yima Lailah.

Zahra har lokacin tana jin Lailah dan bata san da wasu irin kalami zata mata godiya bah.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endDonde viven las historias. Descúbrelo ahora